Connect with us

Labarai

Yadda amarya ta hallaka uwargida har lahira a Kano

Published

on

Rahotonni daga garin Rurum dake karamar hukumar Rano a nan Kano, na cewa wata mata mai suna Zuwaira ‘yar shekaru 35 ta rasa ranta a ranar jumu’ar da ta gabata lokacin da suke bawa hammata iska tsakaninta da kishiyarta biyo bayan wani sabani da ya shiga tsakanin ta da kishiyar mai suna Hauwa Lawan, yar kimanin shekaru 30

Ana zargin Hauwa Lawan ta tura kishiyar mai dauke da goyo rijiyar dake tsakar gidansu a yayin da suke da baiwa hammata iska.

Kakakin rundunar yansandan jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna, ya tabbatar da mutuwar matar mai suna Zuwaira Sani, tare da ceto Jaririn dake goye a bayanta, sannan tuni ‘yan sanda suka cafke wadda ake zargin.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, yayi kokarin jin ta bakin matar da ake zargin wato Hauwa Lawan amma hakansa bai cimma ruwa ba sakamakon bincike da yan sanda ke gudanarwa akanta.

Labarai masu alaka:

Gwamnatin Kano ta janye ‘yan sanda daga gabatar da wadanda ake zargi a gaban kotu

Baba Suda: Matashin da yayi kisan kai ya mika kansa ga ‘yan sanda a Kano

Labarai

Rahoto: hukumar NDLEA na hukunta duk jami’in ta da ya yi laifi – Dakta Ibrahim Abdul

Published

on

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kasa reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya ce, duk lokacin da ya samu daya daga cikin ma’aikatan su ya yi laifi, ya na hanzarin daukar matakin kora ko kuma hukuncin da ya dace.

Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, lokacin da yake mayar da martani a kan matasan da a ke zargin sun fada ruwan kududdufi lokacin da hukumar ta NDLEA ta kai simame yankin Dan Agundi da ke jihar Kano.

 

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa 2 sun gurfana a kotu kan zargin raunata jami’an KAROTA 3

Published

on

Kotu mai lamba 47, da ke rukunin kotunan majistret a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Huda Haruna Abdu, wasu matasa biyu Yunusa Sunusi da kuma Muhammad Babagana, sun gurfana a kotun da tuhumar a kan yi wa wasu jami’an hukumar KAROTA rotse, da suka hada da Usamatu Abdullahi da Sulaiman Musa da kuma Abdulkadir Isma’il.

Ana tuhumar matasan da laifuka guda uku, laifin hada baki da cin zarafi da kuma haddasa mummunan rauni, laifukan da suka saba da sashi na 93 da sashi na 264, sai kuma 247 na kundin laifuka, bayan kuma an karanta musu kunshin tuhumar zargin da a ke yi musu duk sun musanta.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraren shari’ar matar da a ke zargi da kazafin maita

Published

on

Wata mata ta gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a kan zargin bin gari tana yada labarin cewa makwabciyarta da ‘ya’yanta duk mayu ne.

Tun da fari dai matar da a ke zargi da maitar, ta garzaya ofishin ‘yan sanda, tana karar makwabciyar tata, daga bisani kuma ‘yan sanda su ka tattara bayanai su ka mika su kotu domin fara sauraran shari’ar, bayan kuma karantawa matar mai yada labarin maita kunshin tuhumar ta musanta, inda kotu ta dage sauraren shari’ar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!