Connect with us

Manyan Labarai

KAROTA ta biya tarar dubban nairori

Published

on

Wani direban babbar motar daukar kaya ya garzaya hukumar KAROTA domin neman hakkin fasa masa gilashin mota da wani jami’in hukumar yayi

A yammacin larabar data gabata ne rashin jituwa ya afku a tsakaniu, inda wuf dan KAROTA yayi amfani da wata mukekiyar kokara ya narkawa gilashin motar, wanda kimar kudinsa a kasuwar tsaye ta kai naira dubu 50.

Bayan da kura ta lafa ne direban motar yayi tattaki zuwa ofishin hukumar domin bin ba’asi abinda ya kira cin zarafi da akayi masa, “neman hakki nay a zama dole kamar kowane dan Najeriya nima dan kasa” a cewar direban.

Al’amarin ya jefa shakku cikin zukatan mahukunta ma’aikatar ta KAROTA tunda sa’o’I kadan da kammala wani shirin rediyo da shugaban ta Baffa Babba Dan Agundi yayi, inda yace bashi da masaniyar dokar da ta baiwa jamian hukumar damar rike kokara,a saboda haka ne yayi kira cewar su kauracewa amfani da ita a bakin aiki domin gudun aika aika, sai gashi ta faru.

Anata bangaren hukumar ta shaidawa wakilin mu Abba Isa cewa ta rigaya ta biya direban babbar motar kudin sa har naira dubu 50, tare da bashi hakurin cin zarafin da akayi masa.

Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa shine mai Magana da yawun hukumar KAROTA, ya kara da cewa zasu binciki jami’in domin ladaftar dashi, koda kuwa ta kama a sallame shi daga aiki ne da Karin hukunci mai tsanani.

Manyan Labarai

Wani Matashi ya rasu bayan da aka zargi ya rataye kan sa a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce waní matashi rnai suna Umaro Garba ɗan unguwar Jar-Kuka mai shekaru 32 a Duniya, an yi zargin ya rataye kan sa da wani tsumma a sama al’amarin da ya yi sanadiyyar rasuwar sa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar wa Dala FM faruwar al’amarin a ranar Talata 10 ga watan Satumban 2024.a

Ya ce sun samu rahoto ne daga wani mutum daga unguwar Jar-Kuka, da ya ce sun ga ƙanen sa rataye a sama da Tsumma a ranar 8 ga watan Satumban 2024, lamarin da Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, ya bai baturen ƴan sandan na Mariri umarni domin kai ɗaukin gaggawa, inda suka garzaya unguwar da al’amarin ya faru tare da sakko da shi daga saman da ake zargin ya rataye kan nasa.

A cewar sa, “Bayan da jami’an namu suka sakko da matashin suka kai shi babban Asibitin Sir. Muharnnadu Sunusi lamarin da Likata ya tabbatar da rasuwar sa, “in ji Kiyawa”.

Abdullahi Haruna ya ƙara da cewa tuni suka miƙa gawar marigayin ga ƴan uwansa kuma suka yi jana’izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Majiyar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, SP Kiyawa ya kuma ce yanzu haka sun dukufa wajen faɗaɗa bincike akan dalilan da suka sanya matashin ya rataye kan nasa har ya rasu.

Kiyawa ya kuma shawarci al’umma, da idan suka lura da wani baƙon al’amari akan ɗan uwan su musamman ma na keɓancewa a wuri guda, ko alamun suna cikin damuwa, da su rinƙa jan su a jiki domin gujewa ta’addar kashe kai daga wasu suke yi, saboda wani dalili nasu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun bai wa DSS, wa’adin awa ɗaya su saki shugaban mu ko aga matakin da zamu ɗauka – NLC

Published

on

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC, ta bai wa hukumar tsaron farin kaya ta DSS wa’adin awa guda da su saki shugaban su na ƙasa Joe Ajearo, ko kuma aga matakin da zai biyo baya daga gareta.

Sakataren tsare-tsaren ƙungiyar ta NLC, a matakin ƙasa Kwamared Nasir Kabir, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM a yammacin Litinin ɗin nan.

Ya kuma ce a lokacin da jami’an DSS, suka kama shugaban nasu a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, a dai-dai lokacin da zai tafi ƙasar Ingila, babu wata takardar umarnin kamu da suke tare da ita, kuma ƙungiyar ba za ta zuba ido ana zaluntar ƴan ƙasa su zuba idanu su ƙyale ba.

Kwamared Nasir Kabir ya kuma ƙara da cewa yanzu haka sun shiga wata tattaunawar gaggawa, domin samar da matsaya kan kamun da aka yiwa shugaban nasu.

Ƙungiyar ta kuma umartarci mambobin su da su kasance a cikin shirin ko ta kwana kan mataki da za su ɗauka matuƙar ba’a saki shugaban nasu ba, inda ya bukaci kada ƴan Najeriya suji haushin su kan matakin da za aga sun ɗauka bisa zalunci da aka yiwa ƴan ƙasa.

“Yanzu haka mun sanarwa dukkanin mambobin mu na jahohi 36 da Abuja, da su kasace cikin shirin ko ta kwana, da kuma duk manyan ƙungiyogin mu da suka shafi wutar lantarki, da na man Fetur, da makarantu da sauransu, “in ji shi”

Da safiyar Litinin ɗin nan ne dai jami’an tsaron farin kaya na DSS suka kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC, Joe Ajearo, a lokacin da yake shirin barin ƙasar domin tafiya ƙasar Ingila, don halartar taron da aka gayyaceshi na inganta rayuwar ma’aikata da sauran abubuwan more rayuwar su.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta ɗage komawar ɗalibai makarantu Firamare da na Sakandire

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ɗage komawa makarantun Firamare da na Sakandire daga ranar Lahadi da Litinin, har zuwa wani lokaci da za a saka a nan gaba.

Kwamishinan Ilmi na jihar Kano Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren yau Asabar 07 ga watan Satumban 2024.

Doguwa ya kuma ce gwamnatin ta yi niyyar buɗe makarantun kwana ne daga gobe Lahadi, yayin da na jeka ka dawo kuma ana kuɗiri aniyar buɗewa daga ranar Litinin, amma sakamakon wani abu na gaggawa da ya taso ya sanya aka ɗage komawa makarantun zuwa wani lokaci da za’a saka a nan gaba.

Kwamishinan Ilmin ya kuma bai wa iyayen yara haƙuri bisa jinkirin komawa makarantar da aka samu, wanda ya ce an yi hakan ne domin cikar daraja da mutumtakar ƴaƴan su, da kuma ƙara shiri akai.

Continue Reading

Trending