Connect with us

Manyan Labarai

Fadan dabar kofar Na’isa da kofar Dan-agundi, laifin iyaye – Mazaunin Yankin

Published

on

Wani mazaunin ƙofar Na’isa wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce faɗan dabar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin da Ɗan Agundi, laifin iyaye ne, da kuma wasu manya a unguwannin da ake zargin suna goya musu baya ta hanyar daƙile yunƙurin hukumomi na ɗaukar doka a kansu.

Mutumin ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, biyo bayan yadda rikicin faɗan dabar ya sake ɓarkewa a unguwannin a Alhamis ɗin nan, al’amarin da ya janyo asarar dukiyoyin al’umma a yankunan.

Ya ce lamarin ya faro ne tun a lokacin bikin ƙaramar Sallah, lamarin da a baya ƙura ta lafa, sai dai kuma a ranar Alhamis ɗin sai gashi an sake samun faɗan dabar.

A cewar sa, “A lokacin faɗan dabar ya faru an Sassari mutane da dama, hatta Saniya ma ba ta tsira ba sai da aka sareta, tare da fasa gilasan ababen hawan Mutane, “in ji shi”.

Sa dai mutumin ya ce, tuni jami’an tsaron Ƴan Sanda, suka kai ɗauki tare da kwantar da tarzoma, lamarin da ƙurar ta lafa.

Manyan Labarai

Zargin Baɗala: Hisbah ta kama masu zance cikin Mota a Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta kai sumame wani gidan biki, inda ta samu nasarar kama wasu masu zance a cikin Mota, suna aikata abinda bai kamata ba.

Mataimakin babban kwamandan hukumar a jihar Kano, Dakta Mujahideen Aminudden Abubakar, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilin Dala FM Kano, Adam Abubakar Indallahi, a ranar Lahadi.

“Mun samu nasarar ne ƙarƙashin jagorancin jami’ansu na ofirashin gyara kayan ka, yayin zagayen da suka gudanar a unguwar Kurna da filin Durumi da gwammaja, inda suka tashi masu bikin tare da kama wasu Samari da Ƴan mata da zargin suna aikata abinda bai dace ba a cikin Mota, “in ji shi”.

Ya kuma ƙara da cewa, sun jami’an nasu sun kuma kama wasu da ake zargin suna aikata Baɗala akan babur mai kafa biyu samfurin roba-roba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Siyasantar da Tsaro ne ke ƙara ta’azzara faɗan Daba a Kano – Masanin Tsaro

Published

on

Yayin da faɗan Daba ke ƙara zama alaƙaƙai tsakanin al’umma a sassan birnin Kano, masanin tsaron nan Ditective Auwal Bala Durumin Iya, ya ce matuƙar ana son a daƙile lamarin, sai gwamnati ta cire Siyasantar da tsaron, tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kan da ya dace.

Ditective Auwal Bala ya bayyana hakan ne a zantawar sa da tashar Dala FM, a lokacin da yake tsokaci kan hanyoyin da za a bi domin daƙile rikice-rikicen faɗan dabar da ƙwacen Waya da kuma daƙile Shaye-shayen kayan maye a jihar.

“Baya ga batun bai wa jami’an tsaro haɗin kan, da kuma wadata su da kayan aiki, akwai kuma buƙatar suma al’umma su rinƙa bai wa jami’an tsaron bayanan sirri, don kawo karshen faɗan dabar a faɗin jihar Kano, “in ji shi”.

Ditective Durumin Iya, ya ƙara da cewar, suma Ƴan Siyasa ya kamata su kaucewa siyasantar da harkokin Tsaro, da gujewa ɗaukar nauyin Ƴan Dabar, ko kuma fito dasu idan aka kamasu, saboda hakan yana taka rawa wajen ƙara ta’azzara Ayyukan Daba.

 

Jihar Kano dai, ta yi ƙaurin suna wajen fuskantar rikice-rikicen faɗan Daba, da ƙwacen Waya, da kuma sha da dillancin kayan maye, ko da dai tuni hukumomi suka tashi haiƙan domin magance matsalolin.

Continue Reading

Manyan Labarai

Jarabawar JAMB: An dakatar da duban tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025 – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin duban tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025, domin bai wa ɗaliban da za su rubuta jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB, damar isa cibiyoyin zana jarrabawar a kan lokaci.

Kwamishinan muhalli da kula da sauyin yanayi na jihar Kano Dakta Dahir Hashim Muhammad ne ya sanar da hakan, a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Sama’ila Garba Gwammaja ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, an dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin bai wa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ta JAMB, ba tare da wata matsala ba.

“Muna mai tabbatar wa mazauna Kano cewa, dakatarwar duban tsaftar muhallin na wucin gadi ne a iya wannan watan kawai, kuma za a ci gaba da aikin tsaftar muhallin a watan Mayun 2025, “in ji Dr. Ɗahir”

Kwamishinan ya kuma yi kira ga mazauna jihar Kano, da su ba hukuma hadin kai da fahimtar dalilin da ya sa aka yanke wannan hukunci, musamman na ganin cewa ayyukan tsaftar muhalli ba su ci karo da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a jihar ba.

Continue Reading

Trending