Connect with us

Manyan Labarai

An zo wajen daya ya shunawa daya EFCC – Dan Sarauniya

Published

on

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Engr. Mu’azu Magaji Dan Sarauniya ya yi gugar zana kan siyasar cikin gida a jam’iyya mai mulki a Kano ta APC.

Dan Sarauniya ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar, “An zo wajen sahihin labari daga Abuja ya zo cewa, a tsakanin su dayan ya shunawa dayan EFCC… an samu karon bukata!”

Wannan na zuwa ne kwana guda, bayan da rahotonni suka tabbatar da cewa hukumar EFCC ta gayyaci kwamishinan kananan hukumomi na Kano Murtala Sule Garo, hakan tasa wannan furuci da Dan Sarauniya ya yi ya janyo ce-ce-kuce musamman a kafafan sada zumunta.

Tun da farko Dan Sarauniya ya wallafa wasu rubuce-rubuce har karo uku a shafin sa na Facebook wadanda suka hada da cewar “APC a Kano ai taron kasuwace, akwai APC cinye du, kowa ya santa da mambobinta tsirarai, akwai kuma ta maigirma gwamna, APC mai jama’a”.

Haka kuma ya wallafa cewar “Duk sanda ka ji azzalumai sun ce baka da kirki to ka godewa Allah…”.

A watan Afrilun wannan shekara ne gwamnan Kano ya sauke kwamishinan ayyuka na jihar Engr. Mu’azu Magaji Dan Sarauniya bayan wasu kalamai da ya yi a shafin sa na Facebook kan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa marigayi Abba Kyari.

Sai dai daga baya Dan Sarauniya ya nemi afuwa kan abun da ya yi.

Labarai

Rahoto: Saurayi ya kai iyayen budurwar sa kotu kan zargin cinye masa kudade

Published

on

Wani matashi ya yi zargin iyayen budurwar sa sun karbi kudaden aure har da sadaki a hannun sa, bayan ya rage kwanaki uku a daura aure, iyayen budurwar su ka kawar da maganar auren kuma tsawon watanni ba zancen aure ko kuma dawo masa da kudaden da ya bayar.

Sai dai iyayen budurwar sun yi da’awar cewar, an je gwaji ne kafin aure saurayin ya gudu, inda shi kuma ya mayar da martanin cewar, a ranar da a ka je gwajin bai je da isassun kudi ba, shi yasa ya tafi, kuma washe gari ko da yaje gidan budurwar bijiro da zancen ta fasa auren, yanzu tsohon saurayin ta za ta aura, hakan ta sanya ya garzaya kotun shari’ar musulunci domin a bi masa hakkin sa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai sayen filaye ya kai karar abokin cinikin sa kotu bayan shekaru 3

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a unguwar Goran dutse, karkashin mai shari’a Isma’il Garba Kofar Na’isa, wani mutum mai suna Ibrahim Ishaq, ya yi karar wani mai suna Ibrahim Abba, kan cinikin wani filaye da su ka yi shekaru uku da su ka gabata.

Ibrahim Abba ya bai wa Ibrahim Ishaq motoci guda biyu shi kuma ya bashi filaye guda tara, daga bisani takaddama ta barke a tsakanin su, Ibrahiim Ishaq ya na zargin an cuce shi a cinikin, hakan ya sanya shi garzaya wa kotu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: NAFDAC ta kama magungunan dabbobi na jabu a Kano

Published

on

Hukumar lura da ingancin abincin da magunguna ta kasa reshen jihar Kano NAFDAC, ta kai sumame wani gida a karamar hukumar Bichi, ta ka kama  wani mutum Muhammad Jamilu Sani, wanda aka samu yana hada magungunan dabbobi da allurai da ta ke zargin na jabu ne.

Shugaban hukumar Malam Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!