Connect with us

Manyan Labarai

Tsadar Rayuwa: Kungiyar kwadago za ta tsunduma yajin aikin kwanaki biyu

Published

on

Ƙungiyar Ƙwadago ta kasa, NLC ta ayyana gudanar da gagarumar zanga-zangar kwana biyu a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.

Shugaban ƙungiyar na kasa Kwamared, Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a shalkwatar ƙungiyar lokacin wani taron gaggawa da ƙungiyar ta kira ranar a ranar Juma’ar nan.

Mista Ajaero ya ce an ɗauki matakin zanga-zangar ne bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 14 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar nan.

Hakazalika Ƙungiyar dai ta bai wa gwamnati wa’adin ne domin ɓullo da wasu sauye-sauyen da za su magance matsalolin da ‘yan ƙasar nan ke fuskanta sakamakon matsain rayuwar da ake fama musamman ma ga Talaka.

Manyan Labarai

Siyasantar da Tsaro ne ke ƙara ta’azzara faɗan Daba a Kano – Masanin Tsaro

Published

on

Yayin da faɗan Daba ke ƙara zama alaƙaƙai tsakanin al’umma a sassan birnin Kano, masanin tsaron nan Ditective Auwal Bala Durumin Iya, ya ce matuƙar ana son a daƙile lamarin, sai gwamnati ta cire Siyasantar da tsaron, tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kan da ya dace.

Ditective Auwal Bala ya bayyana hakan ne a zantawar sa da tashar Dala FM, a lokacin da yake tsokaci kan hanyoyin da za a bi domin daƙile rikice-rikicen faɗan dabar da ƙwacen Waya da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye a jihar.

“Baya ga batun bai wa jami’an tsaro haɗin kan, da kuma wadata su da kayan aiki, akwai kuma buƙatar suma al’umma su rinƙa bai wa jami’an tsaron bayanan sirri, don kawo karshen faɗan dabar a faɗin jihar Kano, “in ji shi”.

Ditective Durumin Iya, ya ƙara da cewar, suma Ƴan Siyasa ya kamata su kaucewa siyasantar da harkokin Tsaro, da gujewa ɗaukar nauyin Ƴan Dabar, ko kuma fito dasu idan aka kamasu, saboda hakan yana taka rawa wajen ƙara ta’azzara Ayyukan Daba.

 

Jihar Kano dai, ta yi ƙaurin suna wajen fuskantar rikice-rikicen faɗan Daba, da ƙwacen Waya, da kuma sha da dillancin kayan maye, ko da dai tuni hukumomi suka tashi haiƙan domin magance matsalolin.

Continue Reading

Manyan Labarai

Jarabawar JAMB: An dakatar da duban tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025 – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin duban tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025, domin bai wa ɗaliban da za su rubuta jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB, damar isa cibiyoyin zana jarrabawar a kan lokaci.

Kwamishinan muhalli da kula da sauyin yanayi na jihar Kano Dakta Dahir Hashim Muhammad ne ya sanar da hakan, a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Sama’ila Garba Gwammaja ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, an dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin bai wa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ta JAMB, ba tare da wata matsala ba.

“Muna mai tabbatar wa mazauna Kano cewa, dakatarwar duban tsaftar muhallin na wucin gadi ne a iya wannan watan kawai, kuma za a ci gaba da aikin tsaftar muhallin a watan Mayun 2025, “in ji Dr. Ɗahir”

Kwamishinan ya kuma yi kira ga mazauna jihar Kano, da su ba hukuma hadin kai da fahimtar dalilin da ya sa aka yanke wannan hukunci, musamman na ganin cewa ayyukan tsaftar muhalli ba su ci karo da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a jihar ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Babu ɗaga Ƙafa tsakanin mu da Ƴan Daba da masu ƙwacen Waya a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Wayoyin jama’a da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye ta Anty Snaching Phone, ta gargaɗi matasan da suke addabar al’umma da faɗan Daba a cikin birnin jihar Kano, da su ƙauracewa hakan domin ba za su saurarawa dukkanin wanda ya faɗa komar su ba.

Kwamandan rundunar tsaron a jihar Kano Inuwa Salisu Sharaɗa, shi ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, ya ce duk wanda suka kama da laifi musamman ma na faɗan Daba, ko ƙwacen waya ko kuma sha da dillancin kayan maye, za a ɗauki tsattsauran mataki akan sa.

 

“Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu ƙwacen Wayoyin jama’a, da Faɗan Daba, da kuma masu Sha da dallancin kayan Maye a jihar Kano, kuma duk wanda mu ka kama sai mun miƙa shi gurin da ya dace don ɗaukar Mataki, “in ji Inuwa Sharaɗa”.

 

Ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara sanya idanu wajen kula akan shige da ficen ƴaƴan su, ta yadda za su zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Continue Reading

Trending