Connect with us

Manyan Labarai

Jami’an mu ku mayar da hankali akan kare rayuka da dukiyoyin al’umma – Kwamandan Bijilante na Kano

Published

on

Babban kwamandan ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano Ubale Barau Muhammad Badawa, ya gargaɗi jami’an su da su mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin ayyukansu tsakani da Allah S.W.T.

Ubale Barau Badawa ya bayyana hakan ne a yayin taron baiwa jami’an su bita akan yadda za su gudanar da ayyukan su cikin ƙwarewa da kuma dabarun aiki, wanda ƙungiyar tsaro ta Duniya da take da hedikwatar ta a Swezerlan, ta shirya wa jami’an Bijilanten na jihar Kano, da ya gudana a hedkwatar ta a jihar.

Ubale Barau ya kuma ƙara da cewa sun yi matuƙar farin ciki da bitar da ƙungiyar ta baiwa jami’an nasu, ya kuma ce akwai buƙatar duk wanda ya shiga ƙungiyar Bijilanten yasan ya shiga ne domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Da yake nasa jawabin babban manajan ƙungiyar tsaron a ƙasar nan Hafizu Shehu Ringim, ya ce ƙoƙarin da ƴan ƙungiyar Bijilanten suke yi a wajen samar da tsaro ga al’umma, ya sa suka shirya musu bitar domin ƙarfafa musu gwiwa akan aikin, domin cimma nasara.

A nasa ɓangaren jami’in binciken ƙwakwalwa da tattara bayanan sirri na ƙungiyar Bijilante ta ƙasa dake da hedikwatar ta a Abuja Muhktar Ɗahiru Abdullahi Ungogo, shawartar ƴan ƙungiyar Bijilanten ya yi da su guji ɗaukar doka a hannu yayin gudanar da ayyukan su.

Ya kuma shawarci ƴan ƙungiyar Bijilanten da su rinƙa gaggawa miƙa duk wanda suka kama ga jami’an tsaro domin ɗaukar mataki na gaba.

Abdulrahman Sule shine kwamandan ƙungiyar na ƙaramar hukumar Gwarzo, kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda aka baiwa bitar, ya ce hakan zai ƙara musu gwiwa akan ayyukan su, musamman ma wajen tsaurara matakan tsaro a iyakar Kano da Katsina.

Taron ƙarawa ƴan ƙungiyar Bijilanten na jihar Kano ƙarƙashin babban kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ya samu halartar ƴan ƙungiyar daban-daban daga sassan jihar Kano, da ma na wasu jahohin ƙasar nan har da birnin tarayya Abuja.

Manyan Labarai

Ba za mu amince da yadda ake yawan kai wa jami’an mu hari ba a Kano – KAROTA

Published

on

Hukumar kula da zirgar-zirgar ababen Hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce ba za ta lamunta da yadda ake yawan kai wa jami’anta farmaki ba, na ba gaira babu dalili yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Shugaban Hukumar KAROTA, a Kano, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya yi wannan gargaɗin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 09 ga watan Afrilun 2025.

“Hakan na zuwa ne biyo bayan wani mummunan hari da wasu mutane da ke cikin baburin Adai-daita sahu suka kai wa jami’an na mu yayin da suke tsaka da aikinsu a titin da ke dab da gidan Buhari kan hanyar zuwa Gidan Zoo, “in ji shi“.

Sanarwar ta ce, tunda farko an tsayar da wani mai baburin Adai-daita Sahu ne inda yaƙi tsayawa, sai kawai aka hango mai ɗan sahun ya naushi jami’in karotar.

Sai dai a ta bakin Shugaban kungiyar ‘Yan Adai-daita Sahu a jihar Kano, ya ce waɗannan mutane ba halattattun ‘Yan Adai-daita Sahu ba ne, sun dai fake da sana’ar su dan aikata ta’addanci.

Daga bisani dai jami’n hulɗa da jama’a na Hukumar Koratar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya ce hukumar za ta ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, don kare afkuwar irin hakan a gaba.

Hukumar ta ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ya shafe ta, ko kuma ƙorafe-ƙorafe, zai iya kiran waɗannan lambobin domin sanar da ita, da suka haɗar da 09015709449 ko 08059689422 ko kuma 08067311520.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Continue Reading

Manyan Labarai

An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Continue Reading

Trending