Connect with us

Labarai

Ba laifi ne saurayi ya auri Bazawara – Dr Abdallah

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Usman bin Affan da ke kofar Gadon Kaya Dr Abdallah Usman Umar Gadon Kaya ya ce, ba laifi ba ne dan saurayi ya auri bazawara koda ta kere shi a shekaru idan har akwai soyayya a tsakanin su.

Dr Abdallah ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowa daga shirin Rayuwa Abar Koyi wanda ya ke zuwa a tashar Dala a duk ranakun Juma’a.

Ya ce, “Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa Sallama ya auri Nana Khadijah a matsayin ta na bazawara shi kuma bai yi aure ba, kuma su ka zauna lafiya”.

Ya kuma ce, “Ba daidai ba ne a rinka kaskantar da auren bazawara musamman wajan biyan kudin sadaki, saboda haka ya kamata mawadata su rinka auren zawarawa ko saboda rage musu radadin rayuwa”.

Ya kara da cewa, “Abun da wasu matan masu hali ke yi na hana mazajen su karin aure, ba daidai ba ne”. A cewar Dr. Abdallah

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito, Dr Abdallah ya kuma yi kira ga al’umma a kan su rinka tallafawa Zawarawa musamman wadanda a ka mutu a ka bar su da ‘ya’ya.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending