Connect with us

Matattarar Alheri

Saurari Shirin Matattarar Alheri na ranar 27-09-2019 -Hadiza Balanti

Published

on

Matattarar Alheri

Jami’an tsaro sun kama mamallakin ginin da ya ruftawa mutane sama da 10 har aka rasa rayuka a Kuntau 

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mamallakin ginin benen nan mai hawa uku, da ya ruftawa mutane sama da goma a unguwar Kuntau, da ke ƙaramar hukumar Gwale, a ranar Juma’a.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM Kano, a yau Asabar.

SP Kiyawa, ya kuma ce tuni rundunar ƴan sandan ta fara gudanar da bincike akan faruwar al’amarin, kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da mamallakin ginin gaban kotu, domin fuskantar hukunci.

“Za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar tsara Birane ta Jihar Kano domin ci gaba da gudanar da bincike akan yadda aka baza bin ƙa’idojin da suka kamata wajen yin ginin benen, “in ji SP Kiyawa”.

Idan dai ba’a manta ba a ranar Juma’a ne 26 ga watan Afrilun 2024, wani ginin bene mai hawa uku ya ruftawa Leburori sama da goma lokacin da suke aikin ginin benen, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku daga cikin su.

Continue Reading

Matattarar Alheri

Saurari Shirin Matattarar Alheri na ranar 20-09-2019 -Hadiza Balanti

Published

on

Shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi zamantakewar al’umma.

Download Now

Ayi sauraro lafiya.

Continue Reading

Trending