Connect with us

Labarai

Kwamitin bincike kan tsohuwar gwamnatin Ganduje ya fara zama.

Published

on

Kwamitin da gwamnatin jahar kano ta kafa dan binciken gwamnatin Ganduje, ya bayyana irin sigar da masu korafi za su gabatar da ƙorafi a gaban kwamitin.

Gwamnatin jahar kano ta kafa kwamitin karkashin jagorancin mai Shari’a Faruk Lawan, dan bincike akan zargin da gwamnati mai ci take yiwa gwamnatin da ta shude akan yadda akayi tasarrafi da dukiyar jahar Kano.

A yayin zaman kwamitin mai Shari’a Faruk Lawan, ya bayyana cewa duk wani mai korafi zai rubuto korafinsa a takadda, domin gabatar wa a gaban kwamitin.

Gwamnatin dai ta kafa kwamatoci guda 2 dan bincike akan yadda akayi tassarifi da dukiyar jahar kano, da kuma abin da ya janyo ɓatan ƙananan yara, da rikice-rikicen siyasa wadanda akayi zargin sun faru a tsawon shekaru takwas na gwamnatin Ganduje.

Labarai

Bama jin daɗin yadda wasu iyaye suke hana ƴaƴan su maza auren mu – Budurwa mai larurar Ƙafa

Published

on

Wata matashiyar budurwa mai buƙata ta musamman dake da lalurar Ƙafa Samira Ahmad Tijjani, ta nuna rashin jin daɗin ta, bisa yadda mafi yawan iyaye suke nunawa masu lalurar ƙyama, wajen hana ƴaƴan su auren masu lalurar ƙafar lamarin da yasa al’amarin ke matuƙar ɓata musu rai.

A zantawar wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, da budurwar ta ce, mafi yawancin su mata masu lalurar ƙafar sun ma fi mata masu lafiya iya Girki, da sauran ayyukan yau da kullum.

Ta ci gaba da cewa, “Amma abin takaici sai a rinƙa nuna mana ƙyama, ko kuma wariya musamman ma wajen neman aure, bayan kuma ba mu muka yiwa kan mu halitta ba, “in ji Samira”.

Ta kuma ce abinda wasu daga cikin iyaye suke yi musu kan nuna ƴaƴan su ba za su aure mai lalurar Kafa ba, basa jin daɗin hakan, shi yasa ma ta fito domin ta sanarwa al’umma domin gujewa hakan.

A cewar ta, “Ko nima nayi soyayya mara misaltuwa da samari masu lafiyar Ƙafa, amma mahaifiyar ɗaya daga cikin su ta ce ita ba wai bata sona ba, amma tana jin kunyar ta tuna ni a cikin mutane cewar a zummar matar ɗan ta”.

Daga bisani dai ta yi kira ga al’umma da su dai na nuna ƙyamar ko kuma nuna wariya a gare su, bisa yadda iyayen su suke matuƙar shiga cikin damuwa a duk lokacin da aka nuna musu wariyar.

Continue Reading

Labarai

Bayan ƙaddamar da tallafi: Zamu rinƙa raba tallafin jarin Naira dubu 50,000 ga iyaye Mata duk wata – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnatin jihar kano ta kaddamar da rabon taffin kuɗaɗe ga iyaye mata dake kananan hukumoni 44 su 5,200 a fadin jihar nan, domin su dogara da kan su.

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya jagoranci ƙaddamar da rabon tallafin kudaɗen har Naira 50,000 ga iyaye mata dake kananan hukomini 44 a yau Talata, wanda ya gudana a ɗakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnatin kano.

Abba Kabir Yusif ya kuma ce hakan na daga cikin alkawarin da suka yiwa matam tun a lokacin yaƙin neman zaben shekarar 2023 da ta gabata, inda ya ce iyaye mata na da bukatar jari domin dogaro da kan su, musamman ma wajen yin sana’o’i irin su Kosai, Awara, Gurasa da Bandasho da dai sauran ƙananan sana’o’i.

Aƙalla dai Mata ɗari-ɗari ne 100, za su amfana daga kananan hukumomi 36 na Karkara, da kuma na cikin birni takwas 8, kuma iyaye mata dari biyu-biyu (200) za su amfana da tallafin duka dai domin su dogaro da kan su.

Wakilinmu Abba Haruna Idris ya rawaito cewa Gwamnan Kano Abba Kabir, ya ƙara da cewa wannan ba shine na karshe ba, za su rinƙa tallafawara duk wata-wata, domin samawa iyaye mata sana’oin dogaro da kai, ta yadda zasu rinƙa haɓɓaka tattalin arzikin jihar kano.

Continue Reading

Labarai

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi ya tsallake karatu na ɗaya a majalisar dokokin Kano

Published

on

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren majalisar dokokin jihar.

Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau Laraba, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan da akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Ɗiso, ya gabatar da karatun na ɗaya.

Har ila yau, yayin zaman na yau, majalisar ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta tallafa wa wasu kanikawa da kafintoci bisa iftila’in gobarar da ta ƙone musu kaya na miliyoyin Naira, tare da asarar rayuka a kan titin Lawan Dambazau.

Majalisar ta buƙaci hakan ne biyo bayan ƙudurin gaggawa da wakilin ƙaramar hukumar Birni da kewaye Alhaji Sarki Aliyu Daneji ya gabatar.

Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar ya nemi gwamnatin data tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa domin rage musu raɗaɗin iftila’in.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin da ta ɗaga darajar asibitin garin Gano, zuwa matakin babban asibiti domin ƙara inganta kiwon lafiya a yankin har ma da sauran yankuna, kamar yadda ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Shu’aibu Rabi’u ya buƙata.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a dai zaman na yau Laraba, shi ma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙaraye, Injiniya Ahmed Ibrahim, ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin Kano ta gina titi a hanyar da ta tashi daga mahaɗar titin zuwa sansanin horas da matasa ƴan hidimar ƙasa, ta bi ta Kurugu da Dederi har zuwa Yammedi duk a yankin ƙaramar hukumar Ƙaraye.

Continue Reading

Trending