Connect with us

Labarai

Ba sojoji ba ne suka kaiwa gwamnan Borno hari ba – Shalkwatar tsaro

Published

on

Shalkwatar tsaron Najeriya ta mayar da martani ga gwamnan Borno, Babagana Zulum, kan zargin cewa sojoji ne suka da alhakin harin makon jiya da aka kaiwa tawagarsa a Baga da ke karamar hukumar Kukawa.

Babban jami’in shalkwatar tsaron Jonh Enenche a wata hira da ya yi da gidan talibijin na Channels, ya ce rahoton binciken da suka yi akan faifan bidiyon da ya nuna yadda al’amarin ya faru, ya tabbatar musu cewa mayakan Boko Haram ne suka kaiwa tawagar Zulum din hari.

Harin ya faru ne a lokacin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa Monguno da kuma Bagan domin rabawa ‘yan gudun hijira kayan abinci.

A martanin sa na farko, gwamnan yayi mamakin yadda dakarun, suka gaza ceto Baga, duk da yawan sojojin da aka tura sama da shekara guda.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending