Connect with us

Labarai

Tashin Gobara ya yi sanadiyyar konewar dukiya ta mulyoyi a Kano

Published

on

‘Yan kasuwa da sama sun yi asarar dukiyoyin su na miliyoyin Naira a wata gobara da ta kone shaguna da dama a garin Gwarzo da ke karamar hukumar ta Gwarzo a jihar Kano.

Bayanin hakan zuwa ne ta cikin wata sanarwa da Jami’in yada labarai na shiyyar karamar hukumar Gwarzo Rabi’u Khalil ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai bayan faruwar al’amarin.

Rahotanni sun bayyana cewa Gobarar ta faru ne a ranar Litinin da ta gabata, inda ta jefa wadanda lamarin ya shafa a cikin mawuyacin hali, sakamakon yadda masu shagunan suke ta kuka saboda asarar tarin dukiyoyin da suka yi.

Yayin da yake tabbatar da faruwar al’amarin, lokacin da yake zantawa da sashin yada labarai na shiyyar karamar hukumar Gwarzo, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Kwamared Saminu Abdullahi Sa’id, ya ce gobarar ta fara ne da tsakar daren ranar Lahadin da ta gabata kuma ta dauki jami’ansu har zuwa safiyar Litinin kafin daga bisani suka samu nasarar kashe gobarar.

“Gobarar ta kone shaguna da dama, yayin da ta lalata dukiyoyi na miliyoyin Nairori, amma babu wani rauni ko asarar rai a yayin gobarar, “in ji shi”.

Daya daga cikin wadanda lamarin gobarar ya shafa mai suna Dayyabu Lawan Bala ya ce, ya yi asarar kadarori na sama da na Naira miliyan 5 ciki har da shagonsa, inda ya yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su taimaka musu domin rage musu radadin halin da suka shiga.

Bayan faruwar lamarin ne al’umma da dama suka rinka zuwa yiwa ‘yan kasuwar Jaje, kuma ciki har da dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwarzo ta tarayya Hon. Abdulahi Mu’azu Babangandu wanda ya bada tallafin kudi naira dubu dari biyar (#500,000) ga wadanda abin ya shafa bayan ya ziyarci wurin da gobrar ta tashi.

Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.

Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala

Published

on

Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.

“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.

Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.

Continue Reading

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Trending