Connect with us

Labarai

Al’umma su rinka gaggawar sanar damu idan aka samu gobara – Sa’idu Muhammad

Published

on

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Sa’idu Muhammad Ibrahim, ya ja hankalin al’umma da su rinka gaggawar sanar da hukumar yayin da aka samu afkuwar gobara.

Sa’idu Muhammad ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin Dala Fm Buhari isa ta wayar tarho, biyo bayan tashin wata gobara a unguwar Ja’en Shago Tara, wanda tayi sanadiyar kone gidan wani Malam Adamu Aliyu.

Inda yace sanar da hukumar ta su akan lokaci shi ne zai bada damar kashe gobarar kafin tayi karfi.

Ya kara da cewa, al’umma su rinka takatsantsan wajen amfani da wuta domin jin dumi, ko barin kayan wutar lantarki a kunne musamman a wannan lokaci na sanyi da muke tunkara.

Wakilinmu Buhari Isah ya rawaito cewa, Sa’idu Muhammad ya ce, akwai bukatar mutane su kula da duk abinda yake da alaka da wuta domin kaucewa faruwar gobara.

 

Labarai

Laliga : Za a dawo gasar ranar 11 ga watan Yuni

Published

on

Mahukuntan gasar Laliga ta kasar Andulissiya wato Spain, sun tabbatar da cewa za a dawo gasar Laliga a ranar 11 ga watan Yuni mai kamawa inda za a fafata da Real Betis da kuma Sevilla.

Hukumar shirya gasar da hukumar kwallon kafa ta kasar tare da gwamnatin kasar Spain su ne su ka amince da hakan cewa za a kuma dawo gasar na kakar 2021/2022 a ranar 12 ga watan Satumba.

Tun dai a ranar 12 ga watan Maris ne a ka dakatar da gasar sakamakon cutar Corona, sai dai shugaban kasar Pedro Sanchez ya tabbatar da cewa za a iya dawowa gasar a ranar 8 ga watan.

Haka zalika a ranar 17 ga watan Yuni za a dawo gasar Firimiya ta kasar Ingila, a yayin da za a dawo gasar Serie A na kasar Italiya za su dawo ranar 20 ga wata mai kamawa.

Continue Reading

Labarai

Liman: Kulawa da tarbiyyar ‘ya’ya zai rage bata gari da lalacewar matasa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Abubakar Dan Tsakuwa dake unguwar Ja’en Yamma a karamar hukumar Gwale, Mallam Abdulkareem Aliyu, ya yi kira ga iyaye da su kara kulawa da rayuwar ya’yan su domin gudun fadawar su cikin halin shaye-shaye.

Mallam Abdulkareem Aliyu ya yi kiran ne ta cikin hudubar Juma’a da ya gudanar yau a cikin masallacin dake unguwar Ja’en a jihar Kano.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su babu shakka za a rage samun bata gari da lalacewar ya’yan matasa a cikin al’umma. Domin haka ‘ya’ya su kara rubanya biyayyar da su ke yi wa iyayen su, domin su rabauta da rahamar Allah S.W.T.”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, a cikin hudubar Limamin Mallam Abdulkareem Aliyu Dan Tsakuwa ya kuma shawarci al’umma da su kara yawaita addu’o i domin samun sauki daga cutar da a ke fama da ita ta Coronavirus a fadin duniya baki daya.

Continue Reading

Labarai

Kar mutane su shagala cewa sai wata shekarar za su kara yin Azumi -Liman

Published

on

Na’ibin masallacin Juma’a na Quba dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birni a jihar Kano, Ahmad Muhammad Ali, ta cikin hudubar san a yau Juma’a ya ce al’umma da su yi kokarin yin Azimin watan Shawal guda shida na cikin sa akwai falala mai yawa.

A lokacin da yake zantawa da wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki, ya ce” Domin watan Ramadan ya wuce ba a daina ayyuka na alheri ba, domin haka al’umma su sani cewa ka da su ce wai donmin sun kamala azumin Ramadan sai wani na badi, to su sani cewa baka da tabbas cewa z aka kai ko kuwa. Saboda haka mu yawaita yin azumin sakamakon Annabi S.A.W ya sunnata mana azumin Litinin da Alhamis, haka kuma bayan sallar farilla babu sallar da ta fi ta kiyamallaili lada domin kuwa Allah ne da kansa yake sakowa saman duniya, domin kiran wanda yake neman wanda yake neman biyan bukata na biya masa”.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa limamin ya ce su na fatan Allah zai rubuta mana lada sakamakon lalurar da a ka samu na kin halartar sallar juma’a lokacin nan na Corona.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish