Manyan Labarai
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya shiga fadar Masarautar Kano domin fara aiki.

Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, ya shiga fadar Masarautar Kano, a daren jiya Juma’a, domin fara aiki bayan da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bashi takardar kama aiki jiya a ɗakin taro na Afrika House da ke gidan gwamantin jihar.
Wata majiya ta shaidawa Dala FM Kano, cewa mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya shiga masarautar ne a tsakar daren Juma’a, inda ya samu rakiyar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da Kakakin majalisar dokokin jihar Hon. Jibril Isma’il Falgore, sauran ƴan tawagar gwamnan da Hakimai.
Idan dai ba’a manta ba a ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar Kano ta sanar da rushe sarakuna biyar da ke jihar, bayan da ƙudirin gaggawa kan gyaran dokar naɗa masarautun ta tsallake a zauren Majalisar, lamarin da daga bisani gwamna Abba Kabir, ya bayyana Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, a matsayin mai martaba sarkin Kano na 16.
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Kano, kuma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala Lawan Hussaini Ciɗiyar Ƴan Gurasa, ne dai ya gabatar da ƙudirin gyara dokar masarautun, wanda yanzu haka tuni ta zama Doka, bayan da gwamnan Kano ya sa mata hannu.
Yanzu haka dai mai martaba sarkin Kano ya kwana a cikin fadar masarautar jihar, wanda zai fara aikin sa kamar yadda aka saba.

Manyan Labarai
Mun shirya ɗaukar mataki a kan ƴan siyasar da ke ɗaukar nauyin Ƴan Daba a Kano – Anti-Phone Snaching

Rundunar Tsaro da ke yaki da fadan Daba da fashi da makamin Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye ta Anti-Phone Snaching, a jihar Kano, ta ce ta gano cewar yadda wasu daga cikin ‘Yan Siyasa ke daukar nauyin ‘Yan Daba na daga cikin daga cikin dalilan da ke kara ta’azzarar ayyukan ‘yan daban a sassan jihar.
Kwamandan rundunar a Kano Inuwa Salisu Sharada ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Litinin, ya ce yanzu haka sun fara bibiya tare da bincike akan irin matasan da suke damun jama’a da fadan Daba a sassan jihar Kano, don gano ‘Yan siyasar da ke da hannu akan lamarin tare da daukar mataki na gaba.
“Abin takaici ne yadda mafi yawancin masu fadan daban ake samun su kananan yara da ba su wuce shekaru 15 zuwa kasa ba, kuma duk da hakan duk wanda mu ka kama ba za mu saurara masa ba, a don haka ne ma mu ke kira ga iyaye da su tsawatar wa ya’yansu, in ji Inuwa”.
A cewar sa, idan suka kama masu harkar faɗan Daba, mafi yawancin su suna kama faɗin wasu daga cikin ƴan siyasa da suke ɗaukar nauyin su, kuma yanzu haka sun dukufa don gano bakin zaren tare da ɗaukar matakin da ya dace akan dukkan masu hannu kan lamarin.
Tuni dai kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kano Ibrahim Adamu Bakori, ya kaddamar da sabbin dabarun magance harkokin Daba da fashin Waya da kuma shaye-shayen kayan maye a sassan jihar, bayan da ya gana da manyan jami’an ‘yan sandan a ranar Asabar din da ta gabata.

Manyan Labarai
Kwamishinan Ƴan sandan Kano ya ƙaddamar da sabbin matakan daƙile Daba da Fashin Waya a jihar

Rundunar Ƴan sandan jihar Kano ta sha alwashin kakkaɓe matsalar faɗab Daba, da fashin waya da makami, da Shaye-shayen kayan maye, da ke addabar jama’a a birnin jihar, don wanzar da zaman lafiya.
Kakakin rundunar ƴan Sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikewa manema labarai tashar Dala FM ta samu a ranar Lahadi 15 ga watan Yunin 2025.
Kiyawa, ya ce hakan na zuwa ne bayan da kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ƙaddamar da sabbin matakan daƙile ayyukan ’yan daba da masu fashin waya da makami a birnin Kano da kewaye.
Sanarwar ta bayyana cewa kwamishinan ya gana da manyan jami’an rundunar ne a ranar Asabar 14 ga watan Yunin 2025, inda ya umarce su da su soma sumame a dukkan maɓoyar Ƴan Daba, tare da haɗin gwiwa da shugabannin al’umma domin ganin an cafko duk masu hannu a tashe-tashen hankula a faɗin jihar.
“A umarnin da kwamishinan ya bayar, ya umarci dukkanin Baturen Ƴan Sanda wato DPO’s, da shugabannin shiyya na Ƴan Sanda, da sauran dakarun Ƴan sanda, da su nemi haɗin kai da al’umma, tare da ƙara faɗaɗa sintiri don magance matsalolin Daba, da fashin Waya a Kano, in ji Kiyawa”
Har ila yau, rundunar ƴan sandan ta kuma buƙaci haɗin kan jama’a da su rika bayar da bayanan sirri a kan yan daban, ta hanyar kiran waɗannan lambobin wayar 08032419752, ko 08123821575, 09029292926.

Manyan Labarai
Hukumar Shari’a ta shirya kawo ƙarshen ƙwacen Waya a Kano

Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ta ce za ta tunkari matsalar ƙwacen Waya haɗin gwiwa da dukkan shugabannin kasuwannin wayoyi da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da hukunci a jihar Kano, don kawo ƙarshen matsalar.
Kwamishina na biyu a hukumar Shari’a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ne ya bayyana hakan a shafin sa na sada zumunta a ranar Asabar, biyo bayan yadda ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen ƙwacen waya a birnin Kano, lamarin da ke sanadiyyar rayukan jama’a daga masu ƙwacen wayar, tare da asarar dukiyoyi.
Sheikh Ali Ɗan Abba, ya kuma ce, a makon da za a shiga ne Hukumar shari’a ta jihar Kano, za ta bayyana irin tsauraran matakan da za ta ɗauka a kan wannan masifar da ta gallabi al’ummar jihar, wato matsalar fashin Waya da Makami.
Tashar Dala FM Kano, ta ruwaito cewa, Sheikh Ɗan Abba, ya kuma yi addu’a akan lamarin, inda ya ce “Allah ya taimake mu ya kawo mana ƙarshen wannan masifar ta fashin Waya da makami a Kano”.
Wannan dai na zuwa ne yayin da al’ummar Kano, da masana harkokin tsaro, ke ci gaba da kiraye-kiraye ga mahukunta da su ƙara tashi tsaye wajen yin abinda ya dace don kawo ƙarshen ƙwacen waya, da faɗan Daba, da kuma shaye-shayen kayan maye, a jihar, la’akari da yadda lamarin ya ke damun jama’a.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su