Connect with us

Labarai

Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda

Published

on

Shahararren mawakin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Hamisu Breaker ya mika kan sa ga jami’an ‘yan sanda da yammacin ranar Alhamis biyo bayan karawa wani mutum mai suna Sani Kamal Muhammed, mota a mahadar titi dake Dan Agundi a yammacin jiya Laraba.

Sai dai tun a jiyan aka yi zargin Hamisu Breaker, ya arce wanda kuma a yanzu haka ya kawo kan sa sashin na MTD domin bayar da bayanin yadda lamarin ya faru.

Domin jin cikakken rahotan saurari wannan.

Baba Suda

Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Published

on

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.

Cikakken labarin na Zuwa….

Continue Reading

Baba Suda

Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.

Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.

 

Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

 

 

Continue Reading

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Trending