Connect with us

Manyan Labarai

Dalilin da ya sa muke rike gora-KAROTA

Published

on

Dakarun tsaftace tuki a titunan jihar Kano wato KAROTA sunyi martani kan zargin da ake musu cewar suna daukar manyan gorori idan suna bakin aiki

Cikin wata tattaunar kai tsaye ta shirin Barka da Hantsi da shugaban KAROTA Honarabul Baffa Babba Dan Agundi, anyi masa tambayar dalilin daya sanya jami’ansa ke rike gorori a bakin aiki.

Dan-agundi yace hakan na taimaka musu cimma muradai da suka sanya gaba.

Wata hujja da ya sake gindayawa itace hari da aka kaiwa jami’an a bakin aiki ya karu, inda da dama suka kwanta jinyar ko dai karaya a sassan jiki, ko kuma raunuka daban daban

Shugaban hukumar yace a saboda haka ya zamewa KAROTA dole ta rungumi tsaftace aikinta da kuma kare kai daga yiwuwar hari daga wadanda ayyukan hukumar baya yi musu dadi

Koda yake shugaban ya tabbatar da cewa sabawa doka ne jami’an hukumar su rike gora, sai dai kima dokar kasa ta baiwa kowane jami’i damr kare kai daga fadawa halaka

MUNA DA KYAKKYAWAR FAHIMTA DA SAURAN JAMI’AN TSARO.

Anyi wa Baffa Babba tambaya kan wani faifai na bidiyo dake zagayawa a kafafen sadarwar zamani, inda aka ga jami’an hukumar dana soji suna gwada kwanji.

Yace faifai na farko dake nuna sojoji na baiwa yan KAROTA gwale-gwale tsohon hoto ne da ya faru lokacin haihuwar hukumar a kano.

Bidiyo na biyu kuwa jami’an hukumar ne suka kama wani sojan gona, inda tuni suka danka shi ga rundunar soji. Ya kara da cewa wannan aiki ya jawo musu farin jini daga dukkanin jami’an tsaro, inda aikin hukumar su fadada zuwa kama jami’ai na bogi a fadin jihar kano.

A baya bayan nan dai jami’an hukumar sun matsa kaimi wajen takurawa direbobi dake tuki ba bisa ka’ida ba, ko kuma lodin kaya daya wuce kima.

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Trending