Connect with us

Labarai

Dambarwa ta barke tsakanin KEDCO da mutanen unguwar Shagari Quaters

Published

on

Biyo bayan shafe tsawon kwanaki 22 babu wutar lantarki a unguwar Shagari Quarters dake nan Kano, al’ummar yankin sun kai karar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano KEDCO ga hukumar karbar korafe-korafe ta kasa Nigerian Regulatory Commission.

Tun da farko dai kamfanin KEDCO ya nemi al’ummar unguwar da su samar da turakun lantarki don kaucewa biyowar wayoyin wutar lantarki ta cikin gidajen su, sai dai al’ummar unguwar basu aminta da hakan ba, inda suka ce sai dai kamfanin na KEDCO ya saka musu turakun.

Hukumar karbar korafe-korafen tayi zama na musamman domin kawo dai-daito a tsakanin bangarorin, inda aka cimma matsaya cewa al’ummar zasu fara yin karo-karo a tsakanin su domin a cike gurbin turakun lantarkin.

A bangaren kamfanin KEDCO kuwa ya ce ba zai dawo musu da wutar ba har sai sun kammala samar da turakun, saboda hatsarin da za’a iya samu in suka sako wuta zuwa unguwar.

Sai dai al’ummar unguwar sunyi zargin cewa akwai wani layi guda daya da yake da wutar lantarki, bayan an yanke wutar duka unguwar, sai dai jami’an KEDCO basu bada amsar wannan tambayar ba.

Al’ummar unguwar Shagari Quarters dai sun bayyana cewa layin dake da wutar lantarkin layin gidan surukar shugaban kamfanin KEDCO ne.

Rubutu masu alaka:

An gargadi KEDCO kan magance korafe-korafen jama’a

Zamu dauke lantarki a jihohin Kano Katsina da Jigawa- KEDCO.

Labarai

An kama wani matashi da zargin sacewa almajirai kayan sawa

Published

on

Shugaban kungiyar Bijilante na yankin unguwar Hausawa dake karamar hukumar Tarauni a Kano, Usaini Haruna Kailo, ya shawarci iyaye da su kara kulawa da tarbiyyar ya’yan su domin rayuwar su ta zama abar koyi a nan duniya dama ranar gobe kiyama.

Usaini Kailo ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, bayan kama wani matashi da su ka yi, da zargin diban kayayyakin sawa na almajirai cikin wata makarantar tsangaya a unguwar Hausawa ‘yan babura.

Ya ce” Matukar iyaye za su kara kulawa da tarbiyar ya’yan su babu shakka za a rage yawaitar samun lalacewar su”.

Da yake nasa jawabin matashin da a ka kama ya ce” Wannan shi ne na farko kuma shi ne na karshe ba zan kara satar kayayyakin mutane ba”.

Wakilin na mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewa, Kwamandan Bijilanten Usaini Haruna Kailo ya ce, za su mika matashin da su ka kama wajen jami’an tsaro domin matakin da ya dace a kan sa domin hakan ya zama izina ga sauran matasa.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Gwamnatin Kogi ta karyata hukumar NCDC

Published

on

Gwamnatin Jihar Kogi ta musanta rahoton hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC cewa mutum biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ta NCDC ta sanar a shafinta na Twitter cewa an samu bullar cutar Covid-19 a jihar ta Kogi inda tace mutane 2 ne ta tabbatar sun kamu da cutar a jihar.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dakta Saka Haruna Audu ya musanta rahoton, inda sanarwar ta bayyana rahoton na NCDC a matsayin labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe balantana makama.

Ya ce” A shirye gwamnatin Kogi ta ke wajen kare rayukan al’ummar ta, kuma ba za ta sanya siyasa a cikin sha’anin kiwon lafiya a jihar ba”.

Sai dai hukumar NCDC ba ta ce komai ba dangane da ikrarin na gwamnatin jihar Kogi.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Buhari ya nemi sake ciyo bashi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake aikewa da wata wasika ga majalisar wakilai domin sahale masa ya ciyo bashin dala Biliyan 5.

Wasikar da shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya karanta a gaban majalisar a yau alhamis, ta bayyana cewa, za a yi amfani da bashin ne domin cike gurbin kasafin kudin bana, na manyan ayyuka.

Kazalika ta cikin wasikar shugaban ya kuma ce za a yi amfani da bashin wajen kara tallafawa jihohi domin yaki da cutar corona.

A kwanakin bayane dai majalisa ta sahalewa shugaban kan ciyo wasu bashi na biliyan 22.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish