Connect with us

Labarai

Mahajaciyar jihar Kaduna ta rasu bayan ta dawo daga Arafat

Published

on

Hukumar jin dadin Alhazai ta kasa, NAHCON, ta tabbatar da rasuwar Hasiya Aminu, wata maniyaciyar jihar Kaduna.

Hasiya Ta rasu ne a lokacin da ta ke barci jim kadan, bayan ta dawo daga hawan dutsen Arafat, kamar yadda makwabtanta a cikin tanti suka bayyana hakan.

Dr. Usman Galadima, babban jami’in aiyuka, kuma shugaban ma’aikatan lafiya na kasa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa, har yanzu ba a tantance dalilin mutuwar ta ba.

Tuni aka sanar da iyalan ta rasuwarta, kuma za a yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Usman shi ne mahajjaci na biyu da ya rasu a aikin Hajjin 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi a jihar Nasarawa ita ma ta rasu a makon jiya, bayan gajeriyar rashin lafiya kuma an yi jana’izarta a Makkah.

Zaman Arafa a tsawon yini ya zama wajibi ga kowane mahajjaci ya cika domin yin aikin Hajji.

Alhazan Najeriya daga cikin sama da miliyan daya da ke aikin Hajjin shekarar 2022 a Arafat.

Arafat shi ne wurin da Annabi Muhammad ya gabatar da hudubarsa ta karshe a ranar Juma’a kafin rasuwarsa.

Baba Suda

Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Published

on

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.

Cikakken labarin na Zuwa….

Continue Reading

Baba Suda

Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.

Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.

 

Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

 

 

Continue Reading

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Trending