Connect with us

Manyan Labarai

Yanzu-yanzu: An aikewa majalisar dokoki takardar neman rushe Masarautu hudu da dawo da Sunusi Sarkin Kano

Published

on

Yanzu haka wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta rubutawa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman rushe dokar kafa karin masarautu hudu da suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda gwamnatin da ta gabata ta kafa, tare da neman a maido da Sarkin Kano na 14 Mallam Muhammadu Sanusi II.

Bayanin kungiyar na zuwa ne ta cikin wata wasika mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024, da aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, inda ta ce rusa masarautu tare da maido da Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin sarkin Kano “zai samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar Kano.

Jaridar Kadaura24 ta rawaito cewa rubutun wasikar na cewa:

“Mun rubuto wasikar ne don rokon wannan majalisar da ta yi gyara a dokar masarautun jihar kano, muna so a gyara dokar ta yadda za’a rushe sabbin masarautun da aka kirkira guda hudu a shekarun baya.

Wasikar ta ci gaba da cewa, “Mun yi imanin idan har aka hade masarautun suka koma masarauta daya za’a fi samun hadin kai da ci gaban al’ummar Kano”.

“Kuma rushe masarautun gusa hudu zai inganta zaman lafiya da tattalin arzikin jihar kano, don haka muke neman wannan gida zai yi abun da ya da ce dai-dai da doka”.

Wasikar ta kara da cewa, “Mun amince da ikon da Majalisar Dokokin Jihar Kano ke da shi kan harkokin tafiyar da masarautu”.

“Duk da haka, cikin kaskantar da kai muna rokon majalissa da ta sake duba matakin tsige Sarki Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki da akayi a baya, Imaninmu ya ta’allaka ne a kan cewa mayar da shi kan karagar mulki za ta samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano, “in ji wasikar”.

Manyan Labarai

Lauya ya nemi a biya Abduljabbar Kabara Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Published

on

Babbar kotun jaha a ɓangaren ɗaukaka ƙara ƙarƙashin masu Shari’a Aisha Mahamud, da Nasir Saminu, sun sanya ranar 9 ga wannan watan da ake ciki dan ci gaba da sauraron daukaka karar, da Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar.

A zaman kotun na yau lauyan Abduljabbar, Barrista Yusuf Sadik, ya shaidawa kotun cewar a shirye suke a fara sauraron daukaka karar.

Sai dai lauyan gwamnati ya bayyana cewar basu shirya ba dan haka a sanya wata ranar.

Lauyan Abduljabbar ya shaidawa kotun cewar sun bai wa lauyoyin gwamnati takardun bayaninsu tun a watan 2 da ya gabata, dan haka a biya Abduljabbarun Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Sai dai lauyan gwamnati ya yi suka an kuma duba lokacin da aka bada takardun a watan uku ne dan haka wannan lauya ya janye rokonsa.

Daga nan ne kotun ta sanya ranar 9 ga watan nan na Mayu da ake ciki, an kuma umarci lauyan gwamnati da ya yi martani idan yana da shi kafin wannnan rana.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Abduljabbar Nasir Kabara dai ya daukaka karar ne dan kalubalantar hukuncin kutun shari’ar muslunci ta kofar kudu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanya rataya bisa samunsa da laifin ɓatanci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gobara ta ƙone tarin kayayyaki a gidan tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Published

on

Wata Gobara ta tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau dake Mudubawa a yankin Karamar hukumar Nassarawa, inda ta ƙone wasu kayayyaki a ɗakin matar sa waɗanda zuwa yanzu ba’a ƙayyade ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faro ne daga ɗakin Girki na matar tsohon gwamnan Hajiya Halima Shekarau, tun yammacin jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun tsohon Gwamnan Malam Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta shafi iya daki ɗaya ne a cikin gidan dake Munduɓawa.

A nasa ɓangaren kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce da zarar sun kammala tattara alƙaluma da bincike, zai magantu a nan gaba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Trending