Connect with us

Manyan Labarai

Daliban Najeriya dubu 15 za su shiga tsaka mai wuya bayan haramta digirin Benin – Kungiyar Dalibai

Published

on

Kungiyar daliban kasar nan ta bukaci gwamnatin Najeriya, da ta sake nazarta matakin haramta digirin Jamhuriyyar Benin, a cikin kasar lura da yadda hakan zai shafi akalla dalibai dubu 15 da yanzu haka ke tsaka da karatu a Coutonu.

Rahotanni sun bayyana cewa matakin haramta amfani da digirin ta Benin ya biyo rahoton yadda wani dan jarida ya yi basaja tare da kammala digirinsa cikin watanni 2 a kasar, tare da dawowa Najeriyar don fara bautar kasa, daga bisani ya saki abinda ya faru.

Akan kuma wannan dambarwar ne gwamnatin kasar ta haramta digirin daga makwabciyarta wato Coutonu, yayin da daga bisani ta fadada haramcin zuwa wasu kasashe da suka kunshi Uganda da Kenya da kuma Togo da Jamhuriyar Nijar, baya ga kasar Ghana.

Akan batun dakatarwar ne kuma shugaban kungiyar daliban Najeriya da ke karatu a Benin Ugochukwu Favour, yayin zantawarsa da gidan talabijin na Channels, ya roki gwamnatin kasar kan ta sake nazartar matakin tare da tantance ingancin jami’o’in gabanin zartas da makamancin hukuncin, kamar yadda kafar yada labarai ta RFI Hausa ta rawaito.

Ya ce akwai bukatar hukunta iya jami’ar da aka samu da tafka badakalar mai-makon yin kudin goro ga ilahirin jami’o’in da ke Benin din.

Ya kuma kara da cewar yanzu haka akwai daliban Najeriya fiye da dubu 15 da ke karatu a jami’o’I daban-daban da ke cikin kasar ta Benin, kuma daukar matakin kai tsaye zai wargaza rayuwarsu, musamman ma ta karatunsu.

Rahotanni sun yi nuni da cewar sai dai kuma ministan Ilimi na Najeriya, Tahir Mamman ya bayyana cewa, baya ko tausayawa daliban da ke karatu a kasashen da aka haramta, mai-makon haka ma kamata ya yi a tuhume su da aikata babban laifi.

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Continue Reading

Manyan Labarai

An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Continue Reading

Manyan Labarai

Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Published

on

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.

Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.

A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.

Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.

“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.

Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

Continue Reading

Trending