Connect with us

Labarai

Dan KAROTA ya gamu da Ajalin sa

Published

on

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kyawa ya tabbatar da cewa wani Jami’in hukumar karota ya gamu da ajalinsa ana Kano.

DSP Abdullahi Haruna Kyawa ya ce dan KAROTAr ya gamu da ajalin sa ne alokacin da yake kokarin  kama wani mai karamar mota da ake zargin ya saba dokar titi a yankin Yan Dusa, dake dakata a nan Birnin Kano.

Haruna Kiyawa ya ce tabbas sun sami labarin yayin da tuni suka fara tattara bayanai kan wannan batun.

Rahotannin sun bayyana cewar ana dai zargin mai karamar motar ya bi ta kan ruwan cikin jami’in hukumar KAROTA ya kuma tsere.

haha zalika Marigayin wanda ake kira da Tijjani Adamu na aiki ne a sashin ayyukan yau da kulluma na hukumar KAROTA yayin da ya gamu da iftala’in rasa ran sa.

wakilin mu Abba Isa Muhammad ya rawaito cewar,dan KAROTAR na tsaka da gudanar da aikin sa a lokacin da ya gamu da  iftila’in sa na rasa ran sa.

Abba Isa ya ce jami’an KAROTA sun sheda masa cewar, mai karamin motar ya nemi jami’in su da ya sake shi amma yaki amincewa da bukatar sa a don haka ya dauki matakin bin ta kan sa.

Haka zalika kakakin hukumar KAROTA ta jihar Kano Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa yace tuni hukumar ta dauki gawar ta mika ga jami’an ‘yan sanda kuma tuni aka mikata dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Kwararru na Murtala.

Labarai

Karo na farko: An yi gwajin kwakwalwa ga masu niyyar aure a Kano

Published

on

A karo na farko an yi gwajin kwakwalwa ga masu niyyar yin aure a unguwar Danbare da ke jihar Kano domin dakile yawaitar rikicin ma’aurata wanda ke haddasa kashe-kashen juna.

Mai unguwar ta Danbare Saifullahi Abba Labaran ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala ranar Talata.

Ya ce, “Wannan doka mun dade da kafa ta, kuma wadannan bayin Allah da a ka yiwa gwajin mu na yi musu godiya, sakamakon hadin kai da su ka bamu. Wanda zai aure ta zuwa ya ke ya na a gini a unguwar, har a ka saba da shi kamar dan unguwa, ita kuma yarinyar a unguwar ta ke. Likitoci sun ce ya taba faduwa a mashin amma hakan ba wata matsala ba ce, ranar daurin aure za’a kawo takardar gwajin domin kowa yasan babu matsala a tare da su”.

Ya kuma ce, “Ko auro mace a ka yi za’a a shigo da ita unguwar sai mun tabbatar da an yi gwajin. Idan likitoci su ka nuna akwai matsala tsakanin mace ko namiji zamu sanar domin daukar matakin hana auren”. A cewar mai unguwa

Kazalika, shima matashin da zai yi auren ya ce, “Na yi farin ciki da wannan tsarin, an yi mana gwajin kwakwalwa, an kuma gano na taba faduwa a kan mashin, amma an ce ba wata matsala a auren mu, duk abubuwan da a ka zayyana na zama a unguwar na yarda da su. Ni ba asalin dan unguwar ba ne zuwa aikin gini na ke har mu ka saba da su”. Inji matashin

A nata bangaren, itama matashiyar da za’a aura ta ce, “Ni ba a same ni da matsala ba, kuma ‘yar asalin unguwar ce ni. Ina fatan za mu zauna ba matsala ni da shi, kuma zai zauna da ni babu kishiya insha Allahu”. A cewar matashiyar

Saifullahi Abba Labaran ya kuma ja hankalin hukumomi a sauran jihohi domin yin dokar gwajin kwakwalwa ga masu niyyar yin aure, wanda hakan zai kawo karshen kashe-kashe a tsakanin ma’aurata.

Continue Reading

Labarai

Ganduje na ci gaba da bai wa al’umma tallafin Corona

Published

on

Shugaban kwamitin tattara tallafin rage radadin yanayin Corona Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya ce a wannan karon ma gidaje dubu 50 ne za a rabawa tallafin a jihar Kano.

Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da tallafin karo na uku.

Ya ce, “A wannan karon za a fara rabon ne da kananan hukumomi da ke karkashin masaurautar Karaye”.

Ya kuma ce, “Duk magidancin da a ka zabo zai samu buhun shinkafa mai nau’in kilo 25, sai Dawa, da Taliya da kuma man girki”. A cewar Farfesa Muhammad Yahuza

Da yake jawabi gwamnan Kano wanda mataimakin sa kuma shugaban kwamitin  kar ta kwana ya wakilta Nasir Yusif Gawuna ya ce, “Hakika kwamitin tattara tallafin sun cancanci yabo duba da yadda tun daga kafa su su ke gudanar da aikin su”. Inji mataimakin gwamna

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa, kafin kaddamar da tallafin karo na uku sai da kwamitin ya kaddamar da wani tallafin gamayyar kungiyoyi masu zaman kan su da ba na gwamnati ba suka bayar.

Continue Reading

Labarai

Ba’a baiwa daurarru nama mai kashi – DSC Musbahu

Published

on

Mai magana da yawun gidan ajiya da gyaran hali a jihar Kano DSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya ce, ba’a baiwa daurarru nama mai kashi saboda gudun kada su yi amfani da shi wajen illata ‘yan uwan su.

DCS Musbahu, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Doka Gatan Al’umma na gidan rediyon Dala a ranar Talata.

Ya na mai cewa, “Tsokar nama zalla a ke baiwa daurarrun, saboda gudun yin amfani da kashin wajen illata wani da ya ke tare da su, domin kashi makami ne da za’a iya cutar da mutum da shi, don haka a gidan ajiya da gyaran hali duk abun da mu ka san za’a iya cutar wa da shi muna nesan ta shi da daurarrun”.

Ya kuma ce, “Akwai lokacin da a ka samu wata mata ta dauki tsinken tsintsiya da a ka manta a dakin su ta cakawa abokiyar zaman ta a ido, Allah ya takaita abun, a gefen ido ta caka mata bai shiga cikin idanu ba”. A cewar DCS Musbahu

DCS Musbahu ya kara da cewa, duk dabbar da su ka yanka a gidan ajiya da gyaran hali sai an feraye naman an cire kashin daban, domin kashi makami da za’a iya cutar da mutum da shi.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish