Labarai
Zamu dauki matakin doka akan masu cutar mutane a harkar Gidaje, Filotai da hayar Gida a Kano – Kungiyar KAFADA
Kungiyar masu hada hadar siyar da gidaje, da bada hayar su, da kuma siyar da Filotai KAFADA, ta ce ba za ta saurara wa dukkanin wasu bata garin da suke shigowa cikin harkar suna cutar mutane tare da bata musu suna ba.
Shugaban kungiyar ta kasa reshen jihar Kano Isah Jibril Isah Kaci kasa, ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM a yau Laraba, ya ce akwai bukatar kulawar mutane don gujewa fadawa komar bata garin.
Da yake nasa jawabin mataimakin shugaban kungiyar ta KAFADA, Abdulhadi Muhammad Iyan Hadi, ya ce a kokarinsu na kakkabe bata garin cikin su ne ma ya sa suka kulla alaka da jami’an tsaro, domin kara tsaftace harkar.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa kungiyar ta kuma shawarci al’umma da su kara kula a cikin unguwanninsu da bakin da suke shigowa don kaucewa haduwa da bata gari.
Labarai
Za’a fara yiwa ɗalibai gwajin Ƙwaya kafin su shiga kwaleji a Kano
Kwalejin fasaha ta jihar Kano, Poly Technic, za ta fara gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban da za su nemi gurbin karatu a shekara mai zuwa ta 2025.
Shugaban kwalejin Dakta Abubakar Umar Faruk, ne ya bayyana hakan yau Asabar, a yayin taron wayar da kan ɗalibai illar Shan miyagun ƙwayoyi domin kare kai daga cin zarafin Jinsi, da ƙungiyar ɗaliban kwalejin ta shirya.
Taron ya gudana ne a ɗakin taro na Farfesa Hafiz Abubakar, da ke reshen kwalejin na matan fada, da ke jihar Kano.
Shugaban kwalejin wanda maga-takardar makarantar Muhktar Ibrahim Bello, ya wakilta, ya ƙara da cewar matakin gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyin hakan zai taimaka wajen yaƙi da miyagun kwayoyi a kwalejin da ma jihar Kano.
Da yake na sa jawabin akan dabarun kaucewa Shaye-shaye kwamandan hukumar NDLEA ta ƙasa reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, wanda mataimakiyar sa Hajjiya Aisha Hamidu,ta wakilta, ya ce ta hanyar wayar da kai ne ɗalibai da matasa za su gane illar amfani da miyagun ƙwayoyi.
A nasa ɓangaren shugaban kungiyar ɗaliban ƴan asaln jihar Kano, da suka shirya taron Abdurrazak Nasiru Ahali, ya ce sun shirya taron ne domin wayar da kan ɗalibai akan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, ta yadda za su kaucewa amfani da su.
Taron faɗakar da ɗaliban illar miyagun kwayoyin yasamu halartar malamai,masu rike da sarautar gargajiya da sauran masana a fannin Ilimi da lafiya.
Labarai
Mun ƙaddamar da kwamitin karta-kwana da zai kawo ƙarshen cutttuka masu yaɗuwa a Kano – Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da kwamitin kar-ta kwana da zai dunga shiga lungu da saƙo na jihar, domin yin riga-kafin cututtuka don kare jihar daga barazanar kamuwa da cutuka masu yaɗuwa.
Kwamitin dai an kafashi ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin Gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda zai jagoranta.
Da yake ƙaddamar da kwamitin a ranar Alhamis gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa kwamitin da aka ƙaddamar zai gudanar da aikin sa ne yadda ya kamata, ta yadda za’a dunga shiga lungu da saƙo na jihar domin magance duk wasu cututtuka masu yaɗuwa a faɗin jihar.
“Muna kuma kira ga dukkanin waɗanda aka naɗa a wannan Kwamitin da su tabbatar da cewa sun gudanar da aikin su yadda ya kamata wajen riƙe gaskiya da amana, “in ji gwamnan”.
Da yake jawabi a matsayin shugaban kwamitin mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tabbatar wa da gwamnan cewa za su gudanar da aikin su yadda ya kamata domin ciyar da Kano gaba da kare ta daga barazanar cututtuka masu yaɗuwa.
Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, an samarwa da kwamitin baburan hawa guda 88 inda aka karrama masu maganin gargajiya da lambar girmamawa yayin taron ƙaddamar da kwamitin.
Labarai
An gurfanar da matasan da ake zargi da sace bindiga AK-47 a Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da waɗanda ake zargi sace bindiga kirar AK-47, a Kotu, yayin zanga-zanga.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya sanar da hakan a shafin sa na sada zumunta, ya ce an gurfanar dasu a gaban kotu, yau Litinin a kotu mai lamba 54 da ke Nomand-sland a jihar Kano.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su