Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da tallafin kayan abinci da gidauniniyar Dangote za ta rabawa mutane

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci da gidauniniyar Dangote Foundation za ta rabawa al’ummar kasar nan, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa da suke fuskanta.

Da yake ƙaddamar da rabon tallafin a gidan gwamnati, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga kwamitin da za su gudanar da rabon kayan abincin su zamo masu gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da tallafin ya isa ga mabuƙatan da aka tanadi abincin domin su, su samu yadda ya dace.

Aƙalla dai mutane dubu dari da ashirin ne za su amfana da tallafin kayan abincin a jihar Kano (120), waɗanda suka hadar da masu kananan karfi, da kuma masu bukata ta musamman irin su masu larurar Ƙafa, da masu lalurar Ido, da sauransu.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kuma ce tuni tallafin kayan abincin ya isa ga ƙananan hukumomin Kano 44.

“Mun gamsu bisa tsarin da gidauniyar ta Dangote tayi na shigar da dakarun hukumar Hisbah cikin tsarin rabon tallafin abincin, da kuma shuwagabannin ruko na kananan hukumomi 44, Muna fatan cewa za su tsaya kan adalci da gaski yayin gudanar da rabon kayan abincin, “in ji Gwamnan”.

Da yake gabatar da tallafin, Alhaji Aliko Dangote, ya ce mutane miliyan daya ne za su amafana da tallafin buhunan shinkafa da Gero, guda Goma-goma daga dukkanin jihohin kasar nan har da babban birnin tarayya Abuja.

Ɗangote, ya kuma kara da cewar Gidauniyar ta dauki gaɓarar tallafawa al’ummar kasar nan ne da kayan abinci tun lokacin da kasar nan ta tsintar kanta a cikin halin annobar cutar nan ta Covid 19, tun a shekarar 2019, har zuwa yanzu, inda ya ce gidauniyar ba a nan ta tsaya ba tana tallafawa a bangaren Lafiya da Ilimi.

Wakilinmu na fadar Gwamnatin kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma godewa Alhaji Aliko Dangote, bisa samar da wannan tallafi, musamman a wannan yanayi na tsadar rayuwa da ake fuskanta tare da yin Kira ga mawadata da su yi koyi da irin wannan abin Alkhairi, domin samun gwaggwaɓan lada a wajen Ubangiji S.W.T. kamar yadda wakilinmu na fadar Gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito mana.

Manyan Labarai

Wasu ɓata gari sun raunata kwamandan Bijilante da wasu mutane da dama cikin wata unguwa a Kano

Published

on

Wasu bata gari rike da muggan makamai, sun raunata mutane da dama, ciki har da kwamandan Bijilante na unguwar Gaida Goruba da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano, Abdulmalik Isah.

Wasu mutane biyu da al’amarin ya rutsa dasu sun shaidawa wakilin Dala FM Kano, Abubakar Sabo cewa, matasan sun shiga cikin unguwar ta Gaida Goruba, ne a cikin daren jiya Alhamis, da misalin karfe 3, inda suka rinƙa saran mutane da muggan Makamai.

Al’amarin da ya jawo raunata mutane da dama wanda yanzu haka suna Asibiti suna karɓar magani, ciki kuwa har da kwamnadan ƙungiyar Bijilanten yankin Abdulmalik Isah.

Ita ma wata matashiya da aka Sassari mijin yayar ta, bayan da matasan suka ɓalle ƙofar gidan suka shiga, ta ce har yanzu mutumin bai san inda kansa ya ke ba.

Continue Reading

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun kama matashin da ya yi garkuwa da wata yarinya ya nemi miliyan biyu matsayin kudin fansa a Kano – Ƴan Sanda

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna Zakariyya Muhammad, Ɗan shekara 22, mazaunin unguwar Sabuwar Gandu kwarin Barka a jihar, bisa zargin sa da laifin garkuwa da wata ƙaramar yarinya mai suna Amina ƴar shekara biyu da rabi, tare da neman Naira milyan biyu a matsayin kuɗin
fansa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa gidan rediyon Dala FM, a yau Talata 09 ga watan Yulin 2024.

Ya ce bayan samun rahoton yin garkuwa da yarinyar ne kwamishinan ƴan sandan Kano CP Salman Dogo Garba, ya bada umarni ga jami’an su domin kuɓutar da yarinyar tare da kama wanda ake zargi da garkuwa da ita.

Ya ci gaba da cewa, ba tare da ɓata lokaci ba jami’an nasu suka samu nasarar cafke matashin, yana mai cewa yanzu haka matashi Zakariyya Muhammad, yana babban sashin binciken manyan laifuka da ke hedikwatar ‘yan sandan da ke Bombai, ana faɗaɗa bincike, kuma da zarar an kammala za’a gurfanar dashi a gaban kotu domin girbar abin da ya shuka.

Da yake ƙarin bayani wanda ake zargi da yin garkuwa da yarinyar mai suna Zakariyya Muhammad, ya ce bayan da ya dauki yarinyar ne ya nemi Naira
milyan biyu a matsayin kuɗin fansa, ko da dai ya nuna nadamar sa bayan
da ya shiga hannun jami’an tsaron.

Shima mahaifin yarinyar da aka yi garkuwa da itan ya magantu, inda ya ce
ya yi mamaki kan yadda wanda ya sace ƴar tasa suka ga makocin su ne.

A cewar sa, “kafin ɗauke ƴar tamu sai da matashin yazo ya rubuta min lambar wayar sa, inda bayan ɗauke ƴar tamu ne aka rinƙa kiran waya tare da sanar mana cewar zamu bayar da Naira Miliyan biyu a matsayin kuɗin fansa, bayan mun kai ƙara aka bibiya inda aka kamo matashin, ƴar mu kuma yana cikin ƙoshin lafiya, “in ji shi”.

Daga bisani dai rundunar ‘yan sandan jihar Kanon ta kuma ja hankalin iyaye da su kara lura da ya’yan su, inda ta kuma gargadi matasa da su kaucewa sanya kan su cikin halin aikata munanan ayyuka, domin gudun faɗawa komar jami’an tsaro.

Continue Reading

Trending