Manyan Labarai
Zan tuhumi duk wani baturen ‘yan sanda da aka yi korafi kan shi- CP Habu
Kwamishinan Yansandan Jihar Kano CP Habu Ahmad Sani, ya ce za su tuhumi duk wani baturen ‘yansandan da mazauna yankinsa sukayi korafi kan yadda yake gudanar da aikinsa, matukar ya sabawa tsarin aikin dansanda.
CP Habu Ahmad Sani,Ya bayana hakan yayin taron jin korafe-korafe kan yadda Yansanda ke gudanar da aikinsu tare da Lalibo hanyoyin inganta Tsaro da ya gudana yau a Shiyar Yansanda ta Shawuci a nan Kano.
Komishinan ya kara da cewar burin Rundunar shi ne tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar jihar Kano kamar yadda tsarin aikin dan sanda ya tanadar.
Dan sandan da ake zargi da harbe matashi yana hannun mu-CP Habu
Zamu samar da tsaro a jihar Kano-CP Habu
A shirye muke wajen dakile cikin zarafin al’umma – CP Habu Ahmad
Wasu cikin mutanen da sukayi bayani a yayin taron sun bayana abubuwan dake cimusu tuwo a kwarya musamman daga bangaren Yansanda.
‘’Suna masu cewa kamata yayi rundunar ta inganta ayyukanta’’ A cewar su
Wakilinmu Abba Isah Muhammad,Ya ruwaito cewar taron ya samu halartar Alkalai, da Yan Vigilante, da Masu Unguwanni, Kungiyoyin da Sauran Baturen Yansanda dake Karkashin Shahuci Area Command dake nan Kano.
Manyan Labarai
Gundura da ake zargi da sarewa Ɗan Bijilante hannu da fasa motar ƴan sanda ya shiga hannu
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wani Matashi mai suna Inuwa Zakari ɗan shekara 24, wanda akafi sani da Gundura, wanda ake zargi da sarewa wani Ɗan Bijilante hannu, da kuma fasa motar Ƴan Sanda, da wasu Laifuka
Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM a daren Litinin, Kiyawa ya ce Matashi Gundura sun daɗe suna neman sa ruwa a jallo bisa zargin sa da tarin Laifuka.
“Gundura ya kasance abokin fitaccen ɗan Dabar nan Abba Burakita ɗa unguwar Ɗorayi da ya rasu a baya, kuma har kotu ma muka gurfanar da shi daga baya ya fita amma bai dai na abinda ya ke yi ba, a ranar zaɓen ƙananan hukumomin Kano, da ya shigo yana yunƙurin tayar da hankalin al’umma jami’an mu suka kama shi, “in ji SP Kiyawa”.
Har ila yau, Abdullahi ya ce an kama Gundura da wukake guda biyu a wani waje na matattarar Yan Daba da suke kira “Jungle” a Unguwar Dorayi.
Rundunar ƴan sandan ta ce ta kuma cafke ƙarin wasu matasa 14, da ake zargin su da aikata maban-banta laifuka, inda aka kama su a tsakanin 25 ga zuwa 27 na watan Oktoban 2024.
SP Kiyawa ya ƙara da cewa yanzu haka waɗanda ake zargin ana ci gaba da bincike a kan su a babban sashin binciken manyan laifuka na CID, da ke hedikwatar rundunar da ke Bompai a Kano, kuma da zarar an kammala za’a gurfanar da su a gaban kotu.
Manyan Labarai
Ku zauna lafiya yayin zaɓen ƙananan hukumomin da ake gudanarwa a Kano – Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi kira ga al’umma da su tabbatar da an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaɓen ƙananan hukumomin da ake gudanarwa yau a Kano.
Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kaɗa ƙuri’a a mazaɓar sa ta Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a Kano.
Ya kuma ce akwai buƙatar al’ummar jihar su fita rumfunan zaɓen su kaɗa ƙuri’un su domin ƙara inganta Demukuraɗiyya a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Kwankwaso ya kuma jaddada wa al’ummar jihar cewar gwamnatin Kano za ta ci gaba da ayyukan alheri a faɗin jihar, domin samar da ci gaban Jama’a.
A ranar Asabar ɗin nan ne dai ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano 44, wanda shugabannin fa za’a zaɓa za su shafe tsawon shekaru uku-uku a karagar mulki.
Kafin wannan rana an dai samu cece-kuce akan batun zaɓen, wanda a ranar Talatar da ta gabata wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano, ta dakatar da shugabancin hukumar zaɓen ta jihar Kanseic, da umartar Ƴan sandan jihar su ƙairacewa shiga aikin zaɓen.
Ko da dai a jiya Juma’a babbar kotun jahar Kano ƙarƙashin mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta umarci hukumar zaɓen ta gudanar da zaɓen a yau Asabar, tare da umartar Ƴan sandan su shiga aikin zaɓen, ko da dai wasu mazauna jihar sun shaidawa Dala FM cewar, ba su ga jami’an ƴan sanda ba a wuraren zaɓen.
Jami’an tsaron da aka gani sun haɗar da ƴan Karota, da na Hisbah, da kuma ƴan Bijilante, da jami’an rundunar tsaro da ke yaƙi da ƙwacen Waya da faɗan Daba da magance Shaye-shaye ta Anty Snaching Phone da ke Kano.
Manyan Labarai
Har yanzu jam’iyyu 6 ne suka cika ƙa’idar zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar kuma babu APC a ciki – KANSEIC
Hukumar zaɓe ta jihar Kano (KANSIEC), ta bayyana sunayen jam’iyyu 6 a matsayin waɗanda suka cika ƙa’idar shiga zaben ƙananan hukumomin da za a gudanar ranar Asabar a Kano.
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan babbar kotun jaha ta tabbatar da halaccin hukumar zaben.
Farfesa Malumfashi ya bayyana cewar jam’iyyun da suka cika ƙa’idar sun haɗar da Jam’iyyar AA, AAC, Accord, ADC, da APM da kuma jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, shugaban hukumar zaben ya bukaci hukumomin tsaro da su fito su kare rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin gudanar da zaben, kamar yadda babbar kotun jaha ta umarce su a hukuncin da ta yi da ranar Juma’a 25 ga watan Oktoban 2024.
A ranar Alhamis dai an jiyo yadda kwamoshina mai kula da harkokin yaɗa labarai da al’amuran Shari’a na hukumar zaɓe ta jihar Kano Kanseic, Lawan Badamasi, ya ce za su yi amfani da jami’an tsaron cikin gida domin samar da tsaro yayin zaɓen.
Ya ci gaba da cewa daga cikin jami’an tsaron cikin gidan akwai irin su ƴan Karota, da na Hisbah, da kuma Ƴan Bijilante, domin samar da tsaro idan ƴan sanda suka ƙauracewa shiga aikin zaɓen kamar yadda suka samu umarnin hakan daga wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su