Manyan Labarai
Gobara ta ƙone tarin kayayyaki a gidan tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau
Wata Gobara ta tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau dake Mudubawa a yankin Karamar hukumar Nassarawa, inda ta ƙone wasu kayayyaki a ɗakin matar sa waɗanda zuwa yanzu ba’a ƙayyade ba.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faro ne daga ɗakin Girki na matar tsohon gwamnan Hajiya Halima Shekarau, tun yammacin jiya Lahadi.
Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun tsohon Gwamnan Malam Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta shafi iya daki ɗaya ne a cikin gidan dake Munduɓawa.
A nasa ɓangaren kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce da zarar sun kammala tattara alƙaluma da bincike, zai magantu a nan gaba.
Manyan Labarai
Uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a Kano sun rasu
Rahotanni da dumi-ɗumin sa na bayyana cewar yanzu haka uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a unguwar Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano sun rasu.
Wani mazaunin garin ya shaidawa Dala FM Kano, da tsakar ranar Larabar nan cewar, daga cikin mutane ukun da suka rasu har da limamin da ya jagorancin sallar asubar wannan rana, wanda a lokacin ne matashin ya cinna musu wutar lamarin da jikin su mutanen sama da 20 ya sassaɓule.
Idan dai ba’a manta ba matashin ya cinnawa mutanen wuta ne bayan da ya watsa Fetur cikin masallacin yayin da suke tsaka da sallar Asubah, ta wannan rana, wanda tuni jami’an tsaron ƴan sanda suka cika hannun su da shi.
Matashin dai ya ce ya cinnawa mutanen wutar ne biyo bayan wata magana da suke faɗa masa wanda ransa baya daɗi, ina ya sayo Fetur a cikin wani Galan lamarin da yaje ya kunna musu wutar, duk da shima hannayen sa biyu sun ƙone.
Manyan Labarai
Mun kama matashin da ya kunnawa mutane sama da 20 Wuta a cikin wani masallaci – Ƴan Sandan Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da cinnawa wasu mutane Wuta, a lokacin da suke tsaka da Sallar Asubar yau Laraba, a cikin wani Masallaci a garin Larabawar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.
Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM Kano, a yau Laraba, ya ce bayan samun rahoton faruwar al’amarin ne Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya tura tawagar jami’an su inda suka kai ɗaukin gaggawa.
Matashin da ake zargin mai suna Shari’u Abubakar ɗan shekaru shekaru 38, ya ce shine ya siyo Fetur ya kunna wutar inda ya wurgata a cikin masallacin, lamarin da ya sa mutane da dama suka ƙone a sassan jikin su.
“Aƙalla mutane 24 ne suka ƙone bayan da matashin ya kunna musu wutar a cikin masallacin, wanda tuni jami’an mu suka kai su asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, inda suke ci gaba da samun kulawar likitoci, “in ji SP Kiyawa”.
Koyawa, ya kuma ce daga binciken farko da suka fara matashin ya tabbatar da cewa shine ya sayo Mai a gidan Mai a cikin wata roba, yazo ya kunna wutar, biyo bayan wani rikicin gado da a tsakanin sa da wasu daga cikin mutanen yankin su, inda shima hannayen sa biyu suka ƙone.
Manyan Labarai
Sama da mutane 20 ne suka ƙone a sassan jikin su bayan da ake zargin wani abu ya fashe a cikin wani masallaci da ke Kano
Rahotanni na nuni da cewa an yi zargin fashewar wani abu da asubahin wannan rana ta Laraba, a garin larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar kano, wanda kuma ya jikkata sama da mutane 20, sakamakon ƙonuwa a sassan jikinsu.
Yanzyu haka dai da yawa daga cikinsu sun fara karɓar agajin
gaggwa a babban asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, da ke Kano, kamar yadda wani ganau ya shaidawa
gidan rediyon Dala FM, lokacin da ya ziyarci asibitin a safiyar wannan
rana.
Sai dai wani da ya tsallake rijiya da baya mai suna Yusuf Abdullahi, ya ce yana cikin masallacin lokacin da lamarin ya faru suna tsaka da Sallah Asuba aka kunna wutar daga waje inda aka cillota cikin masallacin, saɓanin abin fashewar da wasu suke faɗa.
Ya kuma ce, “Allah ne kawai ya bani ikon fita Amma mutane da yawa ciki har da yan uwana guda biyu lamarin ya rutsa da su, kuma wutar ta yi musu illa babba saboda ko kasan mutum wallahi idan ka gan shi wallahi ba za ka iya gane shi ba”. Inji Yusuf Abdullahi”.
Wakilin Dala FM, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki, ya tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar tarho, sai dai ya ce yanzu haka
yana kan aikin tattara bayanai akan al’amarin, wanda rundunar
za ta fitar nan gaba kaɗan.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
You must be logged in to post a comment Login