Manyan Labarai
Ba za mu dawo da ruwan sha ba a Kano, sai an sanya mu a sabon tsarin albashi – Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha
Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano, sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani, bisa wasu dalilai da suka bayyana da ke damun su.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago reshen hukumar samar da ruwan sha a jihar Kano Kwamared Najib Abdulsalam, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawar sa da Dala FM a cikin daren yau Talata.
Kwamared Najib ya kuma ce ma’aikatan sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta gani ɗin ne sakamakon yadda aka gaza biyan ma’aikatan ruwan sabon tsarin albashi na mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 71,000.
A watan Nuwamban shekarar nan ta 2024, ne dai gwamnatin jihar Kano ta fara biyan ma’aikatan jihar mafi ƙarancin albashin, ko da dai wasu ma’aikatan na ci gaba da kokawa kan rashin samun sabon tsarin albashin.
“Dukkanin ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha a jihar Kano babu wanda ya samu sabon tsarin albashi duk kuwa da yarjejeniyar da muka yi a baya, hakan ne ya sa muka tafi yajin aikin har sai an magance matsalar, “in ji Najib”.
Ya kuma ce sun kashe ruwan sha a jihar Kano, kuma ba za su dawo da shi ba har sai an biya ma’aikatan sabon tsarin albashin, da manajan daraktan Hukumar ya karya Yarjejeniyar da suka yi da shi.
Najib ya ƙara da cewar aikin ma’aikatan aiki ne mai matuƙar ban tausayi bisa yadda suke aiki a cikin ruwa cikin dare da rana, a don haka suke kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kawo musu ɗauki wajen magance matsalar da suka fuskanta ta rashin biyan nasu sabon tsarin albashin.
Manyan Labarai
Kaji da Abinci da Nama sun fi ƙarfin mu a bikin Kirsimetin bana – Mabiya addinin Kirista a Kano
Yayin da mabiya addinin kirista ke gudanar da bikin Kirsimeti yau a faɗin Duniya, wasu mabiya addinin a nan Kano, sun ce bikin kirsimetin a bana ya zo musu lami bisa yadda ya riske su a cikin halin matsin rayuwa biyo bayan rashin kuɗi a hannun su.
Aƙalla sama da kiristoci biliyan biyu ne suka yi bikin kirismetin bana a fadin Duniya, domin tunawa da haihuwar Annabi Isah A.S. wanda mabiya addinin kiritanci ke yiwa lakabi da Yesu Kiristi, kama daga Najeriya, zuwa sauran kasashen Afrika, da Turai, da Amurka da kuma Asiya.
Kiristoci dai na bikin kirismeti da Nishadi, fiye da shekaru dubu biyu da haihuwar Yesu, wanda ya rikiɗe zuwa taron shekara-shekara, lokaci ne na soyayya, da Bege, da farin ciki, da kuma sadaka har ma da addu’o’l a tsakanin su.
Sai dai a zantawar wakilinmu da wani mabiyin addinin kirista mai suna Augusting Edeiken, mazaunin unguwar Ja’en Makera da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano, ya ce bikin kirismetin bana sai sam bar ka, bisa yadda bikin ya same su a cikin karancin kudi a hannu baya ga halin matsin rayuwa da ake ciki kasancewar yanzu ta ciki akeyi.
Shima wani mabiyin addinin kiristan da muka zanta da shi mai suna Stephen Samuel, ya ce a kirismetin na bana sai dai kawai hakuri, domin kuwa ko irin Kajin nan da suke yankawa a kowacce shekara a taru ‘yan uwa da abokan arzuka aci, a bana lamarin ya gagari mafi yawancin su, bisa halin da suka samu kansu a ciki.
“Mun taya Kaji a kasuwa kowacce ɗaya babba mai kyau ana sayar da ita akan kuɗi Naira dubu 25,000, zuwa dubu 30,000, da dai sauran farashi, hakan ya sa muka kasa saya a bana mu ke yin bikin lami babu Nana sai dai iya Abinci, “in ji Stephen”.
Pastor Emmanual Gunu wani malamin wata Coci ne a yankin Sabon Gari da ke nan Kano, ya ce matsin rayuwar da aka samu kai yanzu a ciki ya sanya suka umarci mabiya addinin kiristan a nan Kano, da su tashi da Azumi da kuma kara himma wajen gabatar da addu’a’i domin samun sauƙin rayuwa.
A zagayen da wakilin Dala FM Kano, Hassan Mamuda Y’a’u, ya gudanar a wasu daga cikin unguwannin da mabiya addinin kiristan ke zaune a Kano, ya iske mafiya yawan kiristocin ba su yi yankan dabbobi ba, kamar yadda suka saba a baya, lamarin da bikin kirsimetin ya kara tabbatar da cewar an gudanar da shi cikin lami a wannan shekarar ta 2024.
Manyan Labarai
Mun kama kayan maye na biliyan 1.5, da kuma waɗanda ake zargi da dillancinsu a Kano – Kwamitin Tsaro
Kwamitin tsaro da gwamnatin jihar Kano ta kafa mai yaki da harkokikin Shaye-shaye da faɗan Daba da kuma daƙile kwacen Waya, ya ce daga watan Agustan da ya gabata zuwa wannan wata da ake ciki na Disamban 2024, sun kama kayayyakin maye aƙalla na Naira biliyan ɗaya da rabi.
Shugaban kwamitin tsaron Janar Gambo Ahmad mai Addu’a mai ritaya, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM , ya kuma ce hakan na zuwa ne a ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano na kakkaɓe ayyukan ɓata gari da ke addabar mutane a sassan jihar.
“Daga cikin kayayyakin mayen da muka kama a tsakanin wata biyar ɗin akwai Ƙwayoyi, da tabar Wi-wi, tare da kama waɗanda ake zargi suna dillansin su a wasu daga cikin unguwanni ƙwaryar birnin jihar Kano, “in ji Gambo Ahmad,”.
Har ila yau, Janar Gambo mai Adu’a mai ritaya, ya ƙara da cewar ko a cikin daren Alhamis 19 ga watan Disamban 2024, sai da jami’ansu suka kama mutane shida da ake zargin su da sha da dillancin ƙwayoyi da sayar da tabar Wiwi, a unguwannin Rimin Ƙira, da Shahuci, da kuma Rijiyar Zaki, a Kano.
Ya ci gaba da cewa da zarar sun kammala bincike akan matasan da suka kama, za su gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abinda suka shuka, ko da dai matasan sun bayyana nadamar su inda suka ce ba za’a ƙara samun su a cikin lamarin ba.
Manyan Labarai
Ku gujewa bai wa baƙuwar fuska aron wayoyin ku don gudun fuskantar matsala – Kwamitin Tsaro a Kano
Kwamitin tsaro na unguwar Dabino da ke yankin Tukuntawa a ƙaramar hukumar Birni a Kano, ya bukaci al’umma da su ƙauracewa rinka bayar da aron wayar su ga waɗanda basu sani ba, idan suka bukaci hakan, domin gujewa bai wa waɗanda ka iya sanya su a cikin matsala.
Shugaban kwamitin tsaron Auwalu Garba Soja, shi ne ya bayyana hakan ga gidan rediyon Dala FM, a ranar Alhamis.
Ya ce hakan na zuwa ne biyo bayan yadda suka karɓi ƙorafe-korafe daga wajen mutanen da suka gamu da masu aron wayar har wanda bayan sun ara suka gudar musu da ita a maban-banta lokuta.
“Ya kamata mutane ku ƙara kiyayewa da irin mutanen da suke neman aron wayar ku da zummar za suyi kira ko kuma wani uziri, kasancewar wasu idan suka karɓa suna guduwa da wayar daga ƙarshe su saka ku a cikin matsala, “in ji shi”.
Soja, ya kuma ƙara da cewar sun karɓi ƙorafe-ƙorafen jama’a akan irin wannan matsalar da ba za ta lissafu ba, a don haka dole sai mutane sun kiyaye da wayoyin su, tare da kiyaye irin mutanen da za su rinƙa mu’amula dasu.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su