Connect with us

Manyan Labarai

Zanyi muku jagora wajen sayar da abincin Naira 30- Nanono

Published

on

Tun bayan da ya bayyana wa duniya cewar babu batun yunwa a Najeriya ministan noma Alhaji Sabo Nanono ke fuskantar turjiya, game da kalaman da yayi cewar a naira 30 sai mutum yaci yayi nak musamman a gari kamar Kano.

Kalaman nasa sun haifar da cacar musayar ra’ayi a tsakanin mabiya zaurukan sada zumunta, inda bangarori ke bayyana shakku matuka.

Ministan yana martani ne yayin taron manema labarai ranar litinin data gabata, domin shirye shiryen bikin ranar abinci ta duniya, inda yake karyata ikirarin da wasu keyi cewar akwai yunwa a kasa.

Sabo Nanono yace yqnzu haka abinci ya wadata ko ina, Ko da yake wani hoto dake zagayawa na guda cikin yayan ministan mai suna Adamu Sabo Nanono, an ganshi tsugune gaban wata yarinya yana rike da sahanar wake da shinkafa. Sai dai baa bayyana ko ta nawa ya siya ba.

Kwana biyu kenan ana cacar baki kan raayin ministan, inda hatta a majalisu da matasa kan taru batun ya zama babban abin tattaunawa.

Cikin wata tattaunawa ta wayar tarho a maraice Larabar nan, minista na noma ya ce bai fadi wannan magana ba tare da hujja ba. Yace idan kuma ana tantamar kaalaman nasa zai zo kano domin tabbatar da gaskiyar abinda ya fada.

Alhaji Sabo Na Nono yana mai ra’ayin mutane ke jawowa kansu jafa’i sakamakon rashin sanin me ake nufi da yunwa. Ya ce irin haka ce ta faru lokacin da wasu suka jawo wa al’umma masifar boko haram.

Ya kara da cewa manoma na iyakacin kokarin su wajen ciyar da kasar.

Wannan dai shine karo na farko da martanin nasa, bayan shafe tsawon kwanaki biyu ana muhawara a dandalin sada zumunta musamman facebook.

Labarai

Rahoto: hukumar NDLEA na hukunta duk jami’in ta da ya yi laifi – Dakta Ibrahim Abdul

Published

on

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kasa reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya ce, duk lokacin da ya samu daya daga cikin ma’aikatan su ya yi laifi, ya na hanzarin daukar matakin kora ko kuma hukuncin da ya dace.

Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, lokacin da yake mayar da martani a kan matasan da a ke zargin sun fada ruwan kududdufi lokacin da hukumar ta NDLEA ta kai simame yankin Dan Agundi da ke jihar Kano.

 

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa 2 sun gurfana a kotu kan zargin raunata jami’an KAROTA 3

Published

on

Kotu mai lamba 47, da ke rukunin kotunan majistret a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Huda Haruna Abdu, wasu matasa biyu Yunusa Sunusi da kuma Muhammad Babagana, sun gurfana a kotun da tuhumar a kan yi wa wasu jami’an hukumar KAROTA rotse, da suka hada da Usamatu Abdullahi da Sulaiman Musa da kuma Abdulkadir Isma’il.

Ana tuhumar matasan da laifuka guda uku, laifin hada baki da cin zarafi da kuma haddasa mummunan rauni, laifukan da suka saba da sashi na 93 da sashi na 264, sai kuma 247 na kundin laifuka, bayan kuma an karanta musu kunshin tuhumar zargin da a ke yi musu duk sun musanta.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraren shari’ar matar da a ke zargi da kazafin maita

Published

on

Wata mata ta gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a kan zargin bin gari tana yada labarin cewa makwabciyarta da ‘ya’yanta duk mayu ne.

Tun da fari dai matar da a ke zargi da maitar, ta garzaya ofishin ‘yan sanda, tana karar makwabciyar tata, daga bisani kuma ‘yan sanda su ka tattara bayanai su ka mika su kotu domin fara sauraran shari’ar, bayan kuma karantawa matar mai yada labarin maita kunshin tuhumar ta musanta, inda kotu ta dage sauraren shari’ar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!