Manyan Labarai
An kama tsohon kwamishinan ayyukan Kano bisa zargin badakalar kudi

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano tayi awon gaba da tsohon kwamishinan ayyuka na Gwamnatin Ganduje Injiniya Idris Wada Sale bisa zargin karkatar da wasu kudade naira miliyan dubu daya, da sunan Gyaran hanyoyi da magudan ruwa.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta kama Idris Wada ne tare da Karin wasu mutane biyar da ake zargi da hannu cikin waccar badakala.
An dai fitar da kudin ne da sunan Gyaran wasu hanyoyi 30 da Kuma magudan ruwa, tare da baiwa wasu kamfanoni uku, amma ba’ayi aikin ba.
Kamfanonin dai sun Hadar da North Stone construction Nigeria limited, da Arfat multiresources limited, sai Kuma 1step construction Limited.
Mai magana da yawun hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Abba Kabir ya tabbatar da cewa da zarar sun kammala bincike zasu gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya.

Manyan Labarai
Da Ɗumi-ɗumi: An sallami Ɗan Bello bayan kama shi da aka yi a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan mintuna kaɗan da tsare Bello Habib Galadanci da aka fi sani da Ɗan Bello, yanzu haka an sallame shi ba tare da ɓata lokaci ba.
Majiyoyin dai sun bayyana cewa jami’an tsaro ne da ake zargin daga Abuja suke suka kama matashi Bello Habib Galadanci da aka fi sani da Ɗan Bello, a ranar Asabar 12 ga watan Yulin 2025.
Rahotannin sun bayyana cewa an kama Ɗan Bello, ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, a ranar Asabar 12 ga watan Yulin 2025, kamar yadda DW Hausa ta ruwaito.
Sai dai kawo lokacin da muke kammala haɗa wannan labarin jami’an tsaron ba su fitar da wata sanarwar akan lamarin ba, amma hakan akan ne muka yi ƙoƙarin ji daga ɓangaren kakakin rundunar ƴan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar tarho, sai dai kawo yanzu haƙan mu bata cimma ruwa ba.
Tuni dai kama Ɗan Bello ya fara janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman ma da wasu ke alaƙanta kama shi da zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a ranar 21 ga wannan wata na Yulin 2025, akan nuna damuwa kan tsarin bada fansho ga tsofaffin ƴan sanda a Najeriya.

Manyan Labarai
Ku fito sallar roƙon ruwan da za mu gudanar a Kano don neman ruwan sama – Majalisar Malamai

Majalisar malamai ta jihar Kano ta buƙaci al’umma da su fito sallar roƙon ruwa da za ta jagoranta a gobe Asabar, domin neman dacewa da samun ruwan duba da yadda ake ci gaba da fuskantar ƙarancinsa, ga kuma Damuna na ƙara yin nisa.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban majalisar malaman ta jihar Kano Mallam Ibrahim Khalil, ta ce za a gudanar da sallar roƙon ruwan ne tare da addu’o’i, a masallacin Umar Bin Khattab da ke Dangi kan titin Zaria a Kano.
Sanarwar ta kuma buƙaci dukkanin al’umma da su fito sallar roƙon ruwan domin neman taimakon Allah madaukakin Sarki, wajen samun ruwan, bisa ƙarancin ruwa da ake fama da shi duk kuwa da Damina na ci gaba da nisa.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da al’umma ciki har da Manoma ke ci gaba da addu’a kan Allah ya saukar musu da ruwan sama mai albarka, bisa yadda ake ci gaba da fuskantar ƙarancin sa a halin yanzu.

Manyan Labarai
Wasu lauyoyin gwamnatin Kano sun shirya shiga yajin aiki matuƙar kwamishinan Shari’a bai daina yi musu katsalandan ba.

Wasu lauyoyin gwamnatin Kano da suka roki a sakaya sunansu, sun yi barazanar tsunduma yajin aiki, bisa yadda suka zargi kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Isah Haruna Dederi, yana mayar musu da aiki baya.
Lauyoyin sun bayyana fushin su ne akan cewar kwamishinan Shari’a na jihar kano da zargin ya hana su haƙƙoƙinsu na hular gashin doki da rigar zuwa kotu da kuma na’ura mai ƙwaƙwalwa wadda gwamnan Kano ya bayar da umarnin a basu, lamarin kawo yanzu ya gagara.
Kaza lika, luyoyin sun bayyana irin cin dunduniyar da ake yi wa aikinsu da zarar an kawo takardun tuhuma akan zargin fyade ko kuma kisan kai, ko fashi da makami inda suka ce suna kammala bincike idan sun samu mutum da laifi a wasu lokutan sai kwamishin ya yi umarnin a saki mutumin da ake zargin maimakon a kai shi kotun da ta ke da hurumin yi masa Shari’a.
Akan wannan zarge-zargen kwamishinan ta bakin babban sakatare a ma’aikatar Shari’a Barrister Mustafa Muhammad Nuraddin ya musanta wannan zarge-zarge, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.
Ma’aikatar Shari’a dai nan ce ake gudanar da bincike akan manyan laifuka da zarar yansanda sun kammala nasu binciken, domin yin abinda ya dace.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su