Connect with us

Labarai

Dan wasan Kano Pillars ya chanja sheka

Published

on

Tsohon dan wasan kwallon kafa ta Kano Pillars wato Gambo Muhammad, wanda ya can ja sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Katsina United, ya bayyana cewa ya koma kungiyar da kafar dama.

Gambo Muhammad din yace daga komawar sa kungiyar ta Katsina United ya zira kwallaye biyar a raga sannan ya kuma taimaka an zura kwallo uku a raga.

Don haka ya sha alwashin cewa a kakar wasa ta bana zai baiwa mara da kunya, domin yadda ya saba zura kwallaye a raga to a bana ma ba fashi.

Gambo Muhammad ya bayyana hakan ne a wata ganawar sa da wakilin mu Abubakar sabo a gidan sa dake unguwar Sani mai Nagge dake karamar hukumar Gwale.

Yayin da kungiyar sa ta Katsina United suka zo nan Kano Dan buga gasar cin kofin Rabi’u Sharif Ahlan.

Ya kuma baiwa magoya bayan sa hakuri, bisa canjin kungiya da ya samu a kakar wasa ta bana, amma yana mai tabbatar musu da cewa, babu shakka, zai taka rawa mai kyau a kakar wasa ta bana yadda za su yi farin ciki mai yawa.

Daga karshe Gambo Muhammad ya yi fatan daukar matsayin dan wasan da yafi kowanne dan wasa jefa kwallo a raga a kakar wasan bana.

Labarai

Ministan lafiya zai kawo ziyara asibitin AKTH

Published

on

Ministan ma’aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya, Osagie Emmanuel Ehanire, zai kawo ziyarar jaje ga asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano wato AKTH, sakamakon ballewar cutar zazzabin Lassa da a ka samu a asibitin har ta yi sanadiyar rasa rayukan wasu likitoci guda biyu Dr Habibu Musa da Kaltum Abba da kuma Dr Abdulkadir Abubakar wanda ya rasa ransa ta sanadiyar hadarin mota.

Ministan zai dai kawo ziyara ne a gobe Asabar 25 ga watan da muke ciki domin jajantawa asibitin da kuma al’ummar jihar Kano dama gwamnati baki daya.

A cikin wata sanarwa wadda ta fito daga asibitin na AKTH, ta ce haka zalika wata cibiya ta lafiya da kimiyar kayayyakin aiki ta Nijeriya ta bada tallafin wata na’ura guda biyu ga asibitin wadda za ta ke kula da aukuwar yaduwar cututtuka a cikin asibitin.

Da yake bayar da tallafin na’urorin biyu, Alhaji Sani Abubakar, ya ce”na’urorin suna da matukar amfani kuma nan da nan suke bayyana alamar yanayin mutum nan take da zarar an sami wata cuta a jikin sa.

Ya kuma mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan mamatan sannan ya kuma yi addu’ar samun lafiya ga wadanda a ke zargin cutar ta Lassa ta kama.

Da yake karbar na’urorin, shugaban asibitin na AKTH, Farfesa Abdurrahman Aabba Sheshe, ya godewa kamfanin bias wannan na’urar da ya baiwa asibitin gudunmawar sa sannan ya kuma tabbatar da cewa za a saka na’urorin a dakin bada kulawar gaggawa da hatsari da kuma dakin karbar haihuwa.

Sannan ya kuma bukaci al’umma da su daina yada jita-jita akan yaduwar cutar ta Lassa kamar yadda a ke kozanta ta kuma ya ce jita-jitar ta nuna cewa marasa lafiya sun daina ziyarta asibitin sakamakon barkewar cutar ta Lassa wanda hakan sam maganar bah aka ta ke ba.

 

Continue Reading

Labarai

Wani soja ya tallafawa firamaren Jogana da kujeru

Published

on

Sojan mai suna Brigadier General Sunday Igbinomwahia, ya na daga cikin manyan sojojin a Nijeriya, wanda ya taba zama a garin Jogana dake yankin karamar hukumar Gezawa lokacin kuruciyar sa, har sai da ya kammala karatun sa na firamare da sakandare a yankin na Jogana.

Wannan dalilan ne suka sanya Sojan mai mukamin Brigedier General Sunday Igbinomwahia, bai manta da garin na Jogana ba.

Hakan ya sanya shi ko da yaushe ya kan tallafawa garin Jogana dake jihar Kano, ta hanyoyi da dama da suka hadar da wasann, bunkasa matasa da Ilimi.

A karo na biyu Brigedier Sunday, ya kai tallafin kujeru na sama da miliyan daya ga makarantar firamaren Jogana domin al’ummar yankin su amfana sakamakon irin zaman rayuwar da ya yi a yankin.

Continue Reading

Labarai

An yi garkuwa da wani babur a Kano kuma an bukaci kudin fansa

Published

on

Wanda ake zargin ya dai dauki babur din ne roba-roba kirar Lifan ya kuma ga takardun makarantar mai baburdin a cikin akwatun ajiye kaya wato (booth) harda lambar waya a cikin babur din nan ta key a kuma dauki lambar ya buga ya kirawo mai babur din inda ya nemi a bashi kudin fansa Naira dubu goma sha biyar (15,000) kafin ya bada babur din.

Lamarin da ya sanya nan ta ke mai babur din mai suna Ibrahim ya nemi mai garkuwa da babur din ya bashi lambar asusun san a banki, bayan ya tura kudin a ka sanar da jami’an tsaro suka bibiye shi wato (tracking) din asusun bankin a ka kuma sami nasarar kama shi a Sabon Gari Bata a jihar Kano.

wata abokiyar aikin Ibrahim wacce suka yi waya da wannan matashin da ake zargi da garkuwa da babur din ta ce” A matsayin mahaifiyar Ibrahim na je wa mai garkuwa da babur din amma ya ce shifa balaifin sa bane”.

Sai dais hi mamallakin babur din Ibrahim ya ce “To da ya ke hausawa na cewa rana dubu ta barawo rana daya tak tamai kaya, kuma idan daraban shan duka bari bata magani, ashe asusun bankin wani mai sana’ar bada kudi na turawa wato (POS) na karbo wanda kuma ba mu da alaka ta sanaiya da shi”. Inji Ibarhim.

Bincike dai ya tabbatar da cewa wannan matashin mai garkuwa da babur ya siyar da babur din a kan kudi Naira dubu goma shabiyar, duk da dai kokarin da mukayi na zantawa da wannan matashi al’amari ya faskara, dafatan Allah ya tsari gatari da sarar shuka.

Wakilimmu Mu’azu Musa Ibrahim yarawaito cewa, babur din an siyar da shi ne a kasuwar farm center dake Kano, bayan tarkon da aka danawa matashin na farko a ka kuma kara kama wani matashin wanda shi ma ya siyar da babur din, tahanyar.

Dubun dayan matashin ya cika ne bayan wanda ake zargin na farko ya buga masa waya ya sanar da shi cewa an samu wanda zai kara siyan baburin a kan kudi naira dubu arba’in (40000) duk da sun siyar da babur din suka sake zuwa da niyar karbar wannan kudi naira (40000) domin karawa a kan wancan dubu (15000) baya ga dubu (15000) din da suka nemi kudin fansa tun da farko.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish