Connect with us

Baba Suda

Shirin Baba Suda na ranar Talata 11/02/2020 tare Aliyu Wali

Published

on

A yi sauraro lafiya

Download Now

Baba Suda

‘Yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki – Minista

Published

on

Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki.

 

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB) da nufin samar da wutar lantarki ga ‘yan Afirka miliyan 300 nan da shekarar 2030.

 

Ƙa’idar ta tsara kyawawan manufofi don haɓaka hanyoyin samar da wutar lantarki, ƙara haɓaka makamashi da inganta hanyoyin magance matsalolin dafa abinci mai tsafta ga miliyoyin ‘yan Najeriya – wato Mission 300, kuma muna samun ci gaba mai kyau a kan wannan,” in ji shi.

 

Ya ci gaba da cewa, “Ina mai farin cikin gaya muku cewa cikin ‘yan Afirka miliyan 300 da Bankin Duniya da AfDB ke son cimmawa, Najeriya na kan hanyar da za ta biya ƙasa da kashi 25 cikin 100, wanda ke nufin kusan ‘yan Najeriya miliyan 75. Da muka gabatar da yarjejeniyarmu, sun amince da mu.”

Continue Reading

Baba Suda

Tinubu na bibiyar cigaban da zai kawowa Nigeria daga Turai – Fadar shugaban kasa

Published

on

Biyo bayan kalubalantar shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu dangane da yawan tafiye-Tafiye Zuwa kasashen Turai, fadar shugaban kasa tace shugaban na tafiya ne domin nemoma Nigeria ayyukan cigaba.

 

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da tsare tsare Bayo Onanuga ya fitar tace “shugaban kasa na tafiya kasashen Turai ne saboda nemowa kasar nan cigaba. ”

A baya bayan nan ne Atiku Abubakar da Peter Obi suka kalubalanci shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu kan yawan tafiye-Tafiye da yake yi Zuwa kasashen Turai.

 

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Trending