Manyan Labarai
Shirin Birnin Dala Ya Cika Shekara Daya.

A karon farko gidan Rediyon Dala FM ya shirya kasaitaccen taron murnar cika shekara daya da fara gabatar da wannan kayataccen wasan kwaikwayo mai farin jini na birnin Dala.
Dubun dubatar masoya wannan shiri na Birnin Dala ne, suka halacci wannan taro a ranar asabar,03,03,2018.
Kamar yanda aka tsara anfara taron ne da misalin karfe uku na yamma, yayin da jaruman da suke taka rawa cikin wannan wasan kwaikwayo suka shirya tsaf! Dan gamsar da masoyansu a zahiri ta hanyar gabatar da nuna wasu muhimman gidaje na musamman, dake kunshe cikin wannan wasan kwaikwayo dake nuni da zallar gudanarwar sarautar wasu masarautu guda uku; Masarautar yamma ta sarki Toro,wadda ke nuni da gudanarwar wata masarauta ta marasa addini,
sannan masarautar birnin Dala ta Sarki Ukasha dan sarki Kinana, jikan sarki Nawwasu,wacce ke nuna ainihin gudanarwar masarauta a kasar Hausa,
yayin da a karshe aka shirya nuna fitowar Masaurautar Mazugal ta Sarauniya Bilkisu, masaurautar dake da alaka da Larabawa.
Duk da mashirya wannan taro sunyi iyakar kokarinsu dan gabatar da dukkan abinda aka tsara, sai dai hakansu bai kai ga cimma ruwa ba, sakamakon yawan al’umar da suka taru dan shaida wannan taro, wanda hakan ba komai yake nunawa ba face, hakikanin farin jini, da kuma karbuwa da shirin yasamu a gurin masu sauraro. Babban abin burgewa ga wannan taro bai wuce yadda a cikinsa aka gabatar da wasannin masu burgewa dake nuni da Al’adun gargajiyar Bahaushe.
An kammala wannan taro ne da misalin karfe shidda na yamma,amma fitowa ta gagari yan wasan saboda yawan al’ummar dake muradin daukar hotunan tarihi dasu.


Manyan Labarai
An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Manyan Labarai
Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.
Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.
A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.
Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.
“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.
Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

Manyan Labarai
Mun kama mutane 14 bisa zargin su kan kisan gillan da aka yi wa Mafarauta a Edo – Ƴan Sanda

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta tabbatar da kama mutane 14 da ake zargi da hannu kan kisan da aka yi wa wasu Mafarauta kuma Hausawa ƴan Arewa a garin Uromi da ke jihar Edo.
Sufeton ƴan sandan kasar IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar na ƙasa ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce, tuni Egbetokun ya bai wa mataimakin sa mai kula da babban sashin binciken manyan laifuka na rundunar DIG Sadik Abubakar, umarnin da ya ja ragamar bincike don gano sahihin abinda ya faru tare da ɗaukar matakin da ya dace akan al’amarin.
Idan dai ba’a manta ba, rahotanni sun bayyana cewar mafarautan sun baro birnin Fatakwal ne na jihar Ribas, suna kan hanyar su ta komawa Kano, don gudanar da bikin ƙaramar Sallah, suka gamu da wasu Ƴan Bijilante a garin Uromi da ke jihar Edo, lamarin da suka zarge su da cewa ƴan garkuwa da mutane ne bisa samun su da bindigar gargajiya duk kuwa da sun ce suna da lasisin bindigun.
A cewar jaridar Daily Trust, duk da haka ƴan bijilanten suka sakko da mutanen su aƙalla 27, daga motar dakon kaya ta Ɗangote, suna dukan su, har su ka ƙone kusan mutane 16 daga cikin su, ko da dai wani da ya tsira da ransa ya ce, mutane 20 aka kone, su biyar suka tsira, yayin da mutane biyu suke Asibiti.
IGP Egbetokun, ya kuma ce jim kaɗan da faruwar lamarin ne jami’an rundunar ƴan sanda ta jihar Edo, suka baza koma tare da cafke mutane 14 da ake zargi da hannu kan lamarin, kuma yanzu haka ana faɗaɗa bincike akan batun.
Tuni dai ƴan ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama, da Ƴan Siyasa, da sauran al’ummar Najeriya, suke ta kiraye-kirayen ganin an ɗauki matakin da ya dace akan lamarin, don zama izina ga ƴan baya.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su