Connect with us

Labarai

Zanga-zangar -Yan magani: Zamu duba batun kulle shagunan su da akayi – Gwamnatin Kano

Published

on

Ƴan kasuwar magani dake jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan titin gidan gwamnatin jihar Kano, kan yadda suka ce an tilasta musu tashi daga kasuwar su tare da kuma kulle musu shaguna da dama.

Shugaban Ƴan ƙungiyar ƴan maganin a jihar Alhaji Musbahu Yahaya, ne ya jagorancin zanga-zangar lumana inda suke kira ga gwamnati da tayi duba da irin halin matsi da suke ciki a wannan lokaci wajen kawo musu daukin gaggawa.

Alhaji Musbahu Yahaya ya bayyana dalilin su na ƙin amincewa da komawa kasuwar Ɗangoro, inda ya ce komawar su kasuwar Dangoron ka iya haifar musu da koma baya a sana’ar su.

Da yake jawabi Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da ya sami wakilcin shugaban ma’aikatar fadar gwamnati Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya ce gwamnati zata bibiyi yadda aka rufe shagunan ƴan kasuwar maganin dake jihar, domin samarwa da ƴan kasuwar sassauci kan yadda a yanzu suka shafe kwanaki 3 ba tare da sun gudanar da kasuwancin su ba.

Gwamnatin kano ta kuma yi kira ga shugaban ƙungiyar wajen tattaunawar sirri domin samar da mafita akan al’amarin nasu.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending