Connect with us

Labarai

INUWAR JAMA’AR KANO TA FAYYACE WASU KALUBALE DATA FUSKANTA A BANA WAJEN GUDANAR DA AYYUKANTA

Published

on

Inuwar Jama’ar Kano tace kalubalen da ta fuskanta a shekarar da ta gabata ya biyo bayan karancin kudin shiga da ta fuskanta a shekarar 2017.
Wata takarda mai dauke da sahannun Shugaban Inuwar Jama’ar Kano Alhaji Sani Zango,yayin taron sun a shekara shekara da ta saba gudanarwa.
A wata takarda mai dauke da sa hannun Daraktan Inuwar Jama’ar Kano Alhaji Muhammadu Sani Zango, zauren Inuwar Kanon yace karancin kudin shiga na daya daga cikin manyan kalubalen da suka fuskanta ashekarar da ta gabata haka yasa basu samu damar tallafawa makarantu ba kamar yadda suka saba,
sai dai duk da hakan Inuwar Jama’ar Kano ta mai da hankali wajen tallafawa cigaban Unguwanni da shirye shirye wajen bunkasa Ilimi da alamuran siyasa tare da bayar da gudun mawa wajen yaki da Shaye Shaye da makamantansu.
Haka zalika Inuwar Jama’ar Kano ta taka muhimmiyar rawa wajen wajen wayar da kai game da harkar Almajirci ta kafafen yada labarai tare da shirya taro don tatara bayanai suka kuma mikawa Gwamnatin Jiha.
Dangane da sauyin fasalin kasa kuwa Inuwar Jama’ar Kano ta kafa kwamiti kwamitin da zai fitar da matsaya kan Ra’ayin Jama’ar Kano dangane da batun.
A karshe Darktan Inuwar Jam’ar Kano Alhaji Muhammadu Sani Zango, ya kuma ce zasu sanya kalubalen da ke gaban su a wannan shekarar ta 2018 don magancesu musamman karancin kudin Shiga.

Labarai

Zamu magance ƙalubalen da ake samu a fannin ilimi mai zurfi – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jahar kano ta sha alwashin mangance dukkanin wani ƙalubale a fannin ilimi mai zurfi a fadin jihar Kano.

Kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Ibrahim Yusif kofar mata, ne ya
bayyana hakan a yayin taron yaye daliban kwalejin ilimi ta Aminu
Kano (AKCOE), da ya gudana a ranar Alhamis.

Y kuma ce yanzu haka tattaunawa tayi nisa a hukumance akan bukatar kwalejin dan ganin ta samu wadataccenf ilin da za ta gina jami’a.

Dakta Ibrahim kofar mata ya bayyana gamsuwa da tsarin da kwalejin take bi wajen gudanar da karatu, inda ya kuma ja hankalin dalibai 40 da suka karbi shaidar kammala karatun NCE,
da su zama ababen koyi.

Da yake nasa jawabin shugaban kwalejin Dr. Ayuba Ahmad Muhammad, ya ce da zarar sun shiga sabon tsari za su fara da daukar dalibai yan asalin jahar Kano mutum dubu daya kyauta, tare da biyawa ‘yan makarantar
kudi sama da Naira miliyan 300 yan asalin jahar kano dan
karfafawa matasa gwiwa.

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa al’umma da dama ne suka samu damar halartar taron daga guraren daban-daban na jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Continue Reading

Labarai

Bama jin daɗin yadda wasu iyaye suke hana ƴaƴan su maza auren mu – Budurwa mai larurar Ƙafa

Published

on

Wata matashiyar budurwa mai buƙata ta musamman dake da lalurar Ƙafa Samira Ahmad Tijjani, ta nuna rashin jin daɗin ta, bisa yadda mafi yawan iyaye suke nunawa masu lalurar ƙyama, wajen hana ƴaƴan su auren masu lalurar ƙafar lamarin da yasa al’amarin ke matuƙar ɓata musu rai.

A zantawar wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, da budurwar ta ce, mafi yawancin su mata masu lalurar ƙafar sun ma fi mata masu lafiya iya Girki, da sauran ayyukan yau da kullum.

Ta ci gaba da cewa, “Amma abin takaici sai a rinƙa nuna mana ƙyama, ko kuma wariya musamman ma wajen neman aure, bayan kuma ba mu muka yiwa kan mu halitta ba, “in ji Samira”.

Ta kuma ce abinda wasu daga cikin iyaye suke yi musu kan nuna ƴaƴan su ba za su aure mai lalurar Kafa ba, basa jin daɗin hakan, shi yasa ma ta fito domin ta sanarwa al’umma domin gujewa hakan.

A cewar ta, “Ko nima nayi soyayya mara misaltuwa da samari masu lafiyar Ƙafa, amma mahaifiyar ɗaya daga cikin su ta ce ita ba wai bata sona ba, amma tana jin kunyar ta tuna ni a cikin mutane cewar a zummar matar ɗan ta”.

Daga bisani dai ta yi kira ga al’umma da su dai na nuna ƙyamar ko kuma nuna wariya a gare su, bisa yadda iyayen su suke matuƙar shiga cikin damuwa a duk lokacin da aka nuna musu wariyar.

Continue Reading

Labarai

Bayan ƙaddamar da tallafi: Zamu rinƙa raba tallafin jarin Naira dubu 50,000 ga iyaye Mata duk wata – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnatin jihar kano ta kaddamar da rabon taffin kuɗaɗe ga iyaye mata dake kananan hukumoni 44 su 5,200 a fadin jihar nan, domin su dogara da kan su.

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya jagoranci ƙaddamar da rabon tallafin kudaɗen har Naira 50,000 ga iyaye mata dake kananan hukomini 44 a yau Talata, wanda ya gudana a ɗakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnatin kano.

Abba Kabir Yusif ya kuma ce hakan na daga cikin alkawarin da suka yiwa matam tun a lokacin yaƙin neman zaben shekarar 2023 da ta gabata, inda ya ce iyaye mata na da bukatar jari domin dogaro da kan su, musamman ma wajen yin sana’o’i irin su Kosai, Awara, Gurasa da Bandasho da dai sauran ƙananan sana’o’i.

Aƙalla dai Mata ɗari-ɗari ne 100, za su amfana daga kananan hukumomi 36 na Karkara, da kuma na cikin birni takwas 8, kuma iyaye mata dari biyu-biyu (200) za su amfana da tallafin duka dai domin su dogaro da kan su.

Wakilinmu Abba Haruna Idris ya rawaito cewa Gwamnan Kano Abba Kabir, ya ƙara da cewa wannan ba shine na karshe ba, za su rinƙa tallafawara duk wata-wata, domin samawa iyaye mata sana’oin dogaro da kai, ta yadda zasu rinƙa haɓɓaka tattalin arzikin jihar kano.

Continue Reading

Trending