Manyan Labarai
Rundunar yan sanda na farautar wasu jamian hukumar kiyaye haddura ruwa a jallo.

Ana zargin wasu jami’an hukumar kiyaye hadura da na Civil Defence da lallasa lallasa wani dalibin kwalejin koyon aikin tsafta ko School Of Hygiene a turance.
Jamian sun zargi dalibin da taka musu dandamalin girmamawa a makon da ya gabata, a saboda haka suka daure shi da ankwa a ofishinsu dake Unguwar Sabon Gari, inda ake zargin sun lallasa shi.
Wakilin mu Abba Isa yace bayan ya ce jamian sub garzaya da dalibin zuwa asibiti, bayan da suka fuskanci ya fita daga hayyacinsa.
Mun tuntubi kakakin hukumar kiyaye hadura ta Kasa reshen Jihar Kano Kabiru Ibrahim Daura, ta wayar hannu don ji ta bakinsa sai dai bai samu damar daukar kiranmu ba.
Daga na ne muka ziyarci ofishin hukumar ta kiyaye hadura a nan Kano domin ganawa dashi wanda hakan bai samu ba.
Anata baangare rundunar tsaro ta Civil Defence ta kare kanta akan wannan al’amari, inda tace babu hannun jami’inta kamar yadda akayi zargi.
Kakakin rundunar DSP Ibrahim Abdullahi Idris, Wanda yace jami’insu bashi da hannu face dai ya kai dauki ne don Samar da daidaito kamar yadda ya bayyana a zantawasu da wakilinmu ta wayar tarho.
Haka zalika hukumar makarantar School of Hygiene tace tuni ta samu labarin abunda ya faru kuma sun Sanar da nagaba da su don haka yanzu ba zasu ce komai ba sai sakamakon binciken yansada ya fito.
A karshe wakilinmu Abba Isah Muhammad ,ya tuntubi Kakakin Rundunar Yansandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna, Wanda yace sun samu labarin kuma sun fara bincike.

Manyan Labarai
Fadan dabar kofar Na’isa da kofar Dan-agundi, laifin iyaye – Mazaunin Yankin

Wani mazaunin ƙofar Na’isa wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce faɗan dabar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin da Ɗan Agundi, laifin iyaye ne, da kuma wasu manya a unguwannin da ake zargin suna goya musu baya ta hanyar daƙile yunƙurin hukumomi na ɗaukar doka a kansu.
Mutumin ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, biyo bayan yadda rikicin faɗan dabar ya sake ɓarkewa a unguwannin a Alhamis ɗin nan, al’amarin da ya janyo asarar dukiyoyin al’umma a yankunan.
Ya ce lamarin ya faro ne tun a lokacin bikin ƙaramar Sallah, lamarin da a baya ƙura ta lafa, sai dai kuma a ranar Alhamis ɗin sai gashi an sake samun faɗan dabar.
A cewar sa, “A lokacin faɗan dabar ya faru an Sassari mutane da dama, hatta Saniya ma ba ta tsira ba sai da aka sareta, tare da fasa gilasan ababen hawan Mutane, “in ji shi”.
Sa dai mutumin ya ce, tuni jami’an tsaron Ƴan Sanda, suka kai ɗauki tare da kwantar da tarzoma, lamarin da ƙurar ta lafa.

Manyan Labarai
Ba za mu amince da yadda ake yawan kai wa jami’an mu hari ba a Kano – KAROTA

Hukumar kula da zirgar-zirgar ababen Hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce ba za ta lamunta da yadda ake yawan kai wa jami’anta farmaki ba, na ba gaira babu dalili yayin da suke gudanar da ayyukan su.
Shugaban Hukumar KAROTA, a Kano, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya yi wannan gargaɗin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 09 ga watan Afrilun 2025.
“Hakan na zuwa ne biyo bayan wani mummunan hari da wasu mutane da ke cikin baburin Adai-daita sahu suka kai wa jami’an na mu yayin da suke tsaka da aikinsu a titin da ke dab da gidan Buhari kan hanyar zuwa Gidan Zoo, “in ji shi“.
Sanarwar ta ce, tunda farko an tsayar da wani mai baburin Adai-daita Sahu ne inda yaƙi tsayawa, sai kawai aka hango mai ɗan sahun ya naushi jami’in karotar.
Sai dai a ta bakin Shugaban kungiyar ‘Yan Adai-daita Sahu a jihar Kano, ya ce waɗannan mutane ba halattattun ‘Yan Adai-daita Sahu ba ne, sun dai fake da sana’ar su dan aikata ta’addanci.
Daga bisani dai jami’n hulɗa da jama’a na Hukumar Koratar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya ce hukumar za ta ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, don kare afkuwar irin hakan a gaba.
Hukumar ta ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ya shafe ta, ko kuma ƙorafe-ƙorafe, zai iya kiran waɗannan lambobin domin sanar da ita, da suka haɗar da 09015709449 ko 08059689422 ko kuma 08067311520.

Manyan Labarai
Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.
Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a
“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.
Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.
Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su