Connect with us

Labarai

Abinda ke kawo cigaba a unguwanni

Published

on

Dagacin garin Sharada, Alh Iliyasu Mu’azu Sharada, ya ce hadin kan matasa a cikin unguwannin jihar Kano shi ne zai iya bada dama wajen ganin unguwannin sun ci moriyar samun abubuwan more rayuwar al’umma.

Iliyasu Mu’azu Sharada ya furta hakan ne a yayin kaddamar da injin feshin maganin sauro da kungiyar matasan yankin mai suna Kungiyar Inuwar Mutanen Sharada (IMSHA) suka samar da injin tare da aitawar da feshin a dukannin unguwar Sharada.

Ya ce a baya sun taba samar da irin wannan injin amma rashin hadin kan matasa da al’ummar yankin waien bada tallafi domin siyan sinadarin wanda hakan ya dakile  wannan yunkurin.

Shi kuwa shugaban kungiyar Inuwar Mutanen Sharada, Harisu Sani Hayatu Sharada, ya ce za su bi lungu da sako na dukannin yankin unguwar Sharada don amfani da magugunan kashe sauraye da kwaikwayan su a fadin yankin Sharada.

Sannan ya kuma bukaci masu hannu da shunni na yankin da su tallafa masu da sinadarin kashe sauro da zasu zuba a cikin injinan nasu duba da cewa sinadarin da za su siya  yakai sama da dubu 400 a kullum.

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa kungiyar   za ta bi dukannin manyan layaki 17 na yankin domin gudanar da feshi a cikin lungunan yankin.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending