Connect with us

Lafiya

Yanzu- Yanzu: Ganduje ya fitar da sunayen kwamishinoni

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya aike da sunayen mutum 20 zuwa majalisar dokoki domin tantance su don tabbatar da su a matsayin Kwamishinoni.

Kakakin Majalisar Abdu’aziz Garba Gafasa ne ya bayyana sunayen a cikin kwaryar majalisar lokacin zaman majalisar.

Da safiyar yau ne majalisar ta zauna don sauraran sunayen da gwamnan ya aike mata.

Da ya ke karanta wasikar da gwamnan ya turowa majalisar da safiyar yau, shugaban majalisar dokokin ta Kano Abdul Aziz Garba Gafasa ya ce, wadanda gwamnan ya turo da sunayensu don nadasu a matsayin kwamishinonin sun hada da: Murtala Sule Garo, Eng Muhd Mu’azu Magaji, Barrister Ibrahim Mukhtar, Musa Ilyasu Kwankwaso, Dr Kabiru Ibrahim Getso, Comrade Muhd Garba, Nura Muhd Dankade, Shehu NaAllah Kura.

Dr. Muhd Tahar Adam,  Dr. Zubairu Umar Muhd, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, Sadiq Aminu Wali, Muhd Baffa Takai, Kabiru Ado Lakwaya, Dr Mariya Mahmud Bunkure, Ibrahim Ahmad Karaye, Mukhtar Ishaq Yakasai, Mahmud Muhd Dantsantsi, Muhd Sunusi Said Kiru, Barrister Lawan Abdullahi Musa.

Sauran sune Kabiru Ado Lakwaya da Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa da Barrister Ibrahim Muktar da kuma Eng Mu’azu Magaji.

Wakiliyar mu ta majalisa Khadija Ishaq ta rawaito cewa  ya ruwaito cewa a gobe talata ne ake sa ran fara tantance su.

 

Lafiya

Har yanzu ‘yan Afrika ba su ci moriyar dimukradiya ba – Farfesa Kamilu

Published

on

Masanin kimiyyar siyasa da ke Jami’ar Bayero a jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce, mulkin dimukaradiyya a yankin Afrika bai yi tasirin da za a iya cewa, an ci moriyar sa ba yadda ya kamata, idan a ka yi la’akari da kasashen da suka cigaba.

Farfesa Kamilu Fagge ya bayyana hakan yayin zantawa da wakiliyar mu Maryam Ali Abdullahi a wani bangare na bikin ranar dimukaradiyya da a ke gudanarawa a ranar Talata.

Ya ce, “Mulkin Dimukaradiyya da wani tsari ne da zai bai wa al’umma da a ke mulka damar fadin albarkacin bakin su tare da zabar wadanda su ke da ra’ayi”. Inji Farfesa Kamilu Fagge

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Likitoci masu neman kwarewa sun shiga yajin aiki

Published

on

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a sakamakon rashin biyan mambobinta wasu hakkkokin su tun daga shekarar 2016 zuwa bana.

Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Dakta Abubakar Nagoma Usman ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a ranar Litinin domin shaidawa al’umma halin da a ke ciki game da yajin aikin.

Ya ce, “Akwai kudaden albashi da na alawus-alawus da kungiyar ke bin gwamnati, wanda har yanzu ba mu san matsayin mu a kan lamarin ba”.

Ya kuma ce, “Gwamnatin tarayya na korar mambobin mu daga aiki, duk da cewa sun sadaukar da rayuwarsu tun bayan barkewar annobar cutar Covid-19”. Inji Dakta Abubakar Nagoma Usman

Wakilinmu Bilal Nasidi Mu’azu ya rawaito cewa kungiyar ta ware wasu wurare domin duba marasa lafiya da ke bukatar kulawar gaggawa.

 

Continue Reading

Labarai

Daukar kaya mai nauyi na janyo cutar laka – Dr Chiroma

Published

on

Wani likita da ke asibitin kashi na Dala Dr. Muhammad Chiroma ya ce, mafi yawan raunin laka da ke a samu nada alaka da yadda al’ummar Najeriya ke yin tukin ababen hawa babu kulawa.

Dr Muhammad Chiroma ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Mu tambayi likita wanda ya ke zuwa a tashar Dala FM a dukkanin ranakun Litinin zuwa Alhamis.

Ya ce, “Ba a hatsarin mota kadai a ke samun raunin laka ba har ma a gida a na iya samu ta hanyar fadawo daga saman bene da bishiya da kuma daukar kaya mai nauyi”.

Ya kuma ce, “Yadda a ke bada maganin laka a gargajiyance shima ya na da hadari duba da yadda a ke bin wasu hanyoyi wajen yi wa mai jinyar magani”. Inji Dakta Chiroma

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Dr Muhammad Chiroma ya kuma ja hankalin mutane da su rinka kula da lafiyar su tare da kiyaye irin kayan da za su rika dauka domin kauce kamuwa da cutar laka.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!