Connect with us

Labarai

Yadda zaman majalisar dokokin jihar Kano ya gudana a yau

Published

on

An bukaci gwamnatin jihar Kano Samar da hanyar da ta tashi daga sabon garin Wudil zuwa kasuwar Garko dukkanin su a kananan hukumomin Garko da Wudil dake jihar kano.

Wannan ya biyo bayan wani kudurin hadin gwiwa da yan majalissun kananan hukumomin biyu suka gabatar a zauren majalissar dokokin jihar ta Kano wato Abba Ibrahim Garko da takwararsa na wudil Nuhu Abdullahi Achika.

Inda suka ce Samar da wannan hanya zai  taimaka wajen habaka tattalin arzikin al’ummomin yankunan biyu.

RUBUTU MASU ALAKA:

Majalisa: A gaggauta dawo da yaran da aka sace

Majalisa ta amince ta ginin titunan Kano zuwa Katsina

A dai zaman majalissar dokokin jihar ta Kano na yau Dan majalissar dokokin jihar kano mai wakiltar karamar hukumar Kumbotso Mudassir Ibrahim Zawachiki ya bukaci gwamnatin jihar Kano data Samar da hanyar data tashi daga Na’ibawa bye pass zuwa yan Shana sannan kuma da hanyar Yangizo zuwa Garu dakuma ta Limawa duk a karamar hukumar sa ta Kumbotso.

Bayan gabatar da muhawara akan wadannan kudurori ne dai majalissar dokokin jihar kano karkashin jagorancin Abdulaziz Garba Gafasa ta amince da wadannan kudurori.

KARANTA WANNA:

Mun shirya tsaf don kare cin zarafin yara -Kakakin majalisar yara

Haka zalika majalissar dokokin jihar kano ta amince da Nada Maifada Bello Kibiya a matsayin mamba mai daraja ta daya a hukumar amintattu masu kula da asusun yan fansho ta jihar kano.

Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto da shugaban kwamitin kula da hukumar Fansho ta jihar kano a zauren majalissar dokokin jihar kano Kabiru Yusuf Ismail’ daga karamar hukumar Madobi yayi a zauren majalissar, inda yace kwamitin yayi bincike kwarai akan Maifada sannan kwamitin ya tabbatar da kwarewarsa da jajircewar sa.

Wakiliyarmu ta majalisar dokokin jihar Kano Khadija Ishaq Muhammad ta rawaito cewa Majalissar dokokin jihar kano ta amince da dokar data amince domin kafa hukumar kula da al’amuran majalissar dokokin jihar Kano wadda aka yi ta tun a shekarar 2007 a zamanin tsohuwar gwamnatin Malam Ibrahim shekarau.

Wannan mataki ya biyo bayan bukatar da gwamnan jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yayi inda yace akwai bukatar ayi kwaskwarima akan sabuwar dokar da majalissar ta sake gabatarwa a shekarar 2018, Wanda hakan yasa majalissar ta amince da tsohuwar dokar ta shekarar 2007 mai makon ta 2018.

RUBUTU MAI ALAKA:

Majalisar dinkin duniya ta baiwa Sarkin Kano mukami

Majalissar dokoki ta yi zaman kara yawan sarakunan yanka a kano

Tsohuwar dokar dai tace kowa ka iya jagorantar hukumar matukar yana da kwarewa a aikin majalissar maimakon sabuwar datace lallai sai Wanda ya taba kasancewa Dan majalissa.

Bayan kammala tattaunawa ne kuma shugaban majalissar dokokin jihar Kano Abdulaziz Garba Gafasa ya bukaci gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya gaggauta aiwatar da wannan dokar tare da rantsar da jagororin hukumar kula da al’amuran majalisar dokokin jihar Kano domin fara aiwatar da nauyin da aka Dora musu.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending