Labarai
Mai taimakon marayu zaiyi makotaka da Annabi (s.a.w) a Aljannah

Na’ibin limamin masallaci masjid Ibadurrahman dake Ja’en Shago tara malam Muhammad jaen yayi kira ga al’umma baki daya da suri ka tallafawa marayu duba da irin garabasar dake tartare dayin hakan.
Malam Muhammad ya kuma kara da cewa hadith yazo kan duk Wanda yake daukar nauyin maraya koda kuwa guda daya ne to Allah (SWA) zai bashi makotaka da Ma’aikin Allah (SAW) a gidan aljannah.

Baba Suda
‘Yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki – Minista

Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki.
Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB) da nufin samar da wutar lantarki ga ‘yan Afirka miliyan 300 nan da shekarar 2030.
Ƙa’idar ta tsara kyawawan manufofi don haɓaka hanyoyin samar da wutar lantarki, ƙara haɓaka makamashi da inganta hanyoyin magance matsalolin dafa abinci mai tsafta ga miliyoyin ‘yan Najeriya – wato Mission 300, kuma muna samun ci gaba mai kyau a kan wannan,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Ina mai farin cikin gaya muku cewa cikin ‘yan Afirka miliyan 300 da Bankin Duniya da AfDB ke son cimmawa, Najeriya na kan hanyar da za ta biya ƙasa da kashi 25 cikin 100, wanda ke nufin kusan ‘yan Najeriya miliyan 75. Da muka gabatar da yarjejeniyarmu, sun amince da mu.”

Daurin Boye
Mun kafa kwamiti domin rage farashin – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zaiyi Duba kan hanyoyin shigo da abinci domin rage farashin sa da kaso 50.
Kwamitin dai dake karkashin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima zai yi aiki ne da wasu ministoci, domin ganin an wadatar Nigeria da abinci.
Yayin jawabin sa, Sanata Kashim Shettima yace hakan wani bangare NE na kara inganta tattalin arziki da shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu ke kokari.

Labarai
Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.
A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su