Connect with us

Manyan Labarai

Kotu ta sanya ranar da za ta bayyana matsayar ta kan shari’ar Masarautun Kano

Published

on

Babbar kotun tarayya mai zamanta a Gyaɗi-gyaɗi a nan Kano, ta sanya ranar 13 ga wannan watan dan bayyana ra’ayinta a kan tattaunawar da lauyoyi suka yi a gabanta, a ƙunshin karar da Aminu Babba Dan Agundi ya shigar yana ƙalubalantar rushe masarautun Kano 4 da majalisar dokokin jihar tayi a baya.

A zaman kotun na lauyan gwamnatin Kano Barista Mahmud Magaji SAN, ya yi suka akan hurumin kotun inda ya kawo wasu misalai na wasu shari’o’in da kotun koli ta yi.

Shima lauyan majilisar dokoki ta jahar Kano Barista Ibrahim Wangida, ya yi suka akan hanyar da mai karar ya bi ya shigar da karar bata da tushe.

Barrister Wangida ya bayyana cewar shi mai kara Aminu Babba ba Ɗan majalisar dokoki ba ne, kuma lokacin da ya shigar da karar an riga an rushe dokar da ta naɗa shi a matsayin sarkin dawaki babba dan haka bashi da hurumin zuwa kotu ta ƙalubalantar abin da majalisar tayi.

Majalisar dokokin jahar Kano dai ta rushe dokar masarautu ta shekarar 2019 wadda ta raba masarautar Kano gida biyar, kuma bayan rushe waccan dokar ne gwamnan Kano ya sanya hannu akan sabuwar dokar, tare da bayyana Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, a matsayin sarkin Kano na 16.

Mai kara ya bayyanawa kotun cewar hanyar da majalisar ta bi dan yin sabuwar dokar akwai gyare a cikinta.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, kotun ta kuma sanya ranar 13 ga wannan watan domin bayyana matsayar ta.

Manyan Labarai

Jam’iyyar NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin Kano da wani Kwamishina

Published

on

Jam’iyyar NNPP ta jihar Kano ta bayyana dakatar da sakataren gwamnatin jihar Dakta Abdullahi Baffa Bichi, da Kwamishinan Sufuri na jihar Kano Muhammad Diggwal, daga cikin jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar NNPP a Kano Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren yau Litinin.

Hashim Dungurawa, ya ce dakatar da ƙusoshin gwamnatin jihar Kano su biyu ya biyo bayan zargin keta alfarmar jagoranci, da ta Jam’iyya, da kuma keta alfarmar gwamnati, a don haka ne suka ɗauki matakin ba tare da yin wasa ba akai.

“Jagorancin shugabancin jam’iyyar mu na ƙananan hukumomin da mutane biyun suka fito sun gabatar mana da ƙorafe-ƙorafe kan ƙusoshin gwamnatin biyu, akan zarge-zarge da ake musu ya sa muka ɗauki matakin dakatar da su, har sai mun gama bincike, “in ji Dungurawa”.

Sulaiman ya ƙara da cewar dakatar da Abdullahi Baffa Bichi da Muhammad Diggwal ta fara aiki ne daga ranar Litinin 14 ga watan Oktoban 2024, kamar yadda jam’iyyar ta samu ingantattun shawarwari akan zargin da ake musu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ku tallafawa mazauna Asibitin masu lalurar Ƙwaƙwalwa na Ɗorayi bisa halin da suke ciki – Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam 

Published

on

Ƙungiyar wayar da kan jama’a da kare haƙƙin ɗan adam da tallafawa mabuƙata, ta Awareness for Human Right and Charity Foundation, ta tallafawa mazauna Asibitin masu lalurar Ƙwaƙwalwa da ke unguwar Ɗorayi, da dafaffen abinci, domin rage musu wata damuwa.

Ƙungiyar dai ta rabawa masu lalurar Ƙwaƙwalwar abincin ne da yammacin Asabar 12 ga watan Oktoban 2024, tare da ziyartar wata makarantar tsangaya da ke unguwar Ɗorayi, inda ɗalibai 1,000 suka rabauta da tallafin dafaffen abincin.

Da yake yiwa Dala FM Kano, ƙarin bayani daraktan ƙungiyar ta Awareness for Human Right and Charity Foundation, Kwamared Auwal Usman, ya ce rahotannin da suka samu kan yadda mazauna Asibitin da kuma makarantun tsangayar ke fuskantar ƙalubalen abinci ya sa suka kai musu tallafin domin rage musu wani raɗaɗi.

 

Wasu daga cikin masu lalurar Ƙwaƙwalwar da suka fara samun sauƙi, sun nemi ɗaukin gwamnatin jihar Kano wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta na rashin kyawun wuraren da suke kwana da sauran matsaloli, ko sa samu wani sauƙi.

Da yake nasa jawabin mai kula da Asibitin da ake kula da masu lalurar Ƙwaƙwalwar na Ɗorayi a Kano, Munnir Ɗahiru Kurawa, ya miƙa godiyar sa ga tawagar ƙungiyar bisa kaɓakin alkhairin da ta saukewa masu taɓin hankalin.

Wannan dai na zuwa ne makwanni kaɗan da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Asibitin masu lalurar Ƙwaƙwalwar na Ɗorayi, har ma ya bada umarnin aje a gyara shi, sai dai kawo yanzu hakan bata samu ba kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun biya wa mazauna gidan gyaran hali tara don rage musu raɗaɗi a Kano – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta biya wa wasu mazauna gidan ajiya da gyaran hali na Goron da na yara da ke Kano, su 10 tara, waɗanda suka shaƙi iskar ƴanci.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar na ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ne ya bayyana wa manema labarai hakan jim kaɗan da fitowar su daga gidan gyaran halin lokacin da mutanen suka shaƙi iskar ƴanci a ranar Alhamis.

Tasi’u Idris ya ce sun ɗauki matakin biya wa mutanen tarar ne ciki har da Matasa domin su shaƙi iskar ƴanci kamar kowa, duba da halin matsin rayuwar da ake ciki yanzu a ƙasar nan.

Kasancewar guda daga cikin mambobin ƙungiyar ne na ƙaramar hukumar Kura mai suna Usman Yusuf Gun-Dutse, haɗin gwiwa da uwar ƙungiyar ta ƙasa ne suka biya tarar, a don haka ne muka zanta da shi, inda ya ce ya yi hakan ne domin taimaka wa mutanen.

Da yake nasa jawabin akan batun mai magana da yawun gidajen gyaran halin na jihar Kano SC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa, ya ce abinda ƙungiyar ta yi abin jin daɗi ne bisa yadda aka rage cunkoson mutane a gidajen.

Majiyar tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewar, tuni dai mutanen suka koma cikin ƴan uwan su domin ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Continue Reading

Trending