Connect with us

Manyan Labarai

Kotu ta bada umarni ga jami’an tsaro da hukumar Hisbah kan su dakatar da kama Mansura Isah

Published

on

Babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai Shari’a Abdullahi Liman, ta takadar da hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sanda da kuma mataimakin babban Sifeton ƴan sandan kasar nan daga kama Mansura Isa.

Mai Shari’a Liman ya ayyana cewar ya yi hani ga waɗanda akayi karar ko ƴan korensu ko wakilansu, ko kuma wasu masu aiki amadadinsu daga kamawa ko tsorataswa ko gayyata har zuwa lokacin da za’a saurari kowane ɓangaren.

Wannan umarni dai ya samu ne a cikin wata ƙara mai lamba 159/2024, wadda Mansura Isah ta shigar tana karar hukumar Hisba da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano.

Kotun ta sanya ranar 15 ga wannan watan dan sauraron kowane bangare a shari’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Manyan Labarai

Zan saka hannu akan hukuncin da kotu za ta yanke wa wanda ya cinnawa masallata Wuta har 15 suka rasu – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya ce a shirye yake da ya saka hannu akan duk hukuncin da kotu zata yanke akan matashin da ake zargi da cinnawa masallata wuta a lokacin da da suke tsaka da sallar asuba cikin masallaci a kauyen Gadan dake karamar hukumar Gezawa a makon da mukayi bankwana dashi.

Injiniya Abba Kabir Yusif ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin ziyarar gani da ido da ya kai Asibitin Murtala, inda majinyatan ke samun agajin likitoci, domin kula da su.

Gwamnan ya ce gwamnatin Kano na Allah wadai da wannan lamari, inda ya ce akwai tsantsar rashin imani a cikin sa ace mutane suna tsaka da Sallah azo a cinna musu wuta babu gaira babu dalili.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla dai mutane goma sha biyar ne 15, ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan iftila’in da ya afku a ranar Larabar da ta gabata, wanda ake zargi rabon gado ne sila.

Tuni dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bakin Kakakin ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce matashin mai suna Shafi’u Abubakar yana hannun ta ana faɗaɗa bincike, kuma da zarar an kammala za’a gurfanar da shi a gaban Kotu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Dagatai da masu unguwanni ku guji ɓoye mana bayanan sirri akan ƴan Daba da masu fashin Waya – Rundunar Tsaro a Kano

Published

on

An buƙaci Dagatai da masu unguwanni da su guji ɓoye bayanan sirri akan ƴan Daba ko ɓata gari a duk lokacin da aka buƙaci sanin hakan dan ɗaukar mataki, domin gujewa abinda kaje ya dawo.

Mashawarci na musamman ga gwamnan Kano akan harkokin tsaro, kuma kwamandan rundunar tsaro masu rajin kawar da masu ƙwace wayoyi, da ɓata gari ta KOSSAP, Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan ne a zantwar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya kuma ce matuƙar dagatai da masu unguwannin za su rinƙa ɓoye musu bayanan sirrin a duk lokacin da suka ɓoƙaci sani, babu makawa hakan ka iya haifar da barazana ga rawanin su.

A cewar sa, “Mafi yawan lokuta idan muka je wajen masu unguwanni ko kuma dagatai, neman wani bayanan sirri akan wasu ɓata gari sukan ɓoye mana kuma ba zamu lamunci hakan ba zamu sanar da gwamna abinda ke faruwa, “in ji Inuwa Sharaɗa”

Inuwa Salisu, ya kuma ƙara da cewa a ƙoƙarin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, na magance matsalar tsaro a sassan jihar, ya samar da wani haɗakar jami’an tsaro wato Task Force, da za su rinƙa shiga lungu da saƙo, dan ganin tsaro ya inganta tare da kawar da masu fashi da makamin wayoyin mutane.

Inuwa, ya ci gaba da cewa, “Jami’an mu za su ci gaba da hoɓɓasa a ciki da wajen Kano wajen kawar da ɓata garin da suke addabar mutane a faɗin jahar mu; Duk wanda muka kama zai gayawa Aya zaƙin ta, “in ji shi”

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da neman ɗaukin mahukunta wajen magance matsalar tsaro a sassan jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Continue Reading

Manyan Labarai

Uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a Kano sun rasu

Published

on

Rahotanni da dumi-ɗumin sa na bayyana cewar yanzu haka uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a unguwar Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano sun rasu.

Wani mazaunin garin ya shaidawa Dala FM Kano, da tsakar ranar Larabar nan cewar, daga cikin mutane ukun da suka rasu har da limamin da ya jagorancin sallar asubar wannan rana, wanda a lokacin ne matashin ya cinna musu wutar lamarin da jikin su mutanen sama da 20 ya sassaɓule.

Idan dai ba’a manta ba matashin ya cinnawa mutanen wuta ne bayan da ya watsa Fetur cikin masallacin yayin da suke tsaka da sallar Asubah, ta wannan rana, wanda tuni jami’an tsaron ƴan sanda suka cika hannun su da shi.

Matashin dai ya ce ya cinnawa mutanen wutar ne biyo bayan wata magana da suke faɗa masa wanda ransa baya daɗi, ina ya sayo Fetur a cikin wani Galan lamarin da yaje ya kunna musu wutar, duk da shima hannayen sa biyu sun ƙone.

Continue Reading

Trending