Connect with us

Labarai

Ganduje ya rantsar da kwamishinoni

Published

on

A jiya talata ne gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin kwamishinoninsa guda Ashirin a zangon mulkinsa na biyu a rufaffan dakin taro dake filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata.

Kwamishinonin sun hadar da mataimakin Gwamnan kano Dr Nasir Yusuf Gawuna a matsayin kwamishinan Gona, da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sulen Garo.

Sauran sun hadar da kwamishinan muhalli Dr kabiru Ibrahim Getso, da kwamishinan yada labarai kwamare Muhd Garba sai kwamishinan raya karkara Musa Iliyasu kwankwaso.

Malama Zahra’u Umar a matsayin kwamishiniyar mata da walwalar kananan yara, da Dr Muhd Tahir Baba Impossible a matsayin kwamishinan addini da Muntari Ishaq a matsayin kwamishinan ayyuka na musamman da dai sauran kwamishinonin.

Bayan kammala rantsar da dasu ne Gwmamnan Kano Dr Abdullahi umar Ganduje ya gabatar da jawabi inda yake jan hankali ga kwamishinonin

Guda cikin kwamishinonin malama Zara’u Umar wadda itace kwamishiniyar mata ta bayyana godiyar ga A…..H tare da fatan sauke nauyin da aka dora mata.

Wakilinmu Abba Isha Muhd ya rawaito cewar bayan kammala rantsuwar an basu takardun shedar fara aiki.

 

 

 

 

Labarai

Laliga : Za a dawo gasar ranar 11 ga watan Yuni

Published

on

Mahukuntan gasar Laliga ta kasar Andulissiya wato Spain, sun tabbatar da cewa za a dawo gasar Laliga a ranar 11 ga watan Yuni mai kamawa inda za a fafata da Real Betis da kuma Sevilla.

Hukumar shirya gasar da hukumar kwallon kafa ta kasar tare da gwamnatin kasar Spain su ne su ka amince da hakan cewa za a kuma dawo gasar na kakar 2021/2022 a ranar 12 ga watan Satumba.

Tun dai a ranar 12 ga watan Maris ne a ka dakatar da gasar sakamakon cutar Corona, sai dai shugaban kasar Pedro Sanchez ya tabbatar da cewa za a iya dawowa gasar a ranar 8 ga watan.

Haka zalika a ranar 17 ga watan Yuni za a dawo gasar Firimiya ta kasar Ingila, a yayin da za a dawo gasar Serie A na kasar Italiya za su dawo ranar 20 ga wata mai kamawa.

Continue Reading

Labarai

Liman: Kulawa da tarbiyyar ‘ya’ya zai rage bata gari da lalacewar matasa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Abubakar Dan Tsakuwa dake unguwar Ja’en Yamma a karamar hukumar Gwale, Mallam Abdulkareem Aliyu, ya yi kira ga iyaye da su kara kulawa da rayuwar ya’yan su domin gudun fadawar su cikin halin shaye-shaye.

Mallam Abdulkareem Aliyu ya yi kiran ne ta cikin hudubar Juma’a da ya gudanar yau a cikin masallacin dake unguwar Ja’en a jihar Kano.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su babu shakka za a rage samun bata gari da lalacewar ya’yan matasa a cikin al’umma. Domin haka ‘ya’ya su kara rubanya biyayyar da su ke yi wa iyayen su, domin su rabauta da rahamar Allah S.W.T.”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, a cikin hudubar Limamin Mallam Abdulkareem Aliyu Dan Tsakuwa ya kuma shawarci al’umma da su kara yawaita addu’o i domin samun sauki daga cutar da a ke fama da ita ta Coronavirus a fadin duniya baki daya.

Continue Reading

Labarai

Kar mutane su shagala cewa sai wata shekarar za su kara yin Azumi -Liman

Published

on

Na’ibin masallacin Juma’a na Quba dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birni a jihar Kano, Ahmad Muhammad Ali, ta cikin hudubar san a yau Juma’a ya ce al’umma da su yi kokarin yin Azimin watan Shawal guda shida na cikin sa akwai falala mai yawa.

A lokacin da yake zantawa da wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki, ya ce” Domin watan Ramadan ya wuce ba a daina ayyuka na alheri ba, domin haka al’umma su sani cewa ka da su ce wai donmin sun kamala azumin Ramadan sai wani na badi, to su sani cewa baka da tabbas cewa z aka kai ko kuwa. Saboda haka mu yawaita yin azumin sakamakon Annabi S.A.W ya sunnata mana azumin Litinin da Alhamis, haka kuma bayan sallar farilla babu sallar da ta fi ta kiyamallaili lada domin kuwa Allah ne da kansa yake sakowa saman duniya, domin kiran wanda yake neman wanda yake neman biyan bukata na biya masa”.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa limamin ya ce su na fatan Allah zai rubuta mana lada sakamakon lalurar da a ka samu na kin halartar sallar juma’a lokacin nan na Corona.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish