Connect with us

Manyan Labarai

NDLEA, ta musanta zargin kashe Matashi a Kano

Published

on

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa reshen jihar Kano, NDLEA, ta yi martani dangane da wani zargi da aka yi wa jami’anta akan cewar sun kashe wani matashi a unguwar Bachirawa karshen kwalta.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, a Kano, Sadik Muhammad Mai gatari, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM Kano a ranar Larbar 03 ga watan Satumban 2025.

“Matashin ya faɗo ne daga saman Bene na wani gidan Wanka, har ma wani Rodi ya cake shi lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa, in ji Sadiq”

Shima wani matashi da aka same su tare da marigayin mai suna Hussaini Sani, ya ce suna tare a lokacin da ma’aikatan suka je wurin da lamarin ya faru, yana mai cewa marigayin ne ma ya hana shi ya buɗe kofar kuma daga karshe sai ya zaga ta baya ya diro daga kan ginin benen.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, mahaifiyar marigayin ta yi kukan cewar, lafiya lau suka rabu da ɗan nata, amma a ƙarshe aka kira ta ofishin hukumar inda aka basu gawarsa, har ma ta ƙara da cewar sun ga Duka har da sara a jikin gawarsa.

Manyan Labarai

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da duk wanda ya take haƙƙin mutane a Nijeriya – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Sustainable Growth initiatives for Human Rights Development, ta ce babu ɗaga ƙafa a tsakanin ta da dukkanin wanda ya take wa wasu haƙƙi a Nijeriya, tana mai cewa za ta yi duk mai yiyuwa don ganin an dawo wa da dukkan wanda aka cuta haƙƙinsa.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Abubakar Musa Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin zantwar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, jim kaɗan bayan da su ka buɗe sabon ofishin ƙungiyar reshen unguwar Ƴanshana da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, ranar Lahadi 09 ga watan Nuwamba, 2025, a Kano

Kwamared Abubakar, ya kuma ce za su ci gaba da hoɓɓasa wajen ganin sun ci gaba da bibiya akan cutar da aka yi wa mutane, don ganin an ƙwato musu haƙƙoƙin da aka danne musu ba tare da gajiya wa ba.

A cewar sa, “Daga cikin kuɗirin mu har da nema wa Matasa ayyukan yi, don yaƙi da rikice-rikicen faɗan Daba, da ƙwacen Wayoyi, da kuma daƙile shaye-shayen kayan maye a tsakanin al’umma, tare da taimakon marayu, don inganta rayuwar su, in ji Abubakar.”

Da yake nasa jawabin, sabon shugaban ƙungiyar ta Sustainable Growth initiatives for Human Rights and Development, reshen unguwar Ƴanshana da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, Kwamared Yunusa Muhammad Ahmad, ya ce a shirye su ke wajen ci gaba da bibiya tare da kare haƙƙin bil’adama.

A yayin taron, an ƙaddamar da shugabannin da za su jagorancin aikin ƙungiyar na sabon ofishin da aka buɗe, wanda Kwamared Yunusa Muhammad Ahmad, zai jagorance su.

Taron ya samu halartar al’umma da dama, kuma ciki har da limamin masallacin unguwar Ƴanshana Mallam Muhktar, da mai unguwar yankin, da kuma kwamandan ƙungiyar sintirin Bijilante na unguwar, da dai sauransu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kotu ta sanya ranar yanke wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu hukunci

Published

on

Yanzu haka Babbar kotun Tarayya da ke birnin Abuja, ta saka ranar 20 ga watan Nuwamban 2025, domin yanke wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu hukunci akan tuhumar da ake yi masa.

Mai shari’a, a kotun, James Omotosho, ne ya bayyana haka a zaman kotun na ranar Juma’a 07 ga watan Nuwamba, 2025, a kan shari’ar da ake yi wa Kanu kan zargin ta’addanci.

Maishari’a James, ya ɗauki matakin ne bayan da Nnamdi Kanu, ya kasa fara kare kansa bayan kwana shida da kotun ta ba shi domin yin hakan, kamar yadda kafar BBC ta ruwaito.

Har ila yau, kotun ta kuma ce bayan Kanu ya gaza amfani da damar da aka ba shi domin kare kansa daga tuhumar da ake yi amsa, bai kamata ya ci gaba da iƙirarin da yake yi cewa an hana damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na jin bahasinsa.

Idan ba a manta ba, a ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai, kotun ta ɗage zamanta domin bai wa wanda ake ƙara damar kare kansa kamar yadda ya buƙata a baya, sai dai a yanzu ya kasa kare kan nasa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kotu ta yanke wa magidanci hukuncin sharar Masallaci na tsawon wata 6 a Kano

Published

on

Kotun shari’ar Musulunci mai lamba daya da ke zamanta a Kofar Kudu, ta yanke wa wani magidanci hukuncin share Masallacin Wudilawa na tsawon wata shida bayan samun sa da laifin dukan matarsa.

Tunda fari, matar ta garzaya Ofishin ‘yan sanda ne da ke Jakara a Kano, inda ta yi ƙarar mijinta cewar ya doka mata Muciya a kanta sakamakon haka har sai da ta yi jinya.

Bayan Jin korafinta ne aka turasu Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba daya da ke Kofar Kudu karkashin jagorancin mai sharia Shamsuddin Ado Abdullahi Unguwar Gini.

An kuma gurfanar da shi a kotun, bisa tuhumar samar da rauni, kuma bayan karanto masa ya amsa laifinsa, amma lauyansa wato daya daga cikin lauyan taimakon marasa ƙarfi Barista Muhammad Ali Tijjani, ya roƙi ayi masa sassauci.

Hakan ya sa kotu ta amince, ta kuma yanke masa hukuncin ɗaurin talala, inda zai share masallacin Wudilawa na tsawon watanni shida a sati sau uku.

Haka kuma, an tsalala masa bulala goma, kuma an umarcr shi da ya biya matar kudin maganin da ta kashe wato Naira dubu goma, kamar yadda Freedom Radio ta ruwaito.

Continue Reading

Trending