Connect with us

Manyan Labarai

Yajin aikin Burodi: Mun samu kan mu a cikin mawuyacin hali – Mai gidan Burodi

Published

on

Yayin da aka shiga rana ta biyu a yajin aikin kungiyar masu gidajen Burodi a Kano, mafi yawan masu gidajen burodin na ci gaba da kokawa bisa yadda ake ci gaba da samun tashin kayayyakin da suke sarrafawa.

A zantawar daraktan wani gidan Burodi a jihar Kano Nura Umar Manaja, mai lakabin mai Dallah-Dallah, ya ce mai-makon a samu sassauci kayan da suke amfani da su, ƙuɗaɗen kayayyakin ƙaruwa ma suka yi a fagen farashi, kamar yadda aka wayi gari da hakan a yau Laraba.

“A yau mun wayi gari da ƙaruwar Naira 15,00 akan kowanne Buhu inda yanzu ake siyar da kowanne buhun fulawar Naira 56,500, saɓanin yadda ake siyar da ita a baya, baya ga batun ƙara tsadar sauran kayan da suke amfani da su wajen sarrafa buredin na mu, “in ji Nura Manaja”.

Manaja, ya kuma ce a matsayinsa na manajan gidajen buredin daban-daban a Kano, ya wayi gari babu koda kuɗin da zai yi cefane da shi, a dan haka yanayin da mutane suka samu kansu a ciki sai mahukunta sun yi abinda ya dace wajen dai-dai ta farashi.

Ko da tashar Dala FM Kano, ta tuntuɓi mai magana da yawun ƙungiyar masu gidajen burodin ta ƙasa reshen jihar Kano, Nura Ibrahim, ya ce yau sun tashi da zagayawa gidan Burodin domin tabbatar da masu gidajen buredin sun bi doka akan yajin aikin kwanaki ukun da suka tsunduma, inda yau ake rana ta biyu.

Manyan Labarai

Gobara ta ƙone tarin kayayyaki a gidan tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Published

on

Wata Gobara ta tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau dake Mudubawa a yankin Karamar hukumar Nassarawa, inda ta ƙone wasu kayayyaki a ɗakin matar sa waɗanda zuwa yanzu ba’a ƙayyade ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faro ne daga ɗakin Girki na matar tsohon gwamnan Hajiya Halima Shekarau, tun yammacin jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun tsohon Gwamnan Malam Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta shafi iya daki ɗaya ne a cikin gidan dake Munduɓawa.

A nasa ɓangaren kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce da zarar sun kammala tattara alƙaluma da bincike, zai magantu a nan gaba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za mu duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin su dan kyautata rayuwar su – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin da ake biyan su, domin kyautata rayuwar su kasancewar abin da ake basu bai taka kara ya karya ba.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin ganawa da ma’aikatan kwashe shara a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati jihar a yau.

Gwamna Abba ya bayyana damuwarsa bisa ƙorafe-ƙorafen da ma’aikatan shara suka yi na tsaikon da ake samu wajen biyansu kudin alawus din su tsawon watanni.

“Gwamnati za ta yi bincike domin gano inda matsalar tsaikon biyan ma’aikatan kwashe shara take da nufin magance ta cikin gaggawa, “in ji Gwamnan”.

Ya kuma ƙara tabbatar wa da ma’aikatan cewa, gwamnati za ta tabbatar kowane ma’aikacin shara an tura shi aiki kusa da gidan sa domin sauƙaƙa musu kashe kudi a wajen sufuri.

Wakilinmu na fadar gidan gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Abba Kabir, ya bai wa ma’aikatan tabbacin gwamnati za ta biyasu dukkanin basukan da suke bi, tare da duba yiwuwar ƙara musu kudin alawus nan bada daɗewa ba.

Continue Reading

Trending