Connect with us

Manyan Labarai

Cinikin jariri ya bar baya da kura Kano.

Published

on

Wata Ungozoma Mai suna Tambai Sani ta tsinci kanta cikin badakala, sakamakon zargin da akayi mata na karbar haihuwa, da yunkurin jefanar da jaririyar da aka haifa.

Ba ta hanyar aure aka same shi ba.

Wata Matashiya Mai Suna Fatima Sulaiman dake Hotoro unguwar Kujama ce ta haifi jaririn da aka hakkake ba’a same shi ta hanyar aure ba, kafin daga bisani labari ya sauya.

Wata shaida kan abinda ke faruwa ta shaidawa jakadan mu Abba Isa cewa bacewar basirar yadda za’ayi da jaririn ya sanya ungozomar zuwa da masalaha, cewar idan anason sayarwa tana da masu saya a hannu.

An fara ciniki.

Taya kwabo albarka akayi cinikin jariri har yawan kudi ya kai naira Dubu Saba’in cif-cif. Sai dai abinka da sha’ani na rashin gaskiya cinikin ya yiwu, saai dai kuma wacce amsa za’a baiwa mutanen unguwa akan inda jaririn ya shiga, tunda dai ba mutuwa yayi ba?

Kifi na ganinka.

Tun gabanin lalubo hanyar da za’a binne abin kunyar yan Unguwa suka samu cikakken rahoto, tare da tashin cinikin da ake zargin an kullashi a boye.

Yanzu haka dai magana tayi nisa inda jami’an tsaro suka karbi bayanan mutanen unguwa da cikakkun hujjojin takardun cinikayya, har suka baza koma wajen zabarin wadanda ake zargin kulla harkallar.

Muna da hanzari.

Mahaifiyar Buduruwar Mai suna Adama Sulaiman tace kyauta suka yi da sambaleliyar jaririyar ga wata mata mai suna Kadija Usman, da Allah bai bata haihuwa ba.

Daga bisani Jakadan namu Abba Isah Muhammad ya tuntubi Kakakin Rundunar Yansandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna wanda ya tabbatar da wannan al’amari da tuni ke gabansu domin bincike da tabbatar wa mai laifi laifinsa.

Ko da yake ya zuwa yanzu bai yi karin hasken ko an samu wadanda ke da hannu wajen wannan cinikayya, da ta kasance haramun a dokar Najeriya.

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za mu duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin su dan kyautata rayuwar su – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin da ake biyan su, domin kyautata rayuwar su kasancewar abin da ake basu bai taka kara ya karya ba.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin ganawa da ma’aikatan kwashe shara a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati jihar a yau.

Gwamna Abba ya bayyana damuwarsa bisa ƙorafe-ƙorafen da ma’aikatan shara suka yi na tsaikon da ake samu wajen biyansu kudin alawus din su tsawon watanni.

“Gwamnati za ta yi bincike domin gano inda matsalar tsaikon biyan ma’aikatan kwashe shara take da nufin magance ta cikin gaggawa, “in ji Gwamnan”.

Ya kuma ƙara tabbatar wa da ma’aikatan cewa, gwamnati za ta tabbatar kowane ma’aikacin shara an tura shi aiki kusa da gidan sa domin sauƙaƙa musu kashe kudi a wajen sufuri.

Wakilinmu na fadar gidan gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Abba Kabir, ya bai wa ma’aikatan tabbacin gwamnati za ta biyasu dukkanin basukan da suke bi, tare da duba yiwuwar ƙara musu kudin alawus nan bada daɗewa ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ba harkar siyasa ce ta ƙare mini ba nake yin waƙoƙin su Fatima Mai Zogale da A’isha Humaira- Rarara

Published

on

Fitaccen mawaƙin siyasar nan kuma ɗan masana’antar Kannywood Dauda Adam Kahutu Rarara, ya ce batun da wasu suke yaɗawa cewar ya yiwa Fatima mai Zogale kyautar Mota, lamarin ba gaskiya ba ne.

Dauda Rarara ya bayyana hakan ne ta cikin shirin daga Kannywood na tashar Freedom Radio da ya gudana a daren jiya Juma’a, ya kuma ce duk wanda ya bai wa kyautar Mota, Babur ko Kuɗi, ba shi ne ya ke cewa suyi hoto da mutum ba, “A,a wanda na bai wa ne da kan sa ya ke cewa mu ɗauka”.

Ko da aka yi masa tambaya akan ko yana neman muƙami ne a gwamnatin tarayya, Rarara, ya ce, Ba Muƙami yake nema a siya ba, domin inda ace muƙamin yake nema da tuni ya samu.

Har ila yau, Rarara ya ƙara da cewa ba harkar siyasa ce ta kare masa ba ya ke yin waƙoƙin su Aisha Humaira da Fatima Mai Zogale ba, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Dala FM Kano ta rawaito.

Continue Reading

Trending