Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta harkar Lafiya

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jadadda kudirinsa na tabattar da an inganta harkokin lafiya a wani yunkurin inganta  harkokin kiwon  lafiya a matakai daban-daban na jihar Kano

Mataimakin Gwamna  Nasir Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a harkarkokin lafiya da aka gudanar na kwanaki uku da ya gudana a nan Kano.

Ya ce taron  an gabatar da shi ne a lokacin da ya dace, duba da yadda yawan al’umma ke karuwa, hakan ne yasa ya zama wajibi a tabbatar da an inganta harkokin  lafiya yadda ya kamata.

Alhaji Yusuf Gawuna, ya kara da cewa tuni dai gwamnatin jihar Kano ta fara shirin tallafawa kiwon lafiya a matakin farko yayin da dubu dari uku da saba’in  mutane 370,000 suka ci gajiyar wannan shiri.

Yace Shirin tuni aka inganta shi tare da fara aiki a hukumomin kiwon lafiya  dari biyu da Arba’in da biyar  da  cibiyoyin lafiya  dari da Talatin da Hudu  sai manyan cibiyoyin lafiya  Talatin da bakwai  aka inganta su suka kuma  suke aiki  yadda kamata.

Mataimakin gwamnan Kano Alhaji Yusuf Gawuna y ace gwamnatin  dai har ila yau tuni ta fara aiwatar da shirin tara kudadden aiwatar da kiwon lafiya ga alummar jihar Kano, kamar yadda yake a kundin tsarin lafiya ta jihar Kano.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending