Connect with us

Manyan Labarai

Wani matashi ya shafe sama da awa 5 sannan aka cire masa Addar da masu kilisa suka sara masa a cikin kan sa a Kano

Published

on

Wani matashi ya tsallake rijiya da baya, bayan da wasu masu Kilisa suka sareshi a kan sa da wata tsohuwar Adda, lamarin da tama ƙi fita daga cikin kan nasa a lokacin.

Al’amarin ya faru ne a yankin Mandawari daura da Tal’udu, a dai-dai lokacin da wasu masu Kilisa suka zo wucewa, shi kuma matashin suna kan babur din su mai kafa biyu da abokin
tafiyar sa, bayan da masu kilisar suka kai kora ne suka sari matashin da Addar a kansa inda ta makale aka kasa cireta har sai da ta dangana da wajen likitoci a asibiti.

Mahaifin matashin mai suna Mannir Hamza, ya ce sai da ɗan nasa ya shafe awanni sama da biyar gabanin a samu nasarar cire addar da masu kilisar suka sara masa a tsakiyar kan sa.

“Ina kira ga gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, da kwamishinan ‘yan sandan jihar, da dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, da suyi abinda ya dace wajen kara ɗaɓɓaƙa dokar nan da ta hana kilisa, duba da yadda hakan ke barazana ga tsaro da rayukan al’umma a Kano, “in ji shi”.

A zantawar mahaifiyar matashin da Dala FM Kano, ta ce al’amarin ya matuƙar tayar mata da hankali domin bata taɓa ganin tashin hankali makamancin hakan ba, amma dai an sallame su daga asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan da tuni aka yi wa ɗan nasu aiki har ma ya fara samun sauƙi.

Matar ta ƙara da cewa, ba’a samu nasarar kama waɗanda suka aikatawa ɗan nasu rashin imanin ba, su dai kawai suna Gida aka sanar da su faruwar lamarin inda suka same shi a asibitin Murtala da ke Kano, inda suka tura su na Aminu Kano, wanda a can ne aka samu nasarar ciro Addar daga kan nasa.

Dama dai daɗɗiyar doka ce kan hana kilisa a faɗin jihar Kano, sai dai kuma
a iya cewa wasu matasa yanzu haka sun bijirewa dokar lamarin da hakan kan ƙara haifar da barazanar tsaro da rayukan al’umma.

Manyan Labarai

An yi jana’izar Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Ahmadu Haruna Zago

Published

on

Ɗaruruwan mutane ne suka halarci sallar jana’izar shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna zago, wanda aka gudanar a kofar kudu a fadar mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu.

Babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shine ya jagorancin sallar jana’izar a tsakar ranar Alhamis ɗin nan.

Daga cikin manyan manyan mutane da Suka hallarci sallar jana’izar marigayin Alhaji Ahmadu Haruna zago, akwai gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da tsohon kwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso, da mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, da sauran manyan mutane ciki har da masu riki da mukaman gwamiti.

Da safiyar Alhamis ɗin nan ne dai marigayi Ahmadu Zago, mai shekaru 74 ya rasu, a Asibitin Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya, kafin rasuwar sa yana da mata huɗu da ƴaƴa 37, da jikoki da dama.

Mai martaba sarkin kano Khalifa Muhammadu Sunusi na yayi addu’ar fatan Allah ya jikan marigayin ya kuma baiwa iyalansa da al’ummar jihar Kano jure rashin.

Tuni dai gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga al’ummar jihar da kuma iyalan marigayi Ahmadu Haruna Zago, tare da fatan Allah ya gafarta masa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisar dokokin Kano ta amince da kafa rundunar tsaro mallakin jihar

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa Rundunar tsaro mallakin gwamnatin jiha, bayan ɗaukar tsawon lokaci ana dambarwa a majalisar kan saɗarar dokar da ya ce ba’a yarda wanda yake riƙe da katin shaidar kowace jam’iyyar siyasa ba ya shugabanci rundunar tsaron.

Majalisar ta amince da samar da dokar ne bayan shafe kusan fiye da tsawon awa ɗaya ana muhawara akan da yawa daga cikin tanadin da dokar samar da rundunar tsaron ya yi kafin ayi mata karatu na uku.

Da yake ƙarin bayani akan kunshin dokar, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Husani Dala, ya ce sun yi cikakken Nazari da hangen nesa kafin yin dokar wadda zata taba kowane bangare na jihar Kano wajen daukar ma’aikatan ta musamman wadanda basu da alaka da harkar siyasa.

“Dokar da muka samar ta amincewa jami’an rundunar tsaron ta jihar Kano da za a kafa su ɗauki kowane irin makami domin gudanar da ayyukan su, wanda ya haɗa da kamawa, hana aikata laifi da fatattakar masu aikata laifuka a fadin jihar Kano, “in ji Dala”.

Ditective Auwal Bala Durumin Iya guda daga cikin masana harkokin tsaro ne a ƙasar nan, ya ce akwai buƙatar abi ƙa’idoji wajen ɗaukar jami’an da za su gudanar da aikin rundunar tsaron da zarar gwamnan Kano ya sanya hannu a kan dokar.

A dai zaman na ranar Talata 04 ga watan Fabrairun 2025, majalisar dokokin Kano ta kuma amince da yin gyara akan dokar hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan, da hukumar da ke kula da sufuri a kwaryar birnin kano domin samun damar nada musu mataimaka.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za’a fara cin tarar Naira dubu 25 akan masu tofar da Yawu ko Majina, ko zubar da Shara ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar cin tarar Naira dubu 25 ga duk wanda aka kama da tofar da Yawu, da Majina, yin Bahaya ko zubar da Shara a sha tale-tale da kuma karkashin gadojin dake Kano.

Wannan ya biyo bayan dokar da majalisar ta Samar wadda za ta gudanar da ayyukan hukumar ƙawata birnin Kano da Kula da wuraren shaƙatawa.

Da yake Karin bayani ga manema labarai, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala, ya ce ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakan da za su tsaftace Kano domin shigar da jihar sahun biranen duniya a fannin tsafta da cigaba.

“Bayan tarar ta Naira dubu 25, akwai kuma sauran hukunce-hukunce da dokar ta tanada wadanda za’ayi amfani dasu wajen ladabtar da duk wanda aka samu da laifukan, “in ji Lawan Dala”.

Majalisar ta kuma yi karatu na biyu kan gyaran dokar hukumar kwashe Shara da tsaftar Muhalli ta Kano domin Samar da mataimakin Shugaba.

Continue Reading

Trending