Connect with us

Labarai

Iyaye ku dai ma marawa ƴaƴan ku baya akan abinda suke yi da ya saɓawa doka – Mai unguwar Ja’en Jigawa

Published

on

Mai unguwar Ja’en Jigawa da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Sani Muhammad, ya ce bai kamata a rinƙa samun wasu iyaye da ɗabi’ar nan ta marawa ƴaƴan su baya akan abinda yaran suke aikatawa na saɓawa Doka, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Mai unguwar ya bayyana hakan ne yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a lokacin da yake tsokaci kan yadda ake samun wasu daga cikin iyayen yankin sa na marawa ƴaƴan su baya kan abinda suke yi na ba dai dai ba, lamarin da yake ƙara ƙara kangarar da tarbiyyar ƴaƴan tare da tayar da hankalin al’umma.

Mai unguwa Sani Muhammad, ya kuma ce matuƙar yaran ba za su zauna lafiya a cikin unguwa da al’umma ba, to kuwa za su rinƙa ɗaukar matakin miƙa yaran hannun jami’an tsaro mafi kusa, domin ɗaukar matakin da ya dace a kan su, wajen ganin sun sauke nauyin da aka ɗora musu.

Sani Muhammad, ya ƙara da cewa ko a baya bayan nan wasu matasa sai da suka yi yunƙurin yin abinda bai kamata ba, lamarin da yasa aka ɗauki mataki a kansu amma aka samu wasu daga cikin iyaye suka marawa yaran nasu baya, wanda hakan kan haifar da barazanar tsaro.

Labarai

Mun dawo da Alhazan da suka gamu da rashin lafiya yayin aikin hajjin bana – NAHCON

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON, ta dawo da wasu Alhazan ta na jihohi uku waɗanda suka gamu da rashin lafiya a kasar Saudi Arebia, yau Litinin, sakamakon samun lafiyar da suka yi.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NAHCON ta ƙasa, Musa Ubandawaki ya fitar a yau Litinin, jim kadan bayan Alhazan sun sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya Abuja, a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi.

Ta cikin sanarwar Ubandawaki, ya ce Alhazan jihohin uku da suka gamu da rashin lafiya a kasa mai tsarki, sun haɗar da Muhammad Sulaiman daga jihar Katsina, da Abubakar Sadik daga Kaduna, sai kuma Hajiya Aisha daga jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce Alhazan sun gamu da rashin lafiya ne a kasar bayan sun kammala ibadar aikin Hajjin daya gabata na 2024, wanda aka kwantar dasu a Asibiti inda suka samu kulawar likitoci, kuma izuwa yanzu sun warke wanda hakan yasa NAHCON ta dawo dasu gida Najeriya.

Wakilinmu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim ya ruwaito cewa, a aikin hajjin bana an samu yawaitar masu fama da matsalar rashin lafiya, sai dai an alaƙanta rashin lafiyar ne da yadda aka samu zafin rana a ƙasar Saudiyar.

Continue Reading

Labarai

Mun kulle Asibitoci masu zaman kan su 12 a Kano – PHIMA

Published

on

Hukumar da ke kula da Asibitoci masu zaman kan su ta jihar Kano PHIMA, ta ce zata ci gaba da daukar mataki akan dukkanin Asibitocin da suka saɓa ƙa’idar aiki, domin tsaftace harkar tare da samun damar kulawa da marasa lafiya cikin ka’ida.

Shugaban hukumar ta PHIMA, a nan Kano Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Juma’a 05 ga watan Yunin 2024.

Farfesa Salisu Ahmad, ya kuma ce daga zuwan sa hukumar zuwa yanzu aƙalla sun kulle Asibitoci guda 12, kuma akwai uku daga ciki an cire su daga tsarin asibitoci gaba ɗaya bisa sablɓa ka’idar aiki.

“Zamu ɗauki mataki akan dukkanin masu magungunan gargajiyar da suke zagayawa cikin unguwanni suna damun mutane da karar amsa kuwa, ko kuma bayyana batsa ta hanyar tallata magungunan nasu, domin tsaftace harkar, in ji Salisu”.

Wakilinmu Abdulkadir Muhammad Sani Tukuntawa ya rawaito cewa Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya kara da cewa yanzu haka hukumar ta PHIMA, tayi nisa wajen yiwa masu magungunan gargajiya
rijista tare da tantance su, domin tsarkake harkar da kuma gujewa fuskantar matsala.

Continue Reading

Labarai

Jami’an mu ku gujewa karɓar cin hanci da rashawa yayin aiki – Immigration

Published

on

Shugabar hukumar da ke kula da shige da fice ta kasa Immigration, Kemi Nanna Nandap, ta bukaci jami’ansu da su kaucewa karbar cin hanci da Rashawa a iyakokin kasa, tare da aiki tuƙuru yayin da suke gudanar da ayyukansu a iyakokin Najeriya.

Shugabar Kemi Nanna, da ta samu wakilcin HK Usman, yayin taron da hukumar kula da shige da ficen reshen jihar Kano Immigration, ta gudanar yau a hedikwatar ta, inda ta kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin jami’an hukumar da kuma al’umma.

Ta kuma ce kaddamar da al’amarin zai taimaka wajen daƙile cin hanci da
rashawa a tsakanin jami’an su da kuma al’umma musamman ma a iyakokin kasar nan da kuma ofisoshin da suke aiki.

“Nasan mu masu tsaron ƙasa ne musamman ma a iyakokin ƙasa, dole ne mu yi abinda ya kamata wajen daƙile cin hanci da rashawa a cikin aikin mu: kuma jami’an mu idan suka yi aiki tuƙuru za’a samu nasara, “in ji shi”.

Da yake nasa jawabin shugaban hukumar kula da shige da fice Immigration, ta kasa reshen jihar Kano, Ibrahim Muhammad Abubakar, ya ce sun shirya taron ne domin ƙaddamar da kawar da cin hanci da rashawa a cikin aikin nasu, kasancewar ba abu ne mai kyau ba.

Ya kuma nemi goyon bayan al’ummar ƙasar nan wajen magance harkokin cin hanci da rashawa, musamman ma tsakanin su da jami’an hukumar.

Wakilin Dala FM Kano, Hassan Mamuda Ya’u ya ruwaito cewa taron ya samu halartar jami’an hukumar da dama ciki har na birnin tarayya Abuja, da kuma jami’an tsaro, kuma ciki har da jami’an hukumar kula da gidan gyaran hali na jihar Kano, da na rundunar tsaro ta Civil Defense, da kuma hukumomin gwamnati da dai sauran su.

Continue Reading

Trending