Connect with us

Manyan Labarai

Ana zargin Farfesa da satar yara

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta shirya gurfanar da Farfesa Solomon Musa Tarfa a gaban babbar kotun jiha sakamakon zargin satar yara da a ke yi masa.

Tun da farko dai gwamnatin na zargin Farfesa Solomon Tarfa da laifin satar kananun yara 19, wanda kunshin tuhumar zargin ya bayyana cewar, an gurfanar da Farfesa Solomon Musa Tarfa mazaunin unguwar Nomansland gida mai lamba 15 wanda a ka samu yara maza da mata  19 a cikin gidan sa kuma bincike ya nuna cewar sato yaran ya yi domin ya yi safarar su.

A kan hakan ne gwamnatin jihar ta gurfanar da shi a gaban babbar kotun jiha a ranar 13 ga wannan watan.

Lauyan gwamnati Lamido Abba Soron Dinki, shi ne ya baiwa Farfesa Tarfa, kunshin tuhumar shi kuma Farfesa ya sanya hannu a kai.

A baya dai kotun Majistret mai lamba 29 ta bayar da belin Farfesa Tarfa, sai dai an sanya sharuda a kan belin.

Sai  dai kuma, babban sakatare daga gwamnatin tarayya ya tsaya masa, amma dai lauyoyin sa sun garzaya gaban Justice Faruk Adamu Lawan na babbar kotun jiha mai lamba 7 domin ya sassauta wancan sharadin.

Koda yake lauyoyin gwamnati, Sanusi Ma’aji da Lamido Soron Dinki, sun yi suka sun roki kotun da ta juyar da rokon zuwa babbar kotun jiha mai lamba 2 wadda ita ce za ta saurari shari’ar.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar, an kawo Farfesa Solomon Tarfa cikin kotun Majistret mai lamba 29 sanye da sarka a kafar sa.

 

Labarai

Mai horas da kungiyar Southampton ya kara rattaba sabon kwantiragi

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Southampton, Ralph Hasenhuttl ya kara rattaba sabon kwantiragi a kungiyar ta Southampton.

Ralph Hasenhuttl mai shekaru 52 dan kasar Austrian ya karbi kungiyar ne tun a watan Disamba na shekarar 2018 wanda ya tsallake da su fadawa zuwa ajin ‘yan dagaji.

Mai horaswar ya dai rattaba sabon kwantiragi na tsawon shekaru hudu wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024.

Southampton dai ita ce kungiya da ta taba kwasar kashin ta a hannu har tsawon kwallaye tara da a ka zura mata a raga a gasar wanda Leicester City ta lallasa ta.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Za a ci kasuwanni a ranar da a ka bude Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada dama ga ‘yan kasuwar jihar Kano da su bude dukannin kasuwannin su a ranakun da a ka bude jihar Kano.

Kwamishin yada labarai na jihar, Kwamrade Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan cewa tuni gwamnati ta baiwa ‘yan kasuwar dama bayan ganawa da su ka yi da gwamnati.

‘Yan kasuwar za su bude kasuwannin na su ne tun bayan cikin tsawon kwanaki sama da 50 a rufe sakamakon bullar cutar Corona a jihar Kano.

Da dama dai wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun ci kasuwar su a bayan fage musamman ma wasu daga cikin ‘yan kasuwar Kantin Kwari yadda su ka rinka yin kasuwanci irin samfurin tafi da gidan ka.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: An janye karbar haraji har tsawon watanni biyu saboda Corona

Published

on

Karamar hukumar Doguwa ta janye karbar haraji ga ‘yan asalin karamar hukumar tsawon watanni biyu domin su farfado daga kangin da korona ta jefa su.

Shugaban karamar hukumar Doguwa, Ali Abdul Ali, ya bayyana hakan lokacin kaddamar da tallafin kayan abinci karo na biyu da gwamnati ta gabatar domin ragewa masu karamin karfi radadin zaman gida.

Shugaban karamar hukumar wanda mataimakin sa, Dauda Hamisu Falgore, ya ce” Mun yi la’akari ne da kasancewar mazauna karamar hukumar manoma ne da ‘yan kasuwa”.

A nasa jawabin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar bada agajin gaggawa da tsugunar da gajjiyayyu ta Jihar Kano, Sale Aliyu Jili, ya ce” Za a ci gaba da rabon tallafin karo na Uku ga masu bukatar da su ka cancan ta”.

Da Ya ke nasa jawabin Hakimin karamar hukumar Doguwa, Alhaji Abdullahi Iliyasu, ya yabawa ‘yan kwamitin tare da hakurkurtar da wanda ba su samu ba.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa ‘yan kasuwa da wadan da su ka amfana da tallafin sun bayyana godiyar su.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish