Connect with us

Labarai

Saƙon gwamnan Kano ga maniyyatan jihar sa kan aikin hajji bana 

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta shawarci maniyyatan da za su gudanar da ibadar aikin Hajjin bana, da su alkinta kuɗaɗen guzirin su, sakamakon yadda komai ya yi tsada a yanzu, wanda hakan ya sa gwamnatin jihar ta rika bai wa maniyyatan tallafi kashi – kashi a bana.

Babban daraktan hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Kano Alhaji Lamin Rabi’u Ɗan Baffa, ne ya bayyana hakan, a daren jiya Talata, a lokacin da jirgi na biyu ya ɗauki maniyyatan Kano zuwa birnin Madina, a wani ɓangare na shirye-shiryen fara gudanar da ibadar aikin hajjin bana.

Lamin Rabi’u, ya ce duba da irin halin da ake ciki ne ya sa gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki gaɓarar bai wa maniyyatan tallafi su kimanin dubu uku da dari daya da ashirin da tara.

“A yanzu hukumomin kula da aikin Hajji da Umrah na kasar Saudi Arebia sun kawo sabbin tsare – tsare ga masu zuwa ziyara wanda ya kamata ace sun yiwa sabon tsarin nasu biyayya domin kaucewa samun matsala, “in ji Lamin”.

Wakilin mu daga birnin Madinatul Munawwara Abdulkarim Muhammad Abdulkarim ya ruwaito cewa, da Asubahin yau Laraba ne jirgi na biyu ɗauke da maniyyatan jihar Kano sama da dari biyar Maza da Mata ya sauke su a birnin Madina, domin gudanar da ibada, a ci gaba da shirin gudanar da ibadar aikin hajjin wannan shekara.

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Trending