Connect with us

Labarai

Za mu hukunta duk mai zubar da shara akan hanya – Hukumar kwashe shara

Published

on

Hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli ta jihar kano ta yi barazanar hukunta masu gudanar da aikin fito da shara gafen hanya, ba tare da sanar da hukumar ba gabanin fito da ita ba.

Shugaban hukumar Abdullahi Mu’azu, ya bayyana hakanne a ganawarsu da gidan Radio Dala, lokacin da yake tsokaci kan yadda aka jibge shara akan titin mandawari ba tare da sanar da hukumarba.

Ya kuma hukumar a shirye take ta dinga gaggauta debe dukkanin shara da aka zube a gafen hanya sabo da wani dalili na musamman matukar dai an sanar da ita.

Shugabana hukumar ta kwashe shara Abdullahi Mu’azu ya kuma ce yanzu hukumar zata faradaukan matakin hukunci akan duk wadanda aka samu da jubge sharer a gefen hanya ba tare da sanar da hukumarba.

Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa hukumar ta kuma bukaci ci gaba da samun hadin kan A’umma don samun nasarar tsaftace kano daga shara.

 

Labarai

Laliga : Za a dawo gasar ranar 11 ga watan Yuni

Published

on

Mahukuntan gasar Laliga ta kasar Andulissiya wato Spain, sun tabbatar da cewa za a dawo gasar Laliga a ranar 11 ga watan Yuni mai kamawa inda za a fafata da Real Betis da kuma Sevilla.

Hukumar shirya gasar da hukumar kwallon kafa ta kasar tare da gwamnatin kasar Spain su ne su ka amince da hakan cewa za a kuma dawo gasar na kakar 2021/2022 a ranar 12 ga watan Satumba.

Tun dai a ranar 12 ga watan Maris ne a ka dakatar da gasar sakamakon cutar Corona, sai dai shugaban kasar Pedro Sanchez ya tabbatar da cewa za a iya dawowa gasar a ranar 8 ga watan.

Haka zalika a ranar 17 ga watan Yuni za a dawo gasar Firimiya ta kasar Ingila, a yayin da za a dawo gasar Serie A na kasar Italiya za su dawo ranar 20 ga wata mai kamawa.

Continue Reading

Labarai

Liman: Kulawa da tarbiyyar ‘ya’ya zai rage bata gari da lalacewar matasa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Abubakar Dan Tsakuwa dake unguwar Ja’en Yamma a karamar hukumar Gwale, Mallam Abdulkareem Aliyu, ya yi kira ga iyaye da su kara kulawa da rayuwar ya’yan su domin gudun fadawar su cikin halin shaye-shaye.

Mallam Abdulkareem Aliyu ya yi kiran ne ta cikin hudubar Juma’a da ya gudanar yau a cikin masallacin dake unguwar Ja’en a jihar Kano.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su babu shakka za a rage samun bata gari da lalacewar ya’yan matasa a cikin al’umma. Domin haka ‘ya’ya su kara rubanya biyayyar da su ke yi wa iyayen su, domin su rabauta da rahamar Allah S.W.T.”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, a cikin hudubar Limamin Mallam Abdulkareem Aliyu Dan Tsakuwa ya kuma shawarci al’umma da su kara yawaita addu’o i domin samun sauki daga cutar da a ke fama da ita ta Coronavirus a fadin duniya baki daya.

Continue Reading

Labarai

Kar mutane su shagala cewa sai wata shekarar za su kara yin Azumi -Liman

Published

on

Na’ibin masallacin Juma’a na Quba dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birni a jihar Kano, Ahmad Muhammad Ali, ta cikin hudubar san a yau Juma’a ya ce al’umma da su yi kokarin yin Azimin watan Shawal guda shida na cikin sa akwai falala mai yawa.

A lokacin da yake zantawa da wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki, ya ce” Domin watan Ramadan ya wuce ba a daina ayyuka na alheri ba, domin haka al’umma su sani cewa ka da su ce wai donmin sun kamala azumin Ramadan sai wani na badi, to su sani cewa baka da tabbas cewa z aka kai ko kuwa. Saboda haka mu yawaita yin azumin sakamakon Annabi S.A.W ya sunnata mana azumin Litinin da Alhamis, haka kuma bayan sallar farilla babu sallar da ta fi ta kiyamallaili lada domin kuwa Allah ne da kansa yake sakowa saman duniya, domin kiran wanda yake neman wanda yake neman biyan bukata na biya masa”.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa limamin ya ce su na fatan Allah zai rubuta mana lada sakamakon lalurar da a ka samu na kin halartar sallar juma’a lokacin nan na Corona.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish