Connect with us

Labarai

RUNDUNAR SOJIN NAJERIYA TA TABBATAR DA MUTUWAR MAYAKAN BOKO HARAM.

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta tabbatar da mutuwar mayakan Boko Haram 23 tare da gano wasu makamai yayin wani arangama da suka yi da mayakan a wani kauye dake yankin tafkin Chadi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar,Texas Chukwu ne ya sanar da hakan jiya Talata a birnin Maiduguri dake jihar Borno, ya ce rundunar sojin karkashin bataliya ta 153 tare da hadin gwiwar sojin kasar Kamaru ne suka kai simamen a ranar litinin din da ta gabata.

Ya kuma ce a cikin makaman da suka kwace a hannun mayakan sun hada da bindiga guda 6 kirar AK 47 da Rifles guda biyu da AK 47 kirar jigida guda 8 da albarusai 33 da kuma babura guda 2.

Texas Chukwu, ya kara da cewa, rundunar sojin ta kuma share wasu hanyoyi dake kauyen Tafkin Chadi da Bulakeisa da Tumbuma Babba da Abbaganaram da kuma kauyen Dan Baure.

 

 

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Labarai

Ku guji tada hankalin al’umma yayin zaɓen ƙananan hukumomi a Kano – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta buƙaci al’umma musamman ma Matasa da su kasance masu bin doka da oda tare kuma da gujewa tayar da hankalin jama’a a yayin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin da za ayi a yau Asabar.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar na Ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a safiyar Asabar.

Ya kuma ce bai kamata al’umma su kasance masu taka doka ba, domin bin doka shi ne wayewa.

“Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su bada gudunmawar su yayin zaɓen domin ganin an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin cikin kwanciyar hankali, “in ji Tasi’u”.

Da yake nasa jawabin daraktan ƙungiyar Kwamared Gambo Madaki, kira ya yi ga dukkanin ƴan ƙungiyar su na ƙananan hukumomin Kano 44, da ku guji sanya kayan ƙungiyar su yayin gudanar da zaɓen kasancewar ba sa cikin masu aikin zaɓen ko kuma sanya ido, domin gujewa fuskantar matsala.

Tuni dai hukumar zaɓe ta jihar Kano Kanseic, ta ce za’a fara kaɗa ƙuri’a ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar yau Asabar.

Continue Reading

Labarai

Sarkin Kano ya ɗaga likkafar Alhaji Abbas Ɗalhatu daga Ƴan Daka, zuwa Bauran Kano, da naɗa hakimai 10

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Alhaji Abbas Ɗalhatu shugaban rukunin gidajen Freedom Radio da Dala FM, a matsayin Bauran Kano, bayan da ya ɗaga likkafar sa daga Ƴan Ɗakan Kano.

Sarkin ya naɗa hakiman ne da safiyar yau Juma’a, inda ya kuma naɗa hakimai goma a matakai daban-daban, daga cikin su akwai Kacallan Kano, da Dan Adalan Kano, da mai unguwar Munduɓawa kuma hakimin Gezawa, da sauransu.

Da yake jawabi jim kaɗan da ɗin hakiman da kuma ɗaga likkar Alhaji Abbas Ɗalhatu zuwa Bauran Kano, mai martaba Sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce an naɗa hakiman ne bisa jajirecewar su da taimaka wa al’umma da kuma biyayya ga masarautar Kano.

Sarkin na Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya kuma hori dukkanin hakiman da su mayar da hankali akan samar da ci gaban al’ummar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Doragarai ya ruwaito cewa a yayin naɗin al’umma da dama ne suka samu damar halarta daga ciki da wajen ƙasar nan.

Continue Reading

Trending